DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 399

Likitocin sun fara yajin gargadi game da sace abokiyar aikinsu

 Likitocin sun fara yajin gargadi game da sace abokiyar aikinsu

Kungiyar Likitoci ta Nijeriya NARD ta fara yajin aikin gargadi a fadin kasar sakamakon ci gaba da tsare guda daga cikin ‘yayan kungiyar da aka sace, Dokta Ganiyat Popoola-Olawale.

A cikin sanarwar da ta fitar a Litinin din nan, kungiyar ta ce ta yanke wannan shawarar ne a yayin wani zaman tattaunawa na musamman da ta gudanar ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, 2024.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Dokta Dele Abdullahi Olaitan, Sakatare-Janar, Dokta Anaduaka Christopher Obinna da Sakataren Jama’a da Jama’a, Dokta Egbe John Jonah.

Kungiyar ta ce ta kuduri aniyar shiga yajin aikin gargadi na mako daya a fadin kasar nan daga tsakar dare, karfe 12:00 na safe Litinin 26 ga watan Agusta 2024.

Haka zalika ta nuna rashin jin dadin yadda ake ci gaba da barayi ke cigaba da tsare guda daga cikin su Dakta Ganiyat

Poopola duk da kokarin da hukumomin tsaro da gwamnati suka yi ya zuwa yanzu

akan sakinta.

A baya dai kungiyar ta ba da wa’adin makonni biyu na sakin

Abokiyar aikinsu da aka sace wanda tuni lokacin ya wuce.

An sace Dr Popoola ne a ranar Laraba, 27 ga Disamba, 2023 a cikin National Eye Center Staff Quarters da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

An dauko ta ne tare da mijinta, Nurudeen Popoola, da kuma dan uwan mijin (Folaranmi), wanda ke zaune tare da su.

Daga baya an saki mijin nata a ranar 7 ga Maris, 2024.

Dr Popoola da Folarin har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.

Kungiyar ma’aikatan sufurin jigaren ruwa sun amince da 200,000 a matsayin mafi karancin albashi

Kungiyar ma’aikatan sufurin jigaren ruwa sun amince da 200,000 a matsayin mafi karancin albashi

Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen ruwa, Clearing and Forwarding Employers Association (SACFEA) ta amince da Naira 200,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata a bangaren ruwa.

An cimma yarjejeniyar ce bayan shafe shekaru sama da ashirin ana tattaunawar neman mafi karancin albashin na ma’aikatan.

Adadin ya kai kusan kashi 54 cikin 100 fiye da yadda gwamnatin tarayya ta amince da mafi karancin albashi na N70,000 a baya-bayan nan.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin 2024 ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi tayin mafi karancin albashi na ga ma’aikata daga N62,000 zuwa N70,000, tare da tabbatar da cewa za a sake duba shi bayan shekaru uku, maimakon shekaru biyar. 

Sai dai a wata gagarumar nasara da aka samu, kungiyar SACFEA da kungiyar ma’aikatan ruwa ta Nijeriya (MWUN) sun sanya hannu kan yarjejeniyar a hukumance a karshen mako a birnin Legas karkashin kulawar ministan harkokin ruwa da tattalin arzikin kasa, Adegboyega Oyetola.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, shugaban kungiyar MWUN, Kwamared Adewale Adeyanju, ya ce mafi karancin albashin ma’aikatan ruwa a yanzu ya kai N200,000.

Adeyanju ya ce yarjejeniyar babbar nassarace ga ma’aikatan dake aiki tare da alawus-alawus domin samun walwalar su tare da inganta rayuwar ma’aikatan.

‘Yan siyasar Nijeriya na siyasantar da matsalar tsaro a ƙasar –Ngozi Okonjo-Iweala

‘Yan siyasar Nijeriya na siyasantar da matsalar tsaro a ƙasar –Ngozi Okonjo-Iweala

Babbar daraktar Ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta zargi wasu ‘yan siyasar Nijeriya da siyasantar da matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Yayin da take jawabi a taron shekara-shekara da ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta shirya a birnin Legas a ranar Lahadi, tsohuwar ministar kuɗin ta ce tsaro ne ginshiƙin samun kowane irin ci gaba a ko’ina.

Ta ce ba za’a samu ci gaban tattalin arziki idan babu tsaro ba, haka kuma ba za’a samu tsaro ba dan ba mu da ci gaba ba.

Ta kuma yi zargin cewa akwai ‘yan siyasa a Nijeriya da ke tunanin cewa hanyar da kawai za su bi wajen hana abokan hamayyarsu jin daɗin mulki, shi ne ƙirƙirar musu matsalar tsaro, ba tare da la’akari da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da ba su ji ba su gani ba.

Tace abin da muka sani shi ne ‘yan siyasar ƙasarmu sun siyasantar da matsalar tsaro a ƙasarmu don cimma burinkansu na ƙashin kai, wannan kuma shi ne ya jefa ƙasarmu halin da take ciki a yanzu.

Sanna kuma ta yi kira ga ‘yan siyasar ƙasar su daina siyasantar da matsalar tsaro ta hanyar alaƙanta ta da abokan hamayyarsu na siyasa.

Za a kai gwamnatin Sokoto kara kotun ICC bayan ajalin Sarkin Gobir

Za a kai gwamnatin Sokoto kara kotun ICC bayan ajalin Sarkin Gobir

Kungiyoyin matasa 18 a karkashin kungiyar matasan Afirka masu yaki da aikata ba dai-dai ba sun yi barazanar kai gwamnatin jihar Sokoto gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) kan kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a tsare.

Shugaban kungiyar, Dr Suleman Shu’aibu Shinkafi, wanda ya bayyana hakan a karshen taron kwanaki 2 da su ka yi, ya ce kungiyoyin sun zargi gwamnatin jihar Sokoto kan sakaci da ta kai ga rasuwar sarkin.

Dokta Shinkafi ya ce kungiyoyin sun baiwa gwamnatin jihar Sokoto wa’adin mako biyu don biyan wasu bukatu ko kuma su kai su kotun ICC.

Bukatun mu su ne; domin korar kwamishinan harkokin tsaro na jihar, da biyan diyya ga iyalan marigayi sarki tare da bayyana ra’ayinsa game da rasuwar Sarkin Gobir.

Ya kara da cewa suna zargin gwamnati da sakaci wajen tafiyar da lamarin. Gwamnati ce ta gayyace shi zuwa Sokoto don wani taro amma ta kasa kare rayuwarsa. Haka kuma an kasa kubutar da shi bayan an yi garkuwa da shi.”

Daily Trust ta rawaito cewa duk kokarin jin ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Bello Sambo Danchadi da babban sakataren yada labarai na gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Bawa don jin ta bakinsu ya ci tura, domin ba su amsa kiran waya ko amsa sakonnin tes da aka aika musu ba.

Kotu ta garƙame asusun Bankuna 32 da ke da alaƙa da zanga-zangar tsadar rayuwa

 

Wata babbar kotu a Abuja ta garƙame wasu asusun bankuna na mutane 32 da wasu kamfanoni da ake zargin sun dauki nauyin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa har zuwa lokacin da za a gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke kan karar da lauyan Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Mohammed ya gabatar, ya umurci bankunan da su kamo masu asusun ajiyar ko duk wani mutum da yake mu’amala da asusun ajiyar.

An hallaka jami’an ‘yan sanda yayin zanga-zangar ‘yan shi’a a Abuja

An harbe wani dan kasuwa, tare kashe wasu ‘yan sanda biyu a wani yamutsi da ya kaure tsakanin jami’an ‘yan sanda da mabiya mazhabar Shi’a a kasuwar Wuse da ke Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, an harbi dan kasuwar mai suna Amiru na gudun ceton ransa, yayin da wani alburushi ya same shi a kirji, a lokacin da ‘yan sanda ke korar masu zanga-zanga na mabiya mazhabar Shi’a a Wuse zone 6, Abuja.

Kazalika, bayanai sun ce an kone motocin ‘yan sanda uku a yayin yamutsin.

Mabiya mazhabar Shi’a din dai na muzaharar Arbaeen don cika kwanaki 40 na bikin Ashura.

Durov zai gurfana a gaban kotu bayan kame shi a Faransa

0

Mamallakin manhajar Telegram, Pavel Durov, zai gurfana a gaban kuliya bayan kama shi a filin jirgin saman Faransa

Bayan kama hamshakin attajirin dan kasar Rasha mai shekaru 39 a filin jirgin Le Bourget a daren Asabar zai gurfana a gaban kuliya ranar Lahadi

Ana zargin Durov da kasa daukar matakin hana amfani da dandalin sa ga masu aikata laifuffuka

An cafke ɗan bindiga yana sallah a masallaci

0

An kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a lokacin da yake sallah a cikin wani masallaci a garin Takum na jihar Taraba.

Wani mazaunin unguwar da lamarin ya wakana mai suna Dauda Mai Dawa ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an kama shi ne a lokacin da yake gudanar da Sallar la’asar.

Dauda ya kara da ce a ranar an kama mutane 13 da ake zargi a kan hanyar Takum zuwa Maraban Baissa a jihar

Kotu ta daure barawon da ya saci allunan sanarwa cikin makabartar a Kano, tare da yi masa bulala 30

Wata kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano ta umurci da a daure wani matashi mai shekaru 25 Hassan Adamu a gidan yari bayan da ta same shi da laifin satar allunan sanarwa 15 da aka kafe a wata makabarta a jihar.
Kotun dai ta tuhumin matashin da aikata laifuka biyu, na ratse da kuma sata, inda Alkalin kotun Malam Umar Lawal ya yanke hukuncin daurin watanni 6 ga matashin tare da yi masa bulala 30.
Lamarin da ya faru a ranar 21 ga Agustan, 2024, an kai kara wajen ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Gwale a jihar.

Kafa hukumar kula da Almajirai zai inganta karatun allo a Nijeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Muslimi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa Shugaban Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba sa zuwa Makaranta,

Dr Muhammad Sani Idris, mutum ne da ke da kwarewa a kan yadda za a magance matsalolin da suka addabi karatun allo da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Sarkin Musilmin ya na magana ne yayin da wata tawaga daga hukumar ta ziyarce shi a fadarsa dake Sokoto.
Ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga kudirin hukumar na magance wadannan matsaloli inda ya ce zai tattauna da sarakuna gatgajiya domin samun goyon bayansu. 
Tun da farko,Shugaban Hukumar Almajirai da Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta, Dr Muhammad Sani Idris ya ce twawagar ta sa, ta ziyarci Mai Marataba Sarkin Musulmi ne domin ya sa wa hukumar albarka a wannan aiki na gyara karatun allo, dakuma sa, ko mayar da yara makaranta, tare da koya musu sama’o’i domin dogaro da kai.