An kafa cibiyoyin samar da lantarki a wasu manyan jami’o’in Nijeriya, in ji ministan makamashi
Gwamnatin Shugaba Tinubu a Nijeriya za ta kafa sassan kula da tsofaffi
Za a bude sashen da zai rika duba lafiyar shugaban kasa da sauran manyan kasa a babban asibitin Nijeriya da ke Abuja
Kafanin kasar China ya sake kwace jirgin Najeriya a Canada
Zanga-zangar rashin Sarkin Gobir, ta sa gwamnatin jihar Sokoto kakaba dokar hana fita
Manoman citta a Nijeriya sun yi asarar Naira biliyan 12 a shekarar 2023 – Minista Noma
Gwamnatin tarayya ta ce manoman citta a Nijeriya sun yi asara da ta kai Naira biliyan 12 sakamakon wata annobar da ta lalata amfanin gonakin su a shekarar 2023.
Karamin ministan noma da samar da abinci, Aliyu Abdullahi ne ya bayyana haka a wajen taron Inshorar aikin gona a Abuja.
Ministan ya ce manoman sun yi asarar sama da kashi 90 cikin 100 na yawan amfanin gonakin da suke noma a kakar bara.
Tanko Yakasai ya nisanta kansa daga rade-radin kafa jam’iyyar Arewa
Tsohon mashawarci na musamman ga marigayi shugaban kasa Shehu Shagari, Tanko Yakasai, ya nesanta kansa daga wani labari da jaridar Punch ta yanar gizo ta wallafa na kafa wata sabuwar kungiyar siyasa mai suna “The League of Northern Democrats.”
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 21 ga Agusta, 2024, aka bai wa manema labarai a Kano.
Yakasai ya kara da cewa “Tun da farko ban yi niyyar yin magana game da wannan lamarin ba.”
“ina kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton da jaridar Punch Online Media ta bayar, domin ba ni da hannu a cikin masu shirya taron ko kuma kungiyar da ake magana a kai.”

.jpeg)
.jpeg)
.jpeg)
.jpeg)