DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 421

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da sashin kula da samar da abinci

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da sashin kula da samar da abinci

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sashin kula da tsarin samar da abinci, (PFSCU) a wani bangare na shawo kan matsalolin Kasa ke fama da shi.

Yayin da yake kaddamar da sashin a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Juma’ar nan, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya ce wannan wani bangare ne na shirin gwamnatin na magance matsalar abinci a kasar.

Haka kuma fadar shugaban kasar ta ja hankalin jihohi, da sauran masu ruwa da tsaki da suci gaba da taimaka wa a kokarin da gwamnatin take na magance tashin farashin kayayyaki da kuma karancin abinci a kasar.

El-Rufai ya maka wani dan majalisa a Kaduna da gidan talabijin na Channels a kotu

El-Rufai ya maka wani dan majalisa a Kaduna da gidan talabijin na Channels a kotu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya maka wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna, Henry Marah da gidan talabijin na Channels TV a kotu,kan abinda ya kira bata suna da ake yi masa kan binciken bashin naira biliyan 423.

A cikin takardar sammacin da aka shigar a gaban wata babbar kotun a Abuja mai dauke da kwanan wata 11 ga watan Yuli, 2024, El-Rufai, ta hannun lauyansa, A.U. Mustapha (SAN) ya ce hirar da aka yi a gidan Talabijin na Channels TV a ranar 5 ga watan Yuni mai taken “Binciken Gwamnatin El-Rufa’i” anyi ta ne domin bata masa suna.

El-Rufai na neman abiyashi diyyar naira Biliyan 3,kan abinda ya kira rashin gaskiya da kuma bata masa suna.

An jiyo Marah a cikin hirar yana cewa El-Rufai ya ci bashin ne ba tare da bin ka’ida ba kuma ba a san adadin kudaden ba.

Tun da farko El-Rufai ya shigar da karar ne yana mai cewa kwamitin da majalisar dokokin jihar ta kafa kan binciken bashin da ya ciyo wasu kudade,tare da kwangiloli da sauran batutuwan da suka shafi gwamnatin jihar Kaduna daga ranar 29 ga watan Mayu 2015,zuwa 29 ga Mayu 2023, bai yi masa Adalci ba.

Dama sai mun yi wa wasu kananan hukumomi ciko daga aljihunmu – Gwamnonin Nijeriya

Dama sai mun yi wa wasu kananan hukumomi ciko daga aljihunmu – Gwamnonin Nijeriya

Kungiyar gwamnonin Nijeriya, sun shirya wani muhimmin taro a mako mai zuwa domin duba hukuncin kotun koli da ta bai wa kananan hukumomin kasar cin gashin kai.

Da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da kungiyar gwamnonin Nijeriya tayi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnan jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman, ya ce gwamnonin da ke amfani da dukiyarsu wajen kyautata wa kananan hukumomi sun samu sauki domin an sauke musu wani nauyi.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa gwamnonin jahohin sun ji dadin hukuncin kotun kolin da tayi yace dama can da aljihunan su yawanci suke taimakawa wasu kananan hukumomi.

Yace amma gaba daya, gwamnonin sun ji dadin yadda aka sauke musu nauyin da ke kan su. A cewar sa gaskiya mutane ba su san nawa jihohin ke kashewa wajen ceto kananan hukumomi ba shiyasa ake ta cece kuce kan batun.

Kotu ta bada belin tsohon ministan wutar lantarki kan kudi naira 10bn

Kotu ta bada belin tsohon ministan wutar lantarki kan kudi naira 10bn

Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya a Abuja ya bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman kan kudi naira biliyan 10 da kuma mutum biyu wadanda za su tsaya masa.

An gurfanar da Mamman ne a kan tuhume-tuhume 12 da ke da alaka da hada baki da badakalar kudade.

A yayin da yake yanke hukunci kan neman belin wanda ake kara, Mai shari’a Omotosho ya ce dole ne wadanda za su tsaya masa su mallaki kadarori a Abuja da mafi karancin kudin da ya kai miliyan N750m.

Kotun ta kuma ce dole ne wadanda za su tsaya masa su mika wa kotun takaddun shaidar biyan haraji na shekaru uku.

Kotun ta yanke hukuncin cewa wadanda zasu tsaya masa sai sun mika bayanan banki da fasfo na kasa da kasa ga kotu.

Daga nan ne kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Satumba, 2024, domin a fara shari’ar.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura a jihar

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura a jihar

A ranar Alhamis ne Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura a Jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce kwamitin tsaro na jihar ya yanke shawarar takaita zirga-zirgar babura a Zamfara bayan wani taron gaggawa da aka yi a ranar Laraba.

Sanarwar tace Gwamna Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe a jihar ta Zamfara.

Wannan wani yunkuri ne na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dakile kalubalen tsaro da fadada hanyoyin da gwamnati za ta dauka na karfafa yaki da ‘yan bindiga da sauran munanan dabi’u a jihar.

Gwamnatin Kano ta yi gargadi akan masu yanke bishiyu ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin Kano ta yi gargadi akan masu yanke bishiyu ba bisa ka’ida ba

Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi ga mazauna jihar kan yadda ake yanke   bishiyoyi ba bisa ka’ida ba a jihar, tare da jaddada bukatar dakile illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga muhalli da lafiyar dan adam.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi Nasiru Sule Garo,ne ya bayyana hakan a yayin taro da aka shirya kan tsaftar muhalli a barikin janguza dake Kano.

Muna kira ga jama’a da su goyi bayan kokarin wannan gwamnati ke yi na kara yawan bishiyu domin magance kalubalen sauyin yanayi. 

Domin damunar bana tazo da abubuwa da dama don haka sai al’umma sun lura sossai,ta yadda zasu kaucewa gurbatar muhalli da yanayin ka iya kawowa.

Wata makaranta ta rufta lokacin da dalibai ke tsaka da rubuta jarrabawa a Jos

Wata makaranta ta rufta lokacin da dalibai ke tsaka da rubuta jarrabawa a Jos

Dalibai dama sun makale a wata makaranta da ta rufta a unguwar Busa Buji dake karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.

A cewar shaidun gani da ido, ginin gidan, Saint Academy ya rufta ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Juma’ar nan, inda daliban da ke rubuta jarabawa suka makale.

Bayan samun labarin rugujewar ya, iyaye da dama sun yi tururuwar zuwa makarantar suna domin dauka ‘yayansu.

Har zuwa wannan lokaci ana ci gaba da aikin ceto daliban, kuma jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda sun isa wurin domin ceto daliban da suka makale.

Bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai shine babbar nasarar da Tinubu ya samu ya zuwa yanzu – Ndume

Bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai shine babbar nasarar da Tinubu ya samu ya zuwa yanzu – Ndume

Dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume, ya ce tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi shi ne babbar nasarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya samu tun hawansa mulki a shekarar 2023.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Juma’ar nan, Ndume ya bayyana hukuncin kotun kolin a matsayin babbar nasara da shugaba Tinubu ya samu kawo yanzu tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Sanatan ya kuma yi kira ga Tinubu da ya gaggauta fara aiwatar da hukuncin kotun ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa dole ne al’ummar kasa su fara jin dadin shugabanci nagari.

Yace tun lokacin da gwamnonin jihohin Nijeriya suka sanya kananan hukumomi a aljihu ake ta samun cece kuce da kuma koma baya ga al’ummar kasa.

Na yi matukar farin ciki da ci gaban da aka samu, kuma ina fatan wannan zai zama farkon samun ‘yancin kananan hukumomi a Nijeriya.

Kungiyoyin musulmi a Nijeriya sun bukaci gwamnan Sakkwato da ya karfafawa sarkin musulmi gwiwa

Gamayyar kungiyoyin musulmi a Nijeriya (CMON), mai kunshe da kungiyoyin musulmi 33 a fadin kasar nan, sun bukaci Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato da ya karfafawa sarkin musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku gwiwa

Kodinetan gamayyar kungiyar kuma shugaban kungiyar musulmi (MMPN) Alhaji Abdur-Rahman Balogun ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis a Abuja a wani taron manema labarai.

An dai samu cece-kuce dangane da yunkurin gwamnatin jihar Sokoto na tsige sarkin musulmi Sa’ad Abubakar, wanda kuma shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Nijeriya (NSCIA), bayan korar hakimai 15 da gwamnatin jihar ta yi.

Sai dai gwamnatin jihar Sokoto ta ce rade-radin da ake yi na shirin tsige sarkin musulmin ba gaskiya bane .

Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Sambo Danchadi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da ta gabata , ya ce dokar da aka mika wa majalisar dokokin jihar ba ta da wani tanadi na tsige Sarkin Musulmi illa gyare gyare da suke ciki.

Duk da cewa gwamnatin jihar Sokoto ta musanta cewa ba ta shirin tsige sarkin musulmin, kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC), ta ce har yanzu gwamnatin jihar na ci gaba da wannan yunkurin.

Fursunoni sun tsere daga gidan yarin Koutoukalé a Jamhuriyar Nijar

Rahotanni daga yankin jihar Tillaberi sun tabbatar da tserewar wasu fursunoni da ke tsare a gidan yarin Koutoukalé da ke yankin jihar Tillebari ta Jamhuriyar Nijar.
Bayanan da DCL Hausa ta samu dai na nuni da cewa, gidan yarin na daga cikin gidajen yarin da ke da tsattsauran tsaro kuma mai kunshe da gagga-gaggan ‘yan ta’adda da jagororin su masu hatsarin gaske.
Ma’aikatar cikin gida ta kasar dai tuni ta ce ta ba da umarnin binciko da kuma kamo wadanda suka gudun, don haka ne ma aka ayyana dokar hana zirga-zirga daga bakin karfe 9 na dare a cikin kwaryar birnin Tillaberi.
Gidan yarin Koutoukalé dai da ake kallon sa a mafi tsattsauran tsaro a kasar, dama, an taba dakile wasu hare-hare da ‘yan ta’adda suka kai masa a shekarar 2016 da 2019.