DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 419

Ku dakatar da zanga-zangar adawa da Gwamnatin Tinubu – APC ta gargadi ‘yan Nijeriya

Jam’iyyar APC shiyyar Arewa ta tsakiya ta gargadi matasa da wasu kungiyoyi da ke shirin yin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jam’iyyar ta ce irin wannan shawarar ba za ta yi tasiri ba kuma illa ce ga ci gaban kasar a halin yanzu,  tana mai kira ga masu shirya gangamin da su sake tunani tare da dawo da matasa kan hanyar dai-dai.

Shugaban Jam’iyyar, Alhaji Saleh Mandung Zazzaga, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Jos, babban birnin Jihar Filato, ya ce ya kamata masu kira a gudanar da zanga-zangar su lura da halin da ake ciki a kasar.



Zazzaga ya ce, shugaba Tinubu na kokarin mayar da kasar nan kan turbar ci gaba, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su mara masa baya.

‘Yan sanda sun hana muzaharar Ashura a Kaduna

Rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ta haramta wa kungiyar ‘Islamic Movement of Nigeria’ wacce aka fi sani da Shi’a shirya taruka a jihar ciki har da muzaharar Ashura da kungiyar ta shirya gudanar wa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna.

Hassan ya ce, “Hukumar ta haramta duk wata zanga-zangar da ba ta dace ba a jihar.

Shigo da abinci na iya lalata fannin noma a Najeriya – AfDB

Shugaban bankin raya kasashen Afirka, Dr Akinwumi Adesina, ya gargadi gwamnatin tarayya kan kudirinta na ba da damar shigo da abinci, ya ce hakan ka iya lalata harkar noma a kasar.

Adesina ya fadi hakan ne a wajen wani taro a Abuja, ya kuma shawarci gwamnatin Najeriya da ta samar da ayyukan yi ta hanyar noma.

Idan za a iya tunawa, a ranar 10 ga Yuli, 2024, Ministan Noma Abubakar Kyari, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta dakatar da haraji kan shigo da masara, buhunan shinkafa da alkama na tsawon kwanaki 150.

Gwamnatin tarayya na kokari wajen magance tsadar farashin kayan masarufi – Ministan Noma


Gwamnatin tarayya na kokari wajen magance tsadar farashin kayan masarufi –  Ministan Noma

Gwamnatin tarayya ta amince akwai karancin abinci a kasar, sai dai ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana kokarin shawo kan lamarin kuma nan ba da dadewa ba farashin kayayyaki zai sauka. 

Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya kai sama da kashi 40 cikin 100 a watannin baya-bayan nan.

Sai dai karamin ministan noma Aliyu Abdullahi ya ce akwai wasu shirye-shirye da gwamnatin tarayya ke yi na ganin farashin kayan masarufi sun ragu.

‘Yan majalisa ne suka matsa wa gwamnatin tarayya lamba har ta sanya hannu kan SAMOA – Ministan Tinubu

Jaridar Premium Times ta ce ta samu wata wasika daga Majalisar Dokoki ta kasa zuwa ga Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu, inda ya nemi gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniyar.

Majalisar ta bukaci gwamnati da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar a ranar Alhamis, har sai kwamitin ta ya gudanar da bincike akai.

Sai dai wasikar ta nuna sabanin matsayin majalisar kan yarjejeniyar.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 9 ga Mayu 2024, kuma Muhammed Argungu ya sanya wa hannu, Majalisar ta bukaci ministan da ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ga kungiyar kasashen Afirka da Caribbean da Pacific da Tarayyar Turai.

‘Yan bindiga sun saka haraji Naira miliyan 200 akan al’ummar jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun saka harajin kusan N200m a wasu al’ummomi a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Jaridar Daily Truth ta ruwaito Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Yan Dolen Kaura: Naira miliyan 15; Gidan Zagi: Naira miliyan 15; Million Kanwa: Naira miliyan 20; Kaiwa Lamba: Naira miliyan 26; Gidan Dan Zara: Naira miliyan 22; Jinkirawa: Naira miliyan 16; Dumfawa: Naira miliyan 16; Ruguje: Naira miliyan 7; Babani: Naira miliyan uku da Gidan Duwa: Naira miliyan hudu.

An bayyana cewa wasu kauyukan sun riga sun biya kudaden harajin nasu, yayin da wasu kuma ke fafutukar tattara kudaden da ake bukata.

Wannan lamarin, in ji majiyoyi, ya tilasta wa mazauna kauyukan neman aikin yi a garuruwan da ke kusa da su, don tara kudaden domin biyan bukatun ‘yan fashin.

Wani mazaunin garin Zurmi mai suna Malam Yunusa Musa ya shaida wa Daily Truth cewa harajin ya fara aiki daga wannan makon.

Dalilin da ya sa ba ni da gidaje a London, Amurka – Dangote

 

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya ce gurinsa na bunkasa masana’antu a Najeriya ne ya sa ba ya da gidaje a kasashen waje.

Dangote ya bayyana cewa samun gidaje a Landan ko Amurka zai dauke masa hankali wajen samar ma Najeriya masana’antu.

Attajirin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a matatar man Dangote da ke yankin Ibeju-Lekki a jihar Legas.

Ya ce, “Dalilin da ya sa ba ni da gida a Landan ko Amurka shi ne kawai don ina so in mayar da hankali kan bunkasa masana’antu a Najeriya.

A gidan haya nake zaune a Abuja – Dangote

Hamshakin attajirin nan na Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote ya ce gidan da yake zaune a duk lokacin da ya ziyarci Abuja, ba nasa bane, haya yake yi.
Aliko Dangote a wata ganawa da manema labarai a Lagos, ya ce irin himmar da yake da ita na ganin masana’antu sun habbaka a Nijeriya ne ya sa baya da burin gina gidaje a wajen kasar.
Dangote ya bayyana cewa ya taba mallaka gida a birnin London amma ya sayar da shi a shekarar 1996.
Ya ce dalilinsa na kin yin gidaje a Amurka ko Ingila shi ne don ya kafa masana’antu kuma ya rage lokacin da zai rika batawa don ziyarar kadarorin da ya adana a kasashen waje.

Anyim zai samu dama daidai da kowa a jam’iyyar APC – Ganduje

Anyim zai samu dama daidai da kowa a jam’iyyar APC – Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya tabbatar wa tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim,cewa zai samu dama daidai da sauran mutanen dake cikin jam’iyyar.

Ganduje ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi pius a cikin jam’iyyar APC bayan da yabar jam’iyyar adawa ta PDP a ranar Asabar.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban jam’iyyar APC, Edwin Olofu ya fitar a Abuja ranar Lahadi ya fitar.

Ganduje ya bayyana zuwan Anyim da sauran mutanen jam’iyyar APC a matsayin wata babbar ni’ima ga jam’iyyar.

Ya ce, na yi farin ciki da karbar irin wannan muhimmin babban mutum ga jam’iyyarmu, ina so in tabbatar muku a madadin shugaban kasa Bola Ahmed Timubu cewa, muna maka maraba da zuwa babbar jam’iyyar siyasa a Afirka.

Ku tabbata cewa za mu ba ku dama daidai gwargwado kamar tsofaffin ’ya’yan jam’iyyarmu domin ku zo mu hadu muyiwa jam’iyya aiki dan kaiwa ga Nassara.

Jam’iyyar PDP ta lashe zabukan kananan hukumomin Jihar Adamawa 21 da aka gudanar

Jam’iyyar PDP ta lashe zabukan kananan hukumomin Jihar Adamawa 21 da aka gudanar

Kamar yadda sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta fitar yanzu haka, jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta lashe dukkan kujerun kansiloli a mazabu 226 dake jihar, in ban da gundumar Demsa dake karamar hukumar Demsa inda jam’iyyar NNPP ta lashe kujerar kansila daya.

Shugaban hukumar zaben Mohammed Umar, ya ce jam’iyya mai mulki ta samu gagarumar nasara a dukkanin kananan hukumomin jihar 21, ya bayyana sakamakon ne a yammacin Lahadi a hedikwatar hukumar da ke Yola, babban birnin jihar.

Umar ya ce daga cikin jam’iyyun siyasa 19 da suka yi wa rajista a jihar, 12 ne suka shiga wannan atisayen.

Zaben kananan hukumomin jihar Adamawa shi ne na farko bayan da kotun koli ta bai wa mataki na uku ‘yancin cin gashin kai na harkokin kudi, inda ta umurci gwamnatin tarayya da ta biya kashi 20.60% na kason kudaden kananan hukumomi 774 na kasar nan kai tsaye zuwa asusunsu na kebantattu, ba wai ga asusun ajiyar su ba. ta gwamnoni.

Kotun kolin da ta yanke hukunci a ranar Alhamis din da ta gabata ta kuma haramtawa gwamnoni masu shaye-shayen madafun iko rusa kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.