DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 417

Tinubu zai halarci taron hadin kan kasashen Afrika a Ghana

Tinubu zai halarci taron hadin kan kasashen Afrika a Ghana

A ranar Asabar din nan ne shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Accra na kasar Ghana domin halartar taron koli na tsakiyar shekara na kungiyar tarayyar Afirka (AU) karo na shida.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma, Ajuri Ngelele ya fitar ta ce, shugaba Tinubu zai yi jawabi a taron kan matsayin hadin kan yankin a sassa daban-daban na Afirka, inda ya bayyana nasarori da kalubalen da aka fuskanta a yammacin Afirka tun bayan ganawar karshe da aka yi a Nairobi, Kenya, a watan Yuli shekarar 2023.

Shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, zai gabatar da ‘Rahoto na 2024 game da halin da al’umma ke ciki, wanda zai mai da hankali kan zaman lafiya, tsaro na yankin Afrika, da gudanar da mulki.

Ndume ya ki amincewa da sabon nadin da akayi masa a majalisar dattawa

Ndume ya ki amincewa da sabon nadin da akayi masa a majalisar dattawa

Dan majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ki amincewa da nadin da aka yi masa a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yawon bude ido.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya baiwa Ndume sabon mukami biyo bayan tsige shi daga mukamin babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa ta 10.

Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun bukaci Akpabio da ya tsige Ndume saboda sukar da ya yi wa Shugaba Bola Tinubu a kwanakin baya.

Ndume, yayin da yake mayar da martani game da tsige shi a wata tattaunawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Juma’ar nan, ya ce bai yi nadama ba.

Yace an roke ni da in karbi mukamin Cif Whip na sani sarai cewa na jagoranci yakin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa kuma aka roke ni na zabi kwamitin da nake so kuma na zabi kwamitin kasafin kudin a wancan lokacin Amma ba a bani ba.

Ndume ya kuma bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba batutuwan da ya gabatar, inda ya kara jaddada cewa talakawa na cikin yunwa da fatara.

Yace ba rashin kishin kasa ba ne a tsaya wa Shugaban kasa da duk abin da zai yi, kishin kasa ne a fadi gaskiya ba ga Shugaban kasa kadai ba har kowa.

Mafi karancin albashi na nairai 70,000 ya razana kamfanoni a Nijeriya

Mafi karancin albashi na nairai 70,000 ya razana kamfanoni a Nijeriya 

Kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta Nijeriya Organised Private Sector of Nigeria (OPSN) ta bayyana damuwarta kan yadda zata iya biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000, inda ta ce kungiyoyar kamfanoni masu zaman kansu na fama da matsanancin tsadar kayayyaki.

Darakta janar na kungiyar tuntubar ma’aikata ta Nijeriya (NECA), Adewale-Smatt Oyerinde, wanda ya yi magana a madadin kungiyar, ya yabawa gwamnatin tarayya kan amincewa da sabon mafi karancin albashin ma’aikata, inda ya bukace ta da ta sake duba fasalin da zai karfafa wa kamfanoni masu zaman kansu don samun damar biyan albashi.

Sun yaba wa shugaban kasa kan yadda ya yi alkawarin tallafa wa kananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu don biyan sabon albashin mafi karancin albashin.

Shugaban NECA ya bayyana cewa, a yayin tattaunawa da kwamitin mafi karancin albashi na kasa, OPS ya nuna damuwarsa kan yadda za ta iya biyan N62,000 da kwamitin bangarorin uku ya ba da shawarar akai.

‘Yan sanda a katsina sun kama wani matashi dake kaiwa ‘yan bindiga bayanai

‘Yan sanda a katsina sun kama wani matashi dake kaiwa ‘yan bindiga bayanai

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 13 da ake zargin yana bayar da bayanai ga ‘yan bindiga.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ya bayyana hakan a Katsina.

A ranar 3 ga watan Yuli, rundunar ‘yan sandan tare da hadin guiwar ‘yan kungiyar sakai a jihar da ke kauyen Dansoda a karamar hukumar Dandume sun yi nasarar cafke matashin mai shekaru 13.

An kama wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri kan munanan ayyukansa. Ya kware wajen bayar da bayanai ga ‘yan bindigar.

A yayin gudanar da bincike, ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, sannan kuma ya ambaci wani Abba, wanda a yanzu haka yake a matsayin wanda ya taimaka masa.

Rundunar ta kuma yi nasarar cafke wani Musaddik Abdullahi da ke zaune a unguwar Kofar Kaura a Katsina, mamban wasu mutane hudu da suka yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu dakunan karatun dalibai a jami’ar tarayya ta Nassarawa

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu dakunan karatun dalibai a jami’ar tarayya ta Nassarawa

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu dakunan karatu a tsangayar koyar da fasaha ta Jami’ar Tarayya ta Lafia a jihar Nasarawa, lamarin da ya kawo cikas ga yin karatu ga daliban a sassan da abin ya shafa.

Wasu dalibai da suka bayyana rashin jin dadinsu kan lamarin,sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta dagula karatunsu sosai, wanda hakan ya sa suke shan wuya wajen gudanar da karatu a zauren da ambaliyar ruwa ta mamaye.

Sun yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su shawo kan lamarin, musamman ganin yadda jarrabawar su ta gabato. 

Sun yi gargadin cewa ba tare da daukar mataki cikin gaggawa ba, za a iya yin illa ga karatun su tare da ruguza gine-ginen jami’ar.

NAFDAC ta rufe wani gidan burodi bisa zargin amfani da sikari da baida rijista

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa (NAFDAC) ta rufe wani gidan burodi saboda amfani da sikari da baida rijista a Sokoto.

Ko’odinetan hukumar NAFDAC, Garba Adamu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewa an gano gidan burodin ne a wani sumame na musamman da jami’an hukumar suka kai.

Yace sun gano cewa gidan burodin yana amfani da sukarin waje wanda ba a yi masa rajista ba.

Yace sun sanya wa wasu gidajen biredi shida takunkumi saboda rashin tsafta,kuma suna cigaba da duba wasu wurare harmtattu domin kamasu,inda yace zasu fadada aikin ne zuwa kananan hukumomin a wani bangare na kokarin hukumar na ganin ana sayar da kayan abinci masu tsafta kamar yadda ya kamata.

Ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen ba da kayayyakin da ba a yi wa rajista ba, kuma a ko da yaushe su kai rahoton duk wani abu da ake zargi da kuma gurbacewa ga hukumar ta NAFDAC.

Hare-haren ‘yan bindiga na kara ta’azzara a yankunan jihar Neja

Hare-haren ‘yan bindiga na kara ta’azzara a yankunan jihar Neja

Mazauna garin Kagara a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja sun nuna damuwarsu kan hare-haren da wasu da ba a san ko su wanene ba ke kaiwa a yankin

A cewar wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, yace wadannan hare-haren sun yi sanadin kashe-kashe da jikkata da dama a tsakanin al’ummar yankin. Rahotanni sun bayyana cewa maharan suna zuwa da bindigu ne a kan babura, inda suke kai wa mutane hari ba tare da kakkautawa ba, ko da a tsakar rana cikin rana.

Kwanaki uku da suka gabata daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su tsohon kansila ne da aka ce an yi garkuwa da shi ne a lokacin da yake alwala na sallar Isha’i. Daga baya an sake shi bayan an yi masa tambayoyi game da rayuwarsa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya danganta lamarin da wuce gona da iri da wata kungiyar ‘yan banga da ake kira Yansakai ta yi, maimakon masu garkuwa da mutane.

Farashin masara ya karye a wasu kasuwannin arewacin Nijeriya

Har yanzu masara ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legos a kudancin Najeriya a ‘yan makonnin nan,inda ake sayar da buhun masara mai cin tiya 40 ₦110,000,amma a makon daya gabata ₦108,000 aka sayi buhun masara.
A kasuwar mai’adua jihar Katsina an sai da buhun ₦92,000 a wannan makon,inda a makon jiya aka saya ₦98,0000,an samu sauƙin ₦6000 a makon nan.
Sai dai buhun masara ya fi sauki a kasuwar Dandume jihar Katsina, inda aka sai da ₦85-87,000 .
To a kasuwar Dawanau jihar Kano ₦85,000 ake sai da buhun masara a wannan satin,bayan da a makon da ya wuce aka sayar ₦90,000,an samu ragin ₦5000 kenan.
Sai Kasuwar Gombi jihar Adamawa aka sai da ₦80-85,000,bayan da a makon jiya aka saya ₦95-98,000.
₦90,000 daidai aka sai da buhun masara a kasuwar Giwa jihar a makon daya gabata,amma a wannan makon ₦80,000 ne kuɗin buhun yake a kasuwar.
hakan na nuna cewa farashin masara a ya sauka,amma a wasu daga cikin kasuwanni da ke arewacin kasar a satin nan.
To bari muje bangaren Shinkafa amma ‘yar gida, ita ma dai shinkafar tafi tsada a kasuwar Mile 12 International Market a jihar Lagos da aka saya ₦160,000 a satin nan,bayan da a makon daya wuce aka sayar da buhun ₦155,000.
A kasuwar karamar hukumar Girie da ke jihar Adamawa ₦155,000 ne ake sayar da buhun tsabar shinkafa a makon nan,amma makon daya kare ₦160,000 cif aka sayi buhunta.
Shinkafar Hausa tafi sauki a kasuwar Mai’adua jihar Katsina wanda aka sayar da buhun ₦143,000 a sanin nan,sai dai satin daya shuɗe ₦140,000 daidai ne kuɗin buhun a kasuwar.
Sai kasuwar Dandume jihar Katsina aka saya a kan kudi ₦125-155,000 a wannan makon.
A jihohin Kano da Kaduna an sayi buhun Shinkafa ‘yar gida ₦145,000 a makon nan da ke shirin karewa,yayinda a Makon daya gabata aka sayi buhun ₦150,000 a kasuwannin.
Ita kuwa Shinkafar waje tafi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagos a kudancin Najeriya da aka saya ₦75, 000,bayan da a makon jiya aka saya ₦78, 000.
Sai dai kuma Shinkafar baturen tafi tsada a kasuwannin Arewacin kasar,inda aka sai da Buhunta ₦95, 000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a makon nan,haka batun yake a makon jiya.
An sayi buhun Shinkafa ‘yar waje ₦87,000 a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan satin,bayan da a makon jiya aka saya ₦85, 000,an samu karin ₦2000 kenan.
Ita kuwa kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa farashin buhun Shinkafar bai sauya tufafi ba dana makon jiya da aka saya ₦78, 000.
Idan muka leka kasuwar Giwa jihar Kaduna an sayar da buhunta ₦80,000 cif a wannan makon,bayan da a makon jiya aka saya ₦86,000, an samu sauƙin ₦6000 a mako guda.
Farashin farin wake ma dai yana ci gaba faduwa a sassan kasuwannin kasar, musamman a Kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas,an sayi buhun sa ₦230,000 a makon nan,sai dai an ɗauki tsawon makonni uku ana sayan buhun ₦250,000.
Sai kasuwar Mai’adua jihar Katsina aka saya ₦180,000 a satin nan,haka farashin yake a makon jiya.
Waken yafi sauki a kasuwar Karamar Hukumar Gombi da ke jihar Adamawa a wannan makon da aka sai da ₦140-150,000,amma a wancan makon ₦170,000 an samu sauƙin ₦20,000 kenan a satin nan da ke mana bankwana.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna an sayi buhun farin wake ₦160,000 cif a makon nan,amma a makon jiya ₦180,000 ne kuɗin buhunta,haka nan an samu ragin ₦20,000 kenan a kasuwar.
₦165,000 ake sayar da buhun wake a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano a makon nan, bayan da a makon da ya shude aka saya ₦178000.
To bari mu ƙarƙare da farashin kayan abinci na wannan satin da farashin kwalin taliya.
Farashin kwalin taliya dai na ci gaba da jan akalarsa a wasu kasuwannin kasar nan, musamman a jihar Lagos da ke yankin kudu,wanda ake sai da kwalin na Taliya ₦18,000 tsawon makonni ba tare da ya sauka ba.
Ita ma dai kasuwar Mai’adua jihar jihar Katsina ₦18,000 daidai ake sayar da kwalin taliya,amma a makon daya wuce ₦16,000 aka saida.
Sai kuma kasuwar Giwa jihar Kaduna da ake sayarwa ₦17,500 a wannan makon,haka farashin yake a makon daya shude.
To a kasuwar Zamani da ke nan jihar Adamawa ₦17,500 aka sai da kwalin na Taliya a makon jiya,amma a satin nan ₦17,200 ne kuɗin sa,an samu sauƙin ₦300 a wannan satin.
₦16,300 aka sayar da kwalin taliyar a Kasuwar Dawanau jihar Kano a wannan makon,bayanda a makon jiya aka saya ₦14,000 daidai,karin ₦2300 a mako ɗaya.
Alkaluman da hukumar Kididdiga ta kasa (NBS ) ta fitar a watan Yunin shekarar 2024 na nuna cewar hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya kai kashi 34.19.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kamu da cutar corona

Sakamakon gwajin cutar corona da aka yi wa shugaban kasar Amurka Joe Biden ya nuna cewa shugaban kasar na dauke da cutar.
Ko a shekarar 2022, sai da shugaban kasar mai shekaru 81 ya kamu da cutar ta corona.
A cikin wata sanarwa daga Sakataren fadar shugaban kasar Karine Jeane-Pierre ta ce an yi wa Joe Biden rigakafi, amma dai an ga alamomin cutar ciki hada zubar majina daga hanci, tari da kuma rashin kazar-kazar.
Sanarwar ta ce shugaban kasar zai koma gidansa na Delaware da zama, a inda zai killace kansa kuma ya cigaba da gudanar da harkokin mulki daga can.

Likitoci da sauran malaman asibiti ne ba su cika karbar cin hanci da rashawa ba – Kungiyar NMA

Kungiyar likitocin Nijeriya ta NMA ta bayyana cewa sabon rahoton baya-bayan nan ya nuna yadda aka gano likitoci da sauran malaman asibiti da aka ce ba su cika karbar cin hanci da rashawa ba a wajen aikinsu sabanin ma’aikatan sauran wasu bangarori.

Shugaban kungiyar na kasa Prof Bala Audu ya bayyana wannan kididdigar a yayin wata zantawa a Abuja.

Binciken kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito ya nuna cewa kusan kaso 30% na mutanen Nijeriya na zuwa neman magani wajen likitoci da sauran malaman asibiti kuma ba su biyan wani cin hanci kuma ba a ma neman su biya wani cin hanci.

Sai dai Prof Audu ya ce kaso 4% ne kacal aka ba da cin hanci ga likitoci da malaman asibiti kuma ya ce za su yi kokarin rage yawan wannan adadin.