DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 420

Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa Trump

Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa Trump

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.

An kai harin ne ga Trump a wani gangamin siyasa a ranar Asabar, Yuli 13, 2024, a Pennsylvania, Amurka.

Trump ya tsallake rijiya da baya, yana mai cewa, An harbe shi ne da harsashi wanda ya huda saman kunnen sa na dama.

Hukumar bincike ta FBI ta bayyana cewa Thomas Crooks mai shekaru 20 ya yi harbin bindigar, inda ya halaka mutum daya yayin da wasu biyu suka samu raunuka.

Sai dai kuma a cewar wata sanarwa da Tinubu ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, ya ce harin da aka kai wa Trump abin kyama ne kuma ya wuce ka’idojin dimokradiyya.

Shugaban na Nijeriya ya tabbatar da cewa tashe-tashen hankula ba su da gurbi a dimokuradiyya, ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga tsohon shugaban na Amurka.

‘Yan sanda a Adamawa sun kama wasu jami’an hukumar bada agajin gaggawa tare da wasu ‘yan banga bisa zargin zamba

‘Yan sanda a Adamawa sun kama wasu jami’an hukumar bada agajin gaggawa tare da wasu ‘yan banga bisa zargin zamba

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta dakile wani shiri na aikata zamba tsakanin ma’aikatan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA) da ‘yan banga ke shirin yi.

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar, yace rundunar ta samu bayanai game da shirin da ake shirin da wayan da ake zargin suka yi, inda nan take ta tura wata tawaga zuwa rumbun ajiyar kayayyaki dake unguwar Limawa a karamar hukumar Yola ta Arewa.

Rundunar ‘yan sandan ta cafke mutane takwas da suka hada da ma’aikatan ADSEMA uku da ‘yan banga biyar, sannan ta kwato buhunan masara, gero, da masara 98.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris, ya yabawa DPO Jimeta da tawagarsa bisa gaggaucewa da suka yi da kuma nuna kwarewa, wanda ya kai ga kamawa tare da kwato hatsin da aka sace.

Ya bukaci jama’a da su bayar da bayanai kan maboyar batagari ya kuma baiwa al’ummar jihar Adamawa tabbacin ‘yan sanda zasu ci gaba da kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar

Kyaftin din kasar Ingila Harry Kane ya bayyana cewa yana da matukar burin ya dauki gasar Euro 2024

Kyaftin din kasar Ingila Harry Kane ya bayyana cewa yana da burin lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024.

Gabanin fafatawar su da kasar Sipaniya, dan wasan ya shaidawa jaridar The Mirror cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin sun samu nasara a yau.

Yace a yau idan muka samu nasara,itace nasara mafi girma a tarihi da kuma al’ummar mu

Ya kara da cewa Ina matukar alfahari da zama dan Ingila don haka, babu  wani abu da bazanyi ba don samun nasarar kungiyata,don haka a shirye nake tare da ‘yan uwana abokan wasa domin mu fafata sossai don samun nasara a wannan wasa.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon shugaban kotun da’ar ma’aikata

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon shugaban kotun da’ar ma’aikata 

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dakta Mainasara Umar Kogo a matsayin shugaban kotun da’ar ma’aikata (CCT).

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya rabawa manema labarai tace saboda Dokta Kogo kwararren lauya ne kuma manazarci a fagagen shari’a, tsaro, tattalin arziki, siyasa, da diflomasiyyar kasa da kasa hakan yasa aka zakuloshi domin cancantar sa.

Shugaban kasa yayi fatan cewa sabon shugaban zai nuna kwarewa, gaskiya da rikon amana ga kasa wajen gudanar da ayyukan ofishin sa.

‘Yan jaridar da aka yi garkuwa da su a Kaduna sun kubuta

‘Yan jaridar da aka yi garkuwa da su a Kaduna sun kubuta 

‘Yan jaridar da akayi garkuwa dasu a kaduna na jaridar The Nation, Alhaji AbdulGafar Alabelewe, da na jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu, tare da iyalin su sun samu ‘yanci.

An yi garkuwa da ‘yan jaridan tare da iyalin su daga gidajensu ne a unguwar Danhonu da ke garin Millennium na karamar hukumar Chikun a Kaduna, a ranar 7 ga Yuli, 2024.

Daga baya ‘yan bindigan suka fara sako matar Abdulraheem.

Da yake tabbatar da sakin su, ‘yayan Abdulgafar, Barista Mas’ud Mobolaji Alabelewe, ya ce bayan sako su suna asibiti a Abuja domin karbar magani.

Dan sumogal ya banke kwastam da mota ya mutu

 Dan sumogal ya banke kwastam da mota ya mutu

Hukumar kwastam ta ce an kashe wani jami’inta mai mukamin Sufeto a ranar Juma’a a garin Achilafia da ke hanyar Daura zuwa Kano a jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da wani direban wata mota da ake zargin mai fasa kwauri ne da ke shigo da kaya ta barauniyar hanya ya bugi jami’in a lokacin da yake kokarin gujewa kama shi.

Inda nan take aka garzaya da ma’aikacin kwastam din zuwa babban asibitin Kazaure, daga bisani aka dauke shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Katsina inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

Tinubu ya nada Baffa Babba Dan Agundi Daraktan Janar na cibiyar bunkasa da tattalin arziki ta kasa(NPC)

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Baffa Dan Agundi a matsayin sabon Darakta-Janar na Cibiyar bunkasa tattalin arziki ta Kasa (NPC)

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Dan Agundi tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar dokokin jihar Kano. Ya kuma taba zaman babban magatakarda a babbar kotun shari’a ta jihar Kano.

Baffa Babba ya kuma taba zama Manajan Darakta na hukumar KAROTA ta jihar kano, sannan ya rike shugaban tawagar matasan yakin neman zaben shugaban kasa Bola Tinubu a arewa maso yammacin Nigeria.

Shugaban Kasar ya yi fatan sabon babban daraktan zai sanya kishin kasa wajen inganta aiyukan hukumar domin cigaban kasa.

Ina fatan zaka yi amfani da gogewar da kake da ita wajen ciyar da wannan hukumar gaba.

Cutar mashako ta yi wa yara 4 sanadin mutuwa a Kano

 

An samu bullar wata sabuwar cutar mashako inda ta kashe yara hudu a wasu kauyukan karamar hukumar Mingibir ta jihar Kano.

Rahotannin sun ce karin wasu mutanen 28 na kwance a asibiti kamar yadda wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Tasiu Dadin-Duniya ya fitar a ranar Alhamis, inji rahoton Punch.

A cewar sanarwar, yaran sun kamu da cutar ne a kauyukan Kwarkiya, Kuru, Kunya da Minjibir dake karamar hukumar Minjibir.

‘Yan sanda a jihar Legas sun cafke wani barawo da ya ba direban Uber farfesu ya nemi ya sace masa motarsa

 ‘Yan sanda a jihar Legas sun cafke wani barawo da ya ba direban Uber farfesu ya nemi ya sace masa motarsa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, a ranar Asabar din dinnan ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da satar mota kirar Uber bayan ya lallabi direban da ya bashi farfesu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ranar Asabar.

Mista Hundeyin ya ce, rundunar ‘yan sandan Akinpelu ta samu rahoto a ranar 5 ga watan Yuli da misalin karfe 8:00 na dare daga wani direban Uber, wanda ba a ambaci sunansa ba.

Ya ce direban motar ya ba da rahoton cewa ya dauko fasinja, wanda kawai ya bayyana sunansa da Ishaya, daga gidan man NNPC, Maryland, a cikin motarsa Toyota Corolla zuwa wani otal da ke unguwar Oshodi.

Kakakin ya yi nuni da cewa, a otal din, wanda ake zargin ya saya wa direban abinci, da farantin miya da nama da kuma abin sha guda daya.

A cikin haka ne, lokacin da wanda ake zargin ke neman abinda zai wanke hannunsa, direban ya ba shi makullin motarsa ya yi amfani da shi daga nan ya arce da motar.

Gobara ta tashi a fadar Sarkin Kano

Wata gobara da har yanzu ba a hakikance musabbabin afkuwar ta ba ta babbake fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Juma’a, wayewar Asabar.
DW Hausa ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Kano na cewa, an gano yadda aka lalata mukullin shiga fadar na baya.
 Sai dai ‘yan sandan sun ce sun kaddamar da bincike kan lamarin.