DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 402

Masu karamin karfi za su iya cin abinci mai kyau ta hanyar kayan da ake nomawa a cikin gida – Binciken masana

Masu karamin karfi za su iya cin abinci mai kyau ta hanyar kayan da ake nomawa a cikin gida – Binciken masana

Yayin da farashin kayan abinci ke ci gaba da hauhawa, masana abinci mai gina jiki sun ce iyalai masu karamin karfi na iya cin abinci mai kyau ta hanyar rungumar abincin da ake nomawa a cikin gida.

Masana abinci mai gina jiki sun ba da shawarar cewa a cikin nau’o’in abinci guda 10 da ake da su, mutane su yi ƙoƙari su haɗa akalla biyar daga cikin nau’o’in abinci 10 don samun cin abinci mai kyau ga iyalansu.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa matsakaicin farashin abinci mai kyau ga dan Nijeriya ya tashi a watan Janairu zuwa kiyasin Naira 1,241 a watan Yunin 2024, a cewar wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasa da kuma hukumar ta fitar.Yace iyalai da yawa na fama da matsananciyar rashin abinci saboda tsadar kayayyaki.

Rahoton NBS ya nuna cewa kayan masarufi ya karu da kashi 45 cikin 100 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2024, yayin da hauhawar farashin kayayyaki gaba daya da kuma hauhawar abinci ya karu zuwa kashi 33 da 40 bisa 100.

NBS ta bayyana cewa adadin a watan Yuni ya kai kashi 19 cikin 100 fiye da N1,041 ga kowane mutum a kowace rana kamar yadda aka ruwaito a watan Mayu 2024.

Nijeriya za ta dauki sabon kocin Super Eagles

Nijeriya za ta dauki sabon kocin Super Eagles

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon kocin kasar Sweden Janne Andersson na shirin karbar mukamin sabon kocin Super Eagles.

Andersson mai shekaru 61, wanda ya samu nasarori tare da tawagar kasar Sweden, gami da cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018, an ruwaito cewa NFF ta zabi maye gurbin Finidi George da shi.

Ana saran Andersson ne dai zai jagoranci tawagar ‘yan wasan Nijeriya a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2025 mai zuwa.

Har yanzu dai hukumar NFF ba ta tabbatar da nadin a hukumance ba, sai dai majiyoyi na kusa da hukumar na nuni da cewa an kusa fitar da sanarwar.

Hukumar NYSC ta kori matasa masu yi wa kasa hidima 54 dake da takardun bogi

Hukumar NYSC ta kori matasa masu yi wa kasa hidima 54 dake da takardun bogi

A ci gaba da kokarin da take yi na hana daliban da ba su cancanta ba su samu takardar shaidar yi wa kasa hidima ta NYSC, jami’ar Calabar ta tattara mutum 54 da basu cancanta ba ga hukumar tare da korar su

Darakta Janar na hukumar NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana hakan a Abuja. Ya kuma kara da cewa za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya ce wasu goma sha tara (19) daga cikinsu wadanda tun farko suka yi rajista ta yanar gizo an hana su yin hidima, yayin da guda hudu (4) basu da cikakkun takardun da za a amince dasu.

Ya kara da cewa akwai karin matasa 101 da suma basu cancanta ba domin basa da cikakkun takardu wanda adadinsu yakai 178,kuma haryanzu ana kan bincike akai

Da yake karin haske, Janar Ahmed ya ce hukumar NYSC ba za ta bar wata kafa ba da bata gari zasu shigo domin lalata mata ayyukan ya zama wajibi a cigaba da tsaftacewa.

Kashi 25% na ma’aikatan lafiya a Burtaniya ‘yan Najeriya ne

 

Ministan lafiya da walwalar jama’a, Muhammad Pate, ya yi ikirarin cewa kashi 25% na ma’aikatan kiwon lafiya a kasar Burtaniya ‘yan Najeriya ne.

Da yake bayyana matsalar karancin ma’aikatan kiwon lafiya a Nijeriya, Ministan ya ce kashi 67 na likitocin da Najeriya ta horar duk sun yi hijira zuwa kasar Birtaniya.

Ministan ya kara da cewa duk da babu wata dokar kiwon lafiya da ta hana ‘yan kasar yin hijira, amma zama a gida zai fi dacewa.

Hukumar NCAOOSCE ta bukaci kwararru su ba ta shawarar bunkasa ilimin almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta

A kokarinta na gyaran karatun allo da kuma kawo karshen matsalar rashin zuwa makaranta a Najeriya,  Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba Sa zuwa Makaranta ta shirya taron bita domin lalubo hanyoyin da za a inganta al’almura. 
A dalilin haka ne take kira ga duk wanda ke da wadansu shawarwari a kan matakan da ya kamata a dauka domin cimma nasara, da ya turo bayanan nasa ta email zuwa : info@encaoosce.gov.ng
Domin karin bayani, za a iya kiran wannan lambar: 0909 107 4800.
Mu hada karfi da karfe domin ganin cewa kowanne  yaro a Najeriya ya samu ingantaccen Ilimi.
Sanarwa daga: Dr Muhammad Sani Idris, Shugaban Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta

Gwamnatin Tinubu ta hannun hukumar NCAOOSCE ta zakulo yara 20,000 domin sanya su a makarantun boko a Abuja

0

 

Hukumar kula da Almajirai da yaran da ba su zuwa makarantun boko a Nijeriya ta sanar da kammala zakulo yara sama da 20,000 domin mayar da su makarantun boko.

An samu wannan jimillar yaran ne bayan wani gagarumin aikin fadakar da jama’a na  makonni uku da jami’an hukumar  NCAOOSCE suka shiga lunguna da sako-sako na babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban hukumar Muhammad Sani Idris ya jinjina wa jami’ansa da ake kira Marshals wadanda aka dora wa alhakin zakulo yaran da ba su zuwa makarantun bokon cikin wani kankanin lokaci.

A cikin wata sanarwa da Malam Nura Muhammad, babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga shugaban hukumar ta NCAOOSCE ya fitar, hukumar ta ce  tana da shirin saka milyoyin yara makaranta a duk shekara.

Sanarwar ta ce, da farko an fara kokarin ganin an saka yara 10,000 makaranta, amma irin hobbasar da hukumar ta nuna ya sa aka samu sakamakon da ya ba mutane mamaki.

Muhammad Sani Idris ya ce nan da zuwa watan Satumba, wadannan yara da ake zakulo za a sanya su a makarantun boko dabam-dam da ke yankin Abuja. Ana kuma sa ran daga nan shirin zai fadada zuwa suaran yankunan Nijeriya. 

APC ta kira taron NEC domin fara shirin zabo sabon shugaban

Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar 12 ga watan Satumba domin gudanar da taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC).
Taron kusoshin jami’iyyar na NEC shi ne na biyu mafi girma wajen yanke hukunci ga babban taron jam’iyyar.
Mataimakin sakataren jam’iyyar APC na kasa Barista Fetus Fuanter ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa (NWC) a Abuja, ranar Alhamis.
Fuanter, wanda ya kasance tare da sauran mambobin kungiyar NWC yayin taron manema labarai ya kuma bayyana cewa mambobin jam’iyyar APC na kasa za su yi taro a ranar 11 ga watan Satumba, kafin taron na NEC.

Shugaba Tinubu mutum ne mai tawali’u – Shettima

 Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin mutum mai tawali’u kuma wanda bai yarda da almubazzaranci ba.

“Na fi shugaba Tinubu sanya sutura masu tsada, domin tun da muka hadu da shi agogo daya nake ganin yana sanyawa” in ji mataimakinsa Kashim Shettima.

Ma’aikatan sufurin jiragen sama a Nigeriya na shirin tsunduma yajin aiki

Ma’aikatan sufurin jiragen sama a fadin Nijeriya na ta shirye-shiryen tsunduma yajin aiki.
Hakan ya biyo bayan nuna adawa da yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da cire kashi 50 cikin 100 daga kudaden shiga na cikin gida na manyan hukumomin sufurin jiragen sama.
Yajin aikin zai fara gudana a ranar 21 ga watan Agusta, 2024, Kamar yadda Daily trust ta rawaito.
Sai dai hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta yi gargadin cewa shiga yajin aikin zai kawo cikas ga harkokin jirage a fadin kasar.
Kungiyoyin sun bayyana hukuncin nasu ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Agusta 14, 2024, mai taken, “Ceto Jiragen Sama Daga Rushewa”, kuma aka sake su ga manema labarai a ranar Alhamis.
Hukumomin da abin ya shafa a fannin sun hada da NCAA, Hukumar Kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya, Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya, da Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya.

Farashin kayan abinci ya fara sauka a sassan Nijeriya

Har yanzu masara ba ta sauko ba a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya, inda ake sai da buhun masarar ₦95,000, yayin da a makon da ya gabata aka sai da ₦90,000 cif .

Sai dai a kasuwannin jihohin Adamawa da Lagos an sai da buhun kan kuɗi ₦90,000 daidai a satin nan, amma a makon jiya farashin ya sha bamban a kasuwannin, inda a jihar Adamawa aka sayar da buhun ₦85,000 a makon da ya shude, sai kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos aka sayar ₦103,000.
To a Kanon Dabo ana sai da buhun masara ₦84,000 a satin na da ke shirin karewa, amma satin da ya wuce ₦87,000 aka sayar da buhunsa, an samu ragin ₦3000 kenan a mako guda.
Farashin masara bai sauya zani ba a kasuwar Giwa jihar Kaduna da aka sayar ₦88,000 a makon da ya gabata, haka ake sayarwa a makon nan.
Ita kuwa Shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan satin da ake sayarwa ₦170,000, amma a satin da ya gabata ₦160,000 ne kuɗin buhun Shinkafa a kasuwar.
Sai dai a kasuwar Dawanau jihar Kano farashin bai sauya ba da na makon jiya da aka sai da ₦160,000 daidai.
Haka zalika a kasuwar Mai’adua jihar Katsina farashin buhun Shinkafa ‘yar gida bai canza ba da na satin da ya shuɗe, wanda aka saya kan kuɗi ₦145,000.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos an samu sauƙin ₦5000 kan farashin shinkafa da aka sayar ₦150,000 a makon jiya, yayin da ake sayarwa ₦145,000 a makon nan.
Ita ma dai jihar Adamawa farashin bai sauya tufafi ba a kasuwannin da ake saidawa ₦148,000.
A ɓangaren shinkafar Bature kuwa, ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da ake sayarwa ₦92,000, haka nan a makon da ya gabata ma shinkafar ta fi tsada a jihar da aka sayar ₦98,000.
Shinkafar waje ta fi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagos wanda aka sayar ₦75,000 a satin nan, amma a makon jiya ₦76,000 ake sai da buhun.
Ana sayar da Shinkafar waje ₦87,000 a kasuwannin jihohin Katsina da Kaduna da ke arewacin Najeriya a wannan mako, amma dai farashin ya banbanta a makon da ya gabata, inda a kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayarwa ₦85,000, sai Mai’adua jihar Katsina ake sayarwa ₦88,000-₦90,000.
Sai jihar Adamawa ana sayen buhun Shinkafar Bature ₦78,000-₦80,000 a satin nan.
Ga ma’abota cin alala da kosai kuwa ₦200,000 daidai ake sai da buhun farin wake a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagas, yayin da a makon da ya gabata aka sai da ₦220,000, an samu ragin ₦20,000 a makon nan da ke dab da ƙarewa.
A kasuwannin jihar Adamawa ana sai da buhun wake ₦170,180,-190,000 a satin nan, haka aka sai da satin da ya shuɗe.
To a jihohin Kano da Kaduna da ma Katsina, ana sayar da buhun wake ₦170,000 a wannan mako, farashin haka yake a makon da ya gabata a kasuwannin jihohin Kaduna da Katsina, sai dai kuma a jihar Kano farashin waken ₦155,000 ne a makon da ya gabata.
Bari mu kammala farashin kayan abinci na wannan sati da farashin taliyar Spaghetti.
Kwalin taliyar ya fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da ake saidawa ₦19,500, bayan da a makon jiya aka sayar ₦18,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano,sai Giwa jihar Kaduna aka sayar ₦19,000.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos ma farashin bai canza ba dana makon jiya, wanda aka sayar ₦19,000.
₦17,400 aka sayi kwalin taliya a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a makon nan, bayan da a makon da ya shude aka saya ₦17,600.
To kasuwar zamani da ke jihar Adamawa ₦17,700 ake sayar da kwalinta a makon daya gabata, amma a makon nan ₦17,300 ne kuɗin kwalin taliyar.
Alƙaluman da hukumar kididdiga ta kasa ( NBS) ta fitar a watan Yulin 2024 ya nuna cewar hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya yi kasa da kaso 33.40, saɓanin na watan Yuni da kaso 34.19.
DCL Hausa A’isha Usman Gebi.