DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 418

Mace ta sake ɗare kujerar shugabar ma’aikatan Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake nada mace a matsayin shugabar ma’aikata ta Najeriya.

Misis Didi Esther Wilson-Jack ta maye gurbin Dr Folashade Yemi-Esan tun daga ranar 14 ga wannan wata na Yuli a cewar sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.

Sabuwar shugabar ma’aikatan Najeriya ta kasance babbar sakatariya tun a shekarar 2017 kuma ta yi aiki a Ministoci daban daban tun daga wancan lokaci.

Shawarar shugaba Tinubu na sake ɗaukar mace bata rasa nasaba da dokar nan data bukaci a baiwa mata kashi 25 na mukamai a gwamnatin Najeriya wacca shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tabbatar a zamanin sa

Zamu ƙara Naira tiriliyan shida a kasafin kudin bana – Shugaba Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya na bukatar Majalisar dattawa ta ƙasar ta sake aiki kan kasafin kudin bana, ta yadda za’a ƙãra wasu Naira tiriliyan shida a kasafin kudin na shekarar 2024.

Tanubu ya nemi ayi wannan ƙari ne a bangarori biyu na kasafin kudin, wato ɓangaren kuɗaɗen gudanarwa da kuma na manyan ayyuka waɗanada kowannen su za’a yi ƙãrin Naira tiriliyan uku uku.

A wasikar da ya aike ga majalisar shugaba Tinubu ya ce za’a ciri wadannan kuɗaɗen ne daga kudin haraji da ake tarawa.

Tuni majalisar ta rubuta wannan bukata cikin jerin batutuwa da zata yi zama kansu.

Idan majalisar ta amince da wannan buƙata ta shugaba Tinubu dai kasafin kudin na shekarar 2024 zai tashi daga sama da Naira tiriliyan 27 zuwa sama da Naira tiriliyan 33.

Majalisar dattawa ta Najeriya ta sauke tare da maye gurbin Sanata Ali Ndume

Majalisar dattawan Nijeriya ta sanar da tsige Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a matsaymin babban mai tsawatarwa na majalisar.

Shugaban majalisar dattawan,Sanata Godswill Akpabio ya sanar da hakan bayan kada kuri’a da ‘yan majalisar dattijan na APC suka amince da tsige Ndume a matsayin babban mai tsawatar wa a majalisar.

An dai maye gurbin Ndume da Tahir Mungono wanda ya ke wakiltar Borno ta Arewa

hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Ndume ke sukar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wata wasika da shugabannin jam’iyyar na kasa na kasa, APmC ta aike wa majalisar dattawa, ta bukaci Ndume ya yi murabus daga jam’iyyarsa ta APC, ya koma kowace jam’iyyar adawa da yake so.

Takardar ta samu sa hannun shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da kuma sakataren jam’iyyar Barista Ajibola Bashiru.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu masu biyayya ga Tinubu suka kulla makarkashiyar na dakatar da Ndume daga mukamin sa a majalisar.

             

Kotu ta ce mataimakin gwamnan jihar Edo bai tsigu ba

Kotu ta mayar da mataimakin gwamnan jihar Edo Philip Sha’aibu da aka tsige

Alkalin babbar kotun tarayya a Abuja James Omotosho ya kuma soke naɗin sabon mataimakin gwamna da aka yi a madadin Sha’aibu

Alkali Omotosho ya bada umurnin a maida Philip Sha’abu kujerarsa saboda majalisar dokokin jihar Edo bata bi ƙa’ida ba wurin tsige shi

Gwamnan Kano ya nada sabbin sarakuna 3 masu daraja ta biyu a jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da nadin sabbin sarakuna 3 masu daraja ta biyu a jihar.
Hakan na zuwa ne bayan rattaba hannu kan sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita na kafa sabbin masarautu masu daraja ta biyu a jihar ta Kano.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta ce Gwamnan ya amince da nadin Alhaji Muhammd Mahraz Karaye a matsayin sabon Sarkin Karaye mai daraja ta biyu, wanda kafin nadin nasa shi ne Hakimin Rogo.
Sanarwar ta kuma ambato Alhaji Muhammd Isah Umar a matsayin sabon Sarkin Rano, wanda kafin nadin nasa shi ne Hakimin Bunkure. Da kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda shi ne tsohon Sarkin rusasshiyar Masarautar Gaya, da yanzu aka nada shi matsayin Sarkin Gaya mai daraja ta biyu.
Sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce nadin nasu ya fara aiki nan take.

Gwamnatin tarayya ba ta sayar da jami’o’i ga ‘yan kasuwa ba – Ministan Ilimi

Gwamnatin tarayya ba ta sayar da jami’o’i ga ‘yan kasuwa ba – Ministan Ilimi

Gwamnatin tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa tana sayar da jami’o’in gwamnati ga ‘yan kasuwa.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce an samu wasu na ta yada jita jitar cewa gwamnatin tarayya ta fara sayar da wasu jami’o’i ga ‘yan kasuwa.

Ministan wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da shugabannin hukumomi, ma’aikata da daraktoci a ma’aikatar ilimi a Abuja, ranar Talatar nan, ya ce, Wannan karya ce kwata-kwata kuma babu makamanciyar wannan magana.

Yace shekaru da dama da suka gabata, kamfanoni masu zaman kansu sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da manyan makarantun gaba da sakandare kuma akwai jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya fiye da yadda ake hada jami’o’in gwamnati.

Abin da gwamnati ta yi shi ne bude makarantun gaba da sakandare musamman, jami’o’i don samun gogayya a duniya da ke bai wa wadanda ke aiki a wannan fanni a matakin kasa da kasa damar shigowa kasar tare da kafa cibiyoyi da aka bude domin hadin gwiwa da jami’o’inmu na cikin gida karkashin jagorori.

Na dade ina mafarkin za ma dan wasan Real Madrid-Kylian Mbappe

Na dade ina mafarkin za ma dan wasan Real Madrid-Kylian Mbappe

Kylian Mbappe ya ce burinsa na komawa Real Madrid a lokacin yaro ya cika yayin da aka bayyana shi a filin wasa na Bernabeu mallakin Real Madrid.

Dan wasan na Faransa, mai shekara 25, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a kungiyar a watan Yuli bayan karewar kwantiraginsa na Paris St-Germain ta kasar Faransa.

Da yake magana a gaban magoya bayan kungiyar sama da 80,000 a Bernabeu, Mbappe ya shaida wa magoya bayansa cewa ya yi mafarkin lokacin da zai iya kiran kansa dan wasan Real Madrid.

Mbappe ya ce ,na shafe dare da yawa ina mafarkin wata rana ina buga wa Real Madrid wasa kuma a yau ina farin ciki ba iyaka

Rana ce mai ban mamaki a gare ni, na yi mafarkin wannan rana tun ina yaro kuma bazan taba mantawa ba

Mbappe, wanda aka saka a cikin sabuwar kayan gida na kulob din kuma ya yi jawabi ga ‘yan kallo cikin harshen Sipaniya, shugaban kulob din Florentino Perez ya gabatar da shi ga jama’a.

Da yake magana da Mbappe kafin Bafaranshen yayi magana da jama’a, Perez ya ce: “Ƙaunar da kuka yi wa Real Madrid, kuma kun kasance tare da wannan kulob ɗin tun kuruciyar ku, ya ba ku damar kasancewa a nan kuma ku shawo kan waɗannan matsalolin a hanya. ga mafarkinka.”

Gwamnatin tarayya ta maido da wasu ‘yan Nijeriya 190 daga hadaddiyar daular larabawa

Gwamnatin tarayya ta maido da wasu ‘yan Nijeriya 190 daga hadaddiyar daular larabawa 

Gwamnatin tarayya ta dawo da jimillan ‘yan Nijeriya 190 daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

A cewar wata sanarwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, mai dauke da sa hannun babban daraktan hukumar na shiyyar Arewa ta tsakiya, Bashir Garga, a ranar Talatar nan ta ce, an tarbi wadanda suka dawo a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 5:57 na safe. Tare da tawagar jami’an gwamnati karkashin jagorancin NEMA.

Gwamnatin tarayya ta bukaci dukkan ‘yan kasar, a duk inda suke, da su zama jakadun kasa na gari, tare da kiyaye muhimman dabi’u na kishin kasa,da bin doka da oda, mutunci da mutuntawa.

Idan za a iya tunawa cewa a cikin watan Oktoban shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta dawo da jimillar mutane 542 daga hadaddiyar daular larabawa.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ta cimma yarjejeniya da kasar hadaddiyar daular larabawa domin baiwa masu fasfo din Nijeriya damar samun bizar zuwa kasar daga ranar 15 ga watan Yulin 2024.

Ministan yada labaran Nijeriya Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayyar bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako.

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kirkirar sarakuna masu darajar ta biyu

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kirkirar sarakuna masu darajar ta biyu

A ranar Talata 16 ga watan yuli shekarar 2024 ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.

SolaceBase rawaito cewa majalisar ta yi karatun farko na kudirin kafin tafiya hutu da tayi wanda suka dawo aiki a makon jiya.

Bayan karatu na biyu da na uku na kudurin, mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Bello Butubutu, ya  amince da shi tare da zartar da kudurin.

Kakakin majalisar Jibril Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman majalisar a ranar Talatar 

Sabbin masarautun masu daraja ta biyu da za a kirkiro sun hada da:

1. Masarautar Rano: Rano- Bunkure, Kibiya

2. Masarautar Karaye: Karaye- Rogo

3. Masarautar Gaya: Gaya- Ajingi, Albasu

Gwamnan Jigawa ya ba ma’aikata bashi don su yi noma a daminar bana

Gwamnan Jigawa ya ba ma’aikata bashi don su yi noma a daminar bana

Gwamnatin jihar Jigawa ta raba bashi da kayan noma ga ma’aikata 8,432 domin inganta noma a jihar da kuma bunkasa samar da abinci,kwamitin na shirin tallafa wa aikin gona na jihar Jigawa ne ya aiwatar da shirin wanda shugaban ma’aikata na jihar Muhammad K Dagaceri ya jagoranta.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da rancen ga ma’aikatan da suka amfana da shirin Gwamna Umar Namadi a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli, a babban ofishin kamfanin samar da kayan aikin gona na Jigawa (JASCO Limited) Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa an fito da wannan tsarine domin tallafawa ma’aikata da bunkasa aikin noma a jihar.

Ya ce, an zabo mutane 8,432 da za su ci gajiyar shirin bayar da rancen wanda shine na farko kuma za a cigaba da yi.

A cikin wannan adadin mutanen, an zabo mutum  1,815 da zasu amfana da dubu N500,000 don yin noman shinkafa ,yayin da aka zabo 3,403 da suka amfana da N250,000 domin noman gero.

Haka kuma an zabo mutane 2,068,da suka amfana da dubu 250,000 da zasu yi noman dawa.

Shugaban ma’aikatan jihar Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa,kwamitin ya sanya kudirin zabar ma’aikata 14,000 a matsayin kashi na farko na wadanda za su amfana da shirin kuma wanda shine daya bisa hudu na ma’aikatan dake jihar.