DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 403

Lokacina bana taba ko sisi na kananan hukumomi – Shekarau

 Lokacina bana taba ko sisi na kananan hukumomi – Shekarau

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce a lokacinsa bai taba ko sisi daga kudaden da suke mallakin kananan hukumomi ba

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin bikin cika shekaru 70 na kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya (MSSN).

“Ban taba bukatar wani kaso daga kowane dan kwangila ba. A koyaushe ina kalubalantarsu, idan akwai dan kwangilar da ya yi aiki da ni a cikin shekaru 44 da suka gabata ya san cewa na tambaye shi ya kawo min wani kaso na kwangilarsa

, to ya fito ya fadi haka,” inji Shekarau. 

Kwastam sun fitar da ka’idojin shigo da kayan abinci da aka sawwake wa haraji

Hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS), a ranar Laraba, ta sanar da amincewar Shugaba Bola Tinubu don aiwatar da dokar shigo da kayan abinci da suka hadar da shinkafa, masara, gero, alkama, da wake ba tare da haraji ba.
Don morar wannan tsari hukumar kwastam ta ce dole masu shigo da ita suna da kamfani da ya zama an yi rijista da shi a Najeriya.
Kazalika, kamfanin ya kasance kuma yana aiki na tsawon shekaru biyar tare da biyan kudin haraji na tsawon shekarun.
Bugu da kari, kmfanonin da za su shigo da kayan abincin dole ne su mallaki masana’antar surfa shinkafar mai ƙarfin yin ton 100 a kowace rana.
Hukumar ta kuma ce aƙalla kashi 75% na kayan da aka shigo da su dole ne a siyar da su ta kasuwannin kayan masarufi da aka sani.
Daga karshe hukumar ta bayyana cewa idan kamfani ya gaza cika wadannan sharuda to zai biya haraji, haka kuma za a hukunta duk kamfanin da ya fitar da kayan da aka shigo da su wajen Najeriya kafin ko bayan sarrafa su.

Majalisa ta janye kudirin dokar hukunta duk wanda bai iya rera sabon taken Nijeriya ba

A baya dai, an gabatar da kudirin dokar da ke neman a ci tarar duk wani dan Nijeriya kudi Naira milyan 5 idan har bai iya rera sabon taken kasar ba.
Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, a shafin X na majalisar wakilai, ya ce an yanke shawarar janye kudirin dokar dama wasu dokoki makamantansu.
Hon. Abbas ya fuskanci suka daga mutane kan kudirin dokar, wanda ya kunshi wasu tsauraran tanadi, irin su sanya laifi kan rashin iya taken kasa.

Matsin lamba ne ya sa Shugaba Tinubu ya umurci a kira babbar taron jami’iyyar APC na kasa – Jigon APC

Gamayyar kungiyoyin jami’iyyar APC na shiyyar arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ce umurnin da Shugaba Tinubu ya yi na a kira taron kusoshin jami’iyyar APC na kasa da hakan zai ba da damar a gudanar da babban taron jami’iyyar na kasa, ya biyo bayan matsin lamba da suka yi kan bukatar hakan.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Jos babban birnin jihar Plateau, shugaban gamayyar kungiyoyin Hon Saleh Abdullahi Zazzaga, ya ce sun yi farinciki da shugaban kasa ya aike da wannan wasika ta hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ga shugaban jami’iyyar, Abdullahi Umar Ganduje.
Saleh Abdullahi ya ce a cikin wasikar mai kwanan wata 09/08/2024, ta ba shugaban jami’iyyar zabin kiran taron kusoshin a ko dai 08 ko kuma 19 ga watan Satumba mai kamawa.
Ya ce sun yi murna da jin wannan mataki kasancewar sun jima suna ta kiraye-kirayen da shugaban kasa ya sa baki kan abin da suka kira karfa-karfa da ake shirin yi musu da mukamin shugabancin jami’iyyar da ya subuce musu tun bayan da Abdullahi Adamu ya ajiye.
Shugaban gamayyar kungiyoyin ya ce idan aka hadu babban taron jami’iyyar na kasa, a nan za su baje hajarsu, su mika kokensu na duk abubuwan da ke damunsu da suke ganin kamar an mayar da su saniyar ware musamman su ‘yan arewa ta tsakiyar Nijeriya duk kuwa da abin da ya kira irin wahalar da suka yi wa jami’iyyar APC.

Masu zanga-zanga sun sace takardun shari’ar Ganduje a babbar kotun Kano – Gwamnatin jiha

Gwamna Abba kabir Yusuf na jihar Kano ya ce wasu ‘yan daba sun yi fashin wasu takardun tuhuma kan zarge-zargen cin hanci da aka shigar da su gaban babbar kotun jihar, waɗanda ke kan tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, iyalansa da wasu na kusa da shi, a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi kwanan nan .
Gwamna Abba ya ce tsohon Gwamnan Ganduje, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, na fuskantar tuhume-tuhume masu yawa a gaban babbar kotun jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yuwan Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara domin duba halin da babbar kotun jihar ta shiga bayan da ‘yan daba suka lalata ta yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar.

An kama dan shekaru 62 da ke buga jabun kudi a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama Tahir Ahmad mai kimanin shekaru 62 da zargin buga jabun kudi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ahmad Wakili ya sanar da hakan a Bauchi, inda wata mota daga Jos ta taso zuwa Bauchi, ta tsaya a Tilden Fulani cikin karamar hukumar Toro, inda ta dauko Tahir Ahmad a matsayin fasinja aka nufa da shi zuwa Bauchi.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce ana cikin mota ne, mutumin ya fitar da wata takarda ya fara karanta wasu dalasimai, take ta koma kudi, Naira dubu daya. A cikin motar ne aka fara zargin cewa wannan kudin na ‘samara’ da mutumin nan ya yi a mota na jabu ne.
‘Yan sandan suka ce daya daga cikin fasinjojin motar da aka isa Bauchi, ya garzaya ya sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki.
Ahmad Wakili ya ce bayan kamo mutumin, aka tsananta bincike a kansa, mutumin ya amsa laifinsa, ‘yan sanda sun kuma samu jimillar kudi Naira dubu 238 a hannun mutumin a matsayin kudin jabu.

Mun toshe jimillar kudaden da suka kai N83bn na wadanda suka dauki nauyin zanga-zanga a Nijeriya – NSA

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya ce ya zuwa yanzu an gano fiye da Naira biliyan 83 na kudin yanar gizo wato cryptocurrency da kuma sauran kudade na zahiri da ake zargin an zuba domin a dauki nauyin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka kammala kwanan nan a fadin Nijeriya.
Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana hakan, yayin gabatar da jawabinsa a taron manyan kasa na Nijeriya da Shugaba Bola Tinubu ya kira a Fadar Aso Rock, Abuja.
Nuhu Ribadu ya shaida cewa kuɗaɗen sun haɗa da dala miliyan $50 na kudin yana gizo (cryptocurrency) daga ciki an toshe dala miliyan $38 a cikin karamin asusun kudi na yanar gizo guda huɗu da kuma Naira biliyan N4 da ake zargin wasu kusoshin ‘yan siyasa daban-daban suka bayar a Abuja, Kano, Kaduna, da Katsina.
A cewar wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ɗin ya shaida wa majalisar cewa ana zargin kasashen waje da hannu wajen kitsa daga tutar kasashen waje a yayin zanga-zangar.
Kazalika an gano wani jami’in ƙasashen waje da ke da alaƙa da wannan al’amari, kuma za a ayyana shi a matsayin wanda ake nema nan ba da jimawa ba ‘yan sanda za su sanar da hakan a wannan makon.

Ina samun Naira miliyan 21 duk wata a mukamina na Sanata – Kawu Sumaila

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya Kawu Sumaila ya ce a duk wata yana yana samun jimillar kudi Naira milyan 21.
A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, ta jiyo Sanata Kawu Sumaila na cewa albashin Naira milyan daya da hukumar tattarawa da rarraba kudaden shiga ta kasa ta ce ana ba Sanatoci, ta ragu zuwa N600,000, amma akwai alawus-alawus da ake biya da suka kai Naira milyan 21 ga duk kowane Sanata.
Sanata Kawu Sumaila ya yi magana ne sa’o’i 24 bayan da hukumar da ke da alhakin kayyade albashin masu mukaman siyasa ta fito karara ta sanar cewa albashin kowane Sanata bai wuce N1m ba.
Sai dai Sanatan ya ce da jimillar wadannan kudade ne kowane Sanata ke amfani yana tafiyar da lamurran ofishinsa.

Ba mu kayyade farashin litar fetur dinmu ba – Matatar man Dangote

Hukumar gudanarwar matatar man Dangote ta musanta batun kayyade farashin litar man fetur.
Babban jami’in sashen sadarwa na kamfanin Anthony Chiejina, ya sanar da hakan yayin da yake mayar da martani ga wani rahoto kan hasashen ‘yan kasuwa na sayar da litar fetur din kan kudi N600 na man Dangote da aka wallafa a jaridar Punch a ranar Talata, 13 ga Agusta, 2024.
Chiejina ya bayyana cewa kungiyar ‘yan kasuwan man fetur ta Nijeriya ba abokan kasuwancinsu ba ne har yanzu. Ba kuma su taɓa tattauna batun farashin Man Fetur da su ba, kuma ba su da wani izini ko iko na magana a madadinsu, ko da ko wacce irin manufa.
Kazalika, sanarwar ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan magana mara tushe. Ta kuma kara da cewa suna da hanyoyin sadarwa na hukuma da suke amfani da su wajen bayyana ra’ayoyinsu ga masu ruwa da tsaki.

Majalisar Dattawa na tuhumar wasu hukumomin gwamnati kan batun kudade

Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da kudaden al’umma, ya nuna fushinsa ga shugabannin Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da wasu hukumomi a kasar.
Hakan ya biyo bayan kin amsa tambayoyin da aka gabatar musu a rahoton binciken kudin na shekarar 2019.
Shugaban kwamitin, Sanata Ahmed Wadada ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Wadada ya kuma ce halayyar hukumomin da abin ya shafa na kin amsa tambayoyi a cikin rahoton binciken yana janyo cikas tare da yin illa ga burikan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya, Ma’aikatar Tsaro, Kamfanin Sadarwa na Tauraron Dan Adam na Najeriya, da sauransu.