Fada ya kaure tsakanin wasu direbobi da manajojin Dangote a Obajana
‘Har yanzu shugaban Amurka yana amfani da jirgin sama da ya yi shekaru 34’
Har yanzu shugaban Amurka yana amfani da jirgin sama da yayi shekaru 34 amma Nijeriya ta yi watsi da jirgin mai shekaru 19
Bayan na makonni fadar bata ce komi ba, kan batun siyan jirgin shugaban kasar ta bayyana siyan sabon jirgin kirar Airbus A330, a ranar Litinin din da ta gabata.
Tattaunawa game da sabon jirgin shugaban kasar ya fara ne bayan matsalolin da jirgin Boeing Business Jet (BBJ) ya samu a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shekaru 19 da suka gabata ya samu matsala a wata tafiya da yayi Saudiyya da Netherlands da kuma Afirka ta Kudu.
Sai dai shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da jirgin saman haya, lamarin da fadar shugaban kasar ta bayyana a matsayin abin kunya.
Yayin da jami’an gwamnati ke ta cece-ku-ce kan samar da wani sabon jirgin, talakawa sun nuna rashin amincewar su, ganin yadda matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da ke addabar Nijeriya.
Sai dai a watan Yuni, wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Nijeriya ta sayi jirgin Airbus A330 daga wani bankin kasar Jamus. Rahotanni sun bayyana cewa bankin ya kwace jirgin ne daga hannun wani basarake da ba a bayyana sunansa ba wanda ya ki biyan bashi.
Fadar shugaban kasar dai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, lamarin da ya bar jama’a cikin duhu game da sayan jirgin. A yayin da ake ta cece-kuce a kan kamfanin saga na kasar Sin, ‘yan Nijeriya sun samu labarin cewa da gaske an sayi sabon jirgin. Amma duk da haka fadar shugaban kasar ta yi shiru har zuwa ranar Litinin lokacin da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya fitar da hotuna tare da bayanai
Onanuga, wanda bai bayyana kudin sabon jirgin ba, ya ce, sabon jirgin da aka sayo bai yi wani tsada ba, kuma ya ceci Nijeriya da makudan kudaden da ake kashewa da kuma kudin man fetur.
Atiku ya caccaki Tinubu kan batun tallafin man fetur
Atiku ya caccaki Tinubu kan batun tallafin man fetur
Madugun adawa a Nijeriya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abu bakar ya caccaki shugaba Bola Tinubu kan rahotannin sake dawo da tallafin man fetur.
Atiku ya mayar da martani ne kan rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa shugaban kasar ya umurci kamfanin mai na kasa(NNPCL) da ya kashe kudaden da hukumar ta ke samu kan tallafin mai.
Rahoton ya ci gaba da cewa, ana sa ran kamfanin na NNPC zai dakatar da biyan kudaden na tsawon watanni takwas a wannan shekara – daga watan Mayu zuwa Disamba domin biyan tallafin.
Da yake mayar da martani, Atiku a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na X a ranar Litinin, ya bayyana matakin a matsayin boyeyyen sirri,da ba kowa ya sani ba.
Ya ce, saboda sahihan bayanan da ke yawo ta kafafen yada labarai dangane da yadda gwamnatin tarayya ta ci gaba da bayar da tallafin da ake bayarwa a kan Premium Motor Spirit (PMS) a boye, ya nuna wani babi na rashin gaskiya a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Kamfanin mai na NNPC ya ce kudin da ya biya ba na tallafin man fetur ba ne
Kamfanin mai na NNPC ya ce kudin da ya biya ba na tallafin man fetur ba ne
Kamfanin mai na Nijeriya (NNPC Ltd.) ya ce bai biya wa kowa tallafin man fetur ba cikin watanni tara da suka gabata.
Babban jami’in kula da harkokin kudi na kamfanin, Alhaji Umar Ajiya ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a Abuja.
Ajiya ya ce kamfanin NNPC yana magance matsalar shigo da motoci na Premium Motor Spirit ne kawai tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya.
Yace a cikin watanni takwas zuwa tara da suka gabata, NNPC bai biya kowa ko kwabo ba a matsayin tallafi,babu wani dan kasuwa da ya karbi kudi daga gare su ta hanyar tallafi.
Yakara da cewa Abin da ya faru shi ne, suna shigo da PMS, wanda aka sauke a kan wani farashi na musamman, kuma gwamnati ta ce su sayar da shi a kan farashi mai sauki.
Ya ce kuma yarjejeniyar tana tsakanin gwamnatin tarayya da Kamfanin NNPC, don haka basu biya wani kudi ba da sunan tallafi.
Kungiyar kwadago ta NLC na yin wani taron gaggawa kan wani zargi da ake yi wa shugabanta, Ajaero
Kungiyar kwadago ta NLC na yin wani taron gaggawa kan wani zargi da ake yi wa shugabanta, Ajaero
Tuni dai wasu shugabannin kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da suka hada da shugaban ta, Joe Ajaero suka hallara a hedikwatar kungiyar ta NLC domin gudanar da wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa.
Taron dai na zuwa ne biyo bayan kiran da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi wa Ajaero domin gudanar da bincike kan zargin bada kudade wajen aikata ba dai-dai ba da cin amanar kasa da kuma aikata laifuka ta yanar gizo.
Sammacin dai ya umarci shugaban NLC ya gabatar da kansa domin amsa tambayoyi da misalin karfe 10:00 na safiyar yau.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, gidan talabijin na Channels ya ba da rahoton yadda gayyatar NPF ke kunshe a cikin wata wasika mai kwanan wata 19 ga Agusta 2024, kuma mai dauke da sa hannun ACP Adamu Muazu a madadin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma yi gargadin cewa za a bayar da sammacin kama shi idan Ajaero ya ki bin umarnin hukumar.
Hukumar karbar korafe-korafe za ta gudanar da bincike kan zargin badakalar wasu kudade a Kano
Hukumar karbar korafe-korafe za ta gudanar da bincike kan zargin badakalar wasu kudade a Kano
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta kaddamar da fara bincike a kan zargin karkatar da wasu makudan kudade, da kuma zargin an karkatar da kudaden tallafi na gwamnatin tarayya.
Daga cikin wadanda ake sa ran za a yi musu tambayoyi kan badakalar da ake zargin sun hada da Musa Garba Kwankwaso, wanda dan gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne da kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Shehu Wada Sagagi.
Musa Kwankwaso, wanda dan uwan kwankwaso ne ubangidan Abba Kabir Yusuf, an yi zargin cewa yana da hannu a badakalar sayen kayayyaki. Wani kamfani mai suna Novomed Pharmaceuticals, wanda Musa Kwankwaso darakta ne kuma ake kyautata zaton mallakarsa ne ya bayar da kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.
Kwangilar da aka ce an bayar da ita ba tare da bin ka’ida ba, ta kunshi kowace karamar hukuma tana biyan kusan Naira miliyan 9 duk wata, wanda ya kai Naira miliyan 396 a duk wata.
Wannan badakalar ta fito fili ne a lokacin da Bello Galadanchi, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta umurci kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 44 da su biya kimanin Naira miliyan 10 domin samar da maganin, tare da bayar da kwangilar ne kadai ga kananan hukumomin. Novomed Pharmaceuticals.
A karshen makon da ya gabata ne Gwamna Abba kabir Yusuf ya nesanta kansa da kwangilar inda ya musanta sanin tun da farko kan yarjejeniyar tare da bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.
A wata tattaunawa ta musamman da Daily Trust,shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji ya ce sun gayyaci duk wa’yanda ake zargi domin amsa tambayoyi tare da gano gaskiyar lamarin.
Ya bayyana cewa gayyatar na daga cikin kashi na farko na binciken da nufin tattara muhimman bayanai da takardu da suka shafi kwangilar.
Yaki da cin hanci da rashawa na bukatar taron-dangi, in ji Shugaba Tinubu
‘Yan bindiga sun halaka hadimin gwamnan Katsina da matarsa
‘Yan bindiga sun halaka hadimin gwamnan Katsina da matarsa
Wasu ‘yan bindiga sun halaka Salisu Ango, guda daga cikin ma’aikatan gwamna Dikko Radda a kauyen Gyaza dake karamar hukumar Kankia a jihar Katsina da matarsa ta farko, tare da yin awon gaba da matarsa ta biyu.
An bayyana cewa sun halaka mutum daya, tare da raunata wani, sannan sun yi awon gaba da wasu 28 a unguwar Shirgi da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
An kuma bayyana cewa sun yi awon gaba da wasu dabbobi da ba a tantance adadinsu ba a kauyen lokacin da suka kai harin harin.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wanda aka kashe a matsayin Amadu Suru, wanda aka harbe shi a lokacin da yake kokarin hada dabbobinsa a rumfarsu.
Ya kuma shaida wa Daily Trust cewa maharan sun kai farmaki kauyen ne a daren Lahadi inda suka kai samame wasu gidaje.
Ya ce mata da kananan yara su ne manyan wadanda akai garkuwa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Gyaza da misalin karfe 10:00 na dare, inda suka kai farmaki gidan Ango, inda suka harbe shi da matarsa har lahira.
Kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta bayyana shirin ta na shiga yajin aiki
Kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta bayyana shirin ta na shiga yajin aiki
Kungiyar malaman jami’o’i ta sanar da gwamnatin tarayya shirin ta na shiga yajin aiki a fadin kasar kamar yadda rahoton jaridar PUNCH ya rawaito.
Wasu majiyoyi daga majalisar zartaswar kungiyar ASUU ta kasa sun tabbatar wa da PUNCH a Abuja hakan a Litinin dinnan.
An fitar da sanarwar ne a karshen taron hukumar da aka gudanar a jami’ar Ibadan, kuma ana sa ran mika kwafin ga ma’aikatun kwadago da ilimi na tarayya.
Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin tarayya.
A ranar 26 ga watan Yuni ne Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya gayyaci kungiyar kwadagon zuwa wani taron tattaunawa kan batutuwan da suka shafi jami’o’i da kuma dakile yajin aikin da suka shirya yi.
Rundunar sojin Nijeriya ta girke jami’ai domin kare manoma a wasu jihohin Arewa
Rundunar sojin Nijeriya ta girke jami’ai domin kare manoma a wasu jihohin Arewa
Yayin da aka fara damina, rundunar sojin Najeriya ta ce ta girke sojoji a wasu jihohin arewacin kasar, domin kare manoma daga hare-haren da ‘yan bindiga ke kai musu yayin da suke gudanar da ayyukan su.
A wata sanarwa da daraktan hulda da manema labarai na rundunar Manjo Janar Edward Buba ya fitar ta ce an tura dakarun musamman a jihohin arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.
A cewarsa, matakin ya baiwa manoma da yawa damar samun yin noma don ganin ba a samu matsala ba har zuwa lokacin girbi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da karancin abinci wanda ya kara tabarbare hauhawar farashin kayayyakin abinci da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta bayyana sama da kashi 40 cikin 100.









