DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 422

Ku riƙa yin sãra kuna duba bakin Gãtari – shugaba Tinubu ga NLC

Shugaban Najeriya Bola Tinubu yana kan hankalin ƙungiyar kwadago NLC ta yi la’akari da yanayin ƙarfin gwamnati wurin neman mafi ƙarancin albashi.

Tinubu ya ce ya san muhimmancin faranta wa ma’aikata kuma ya san yanayi da suke ciki, amma kuma ya kamata ana sara ana duba bakin Gatari.

Shugaban na Najeriya a wata ganawa da shugabannin kungiyar ta NLC Alhamisɗinnan ya ce gwamnatin sa dau kyautatawa ma’aikata abu mai muhimmanci saboda al’umma baki daya tana amfana da aikin su da ya gudana cikin farin walwala.

A jawaban su yayin ganawar da shugaban kasa shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero ya nuna wa shugaban kasa Tinubu muhimmancin a kara sosai kan abin da ya ke a yanzu, a matsayin mafi ƙarancin albashi, saboda rayuwar tsada da ma’aikata ke fama da ita.

Na yi matuƙar farin ciki da hukuncin kotun ƙoli kan yancin ƙananan hukumomi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar kuma madagun adawa a Kasar ya yaba hukuncin kotun koli da ya baiwa kananan hukumomin ƙasar ikon sarrafa kuɗaɗen su ba tare da an hada su da gwamnoni ba.

Atiku, a shafin sa na twitter, ya ce wannan mataki na kotun ƙoli nasara ce ga yan Najeriya kuma abin a yaba ne matuka saboda ya kawar da mummunan tsarin nan da gwamnatocin jihohi ke amfani da shi suna sakaye kuɗaɗen ƙananan hukumomi a asusun gwamnatin jiha.

Madugun adawan na Najeriya yayi fatan yancin na kananan hukumomi zai zarta ɓangaren kudi kadai, yana bayar da shawarar a raba su da jihohi kuma wurin karbar Barack da tara shi saboda yadda ya ce gwamnatocin jihohi ke yin yadda suka ga dama da kuɗin haraji na kananan hukumomi.

Farashin shinkafar bature ya karye a wasu kasuwannin Nijeriya

Farashin masara dai na ci gaba da cin karensa babu babbaka a sassan kasuwannin kasar Najeriya musamman a jihar Legos da ke kudancin kasar, inda a makon nan ake sai da buhunta a kan kudi N108,000, an samu karin N3000 kenan kan farashin makon da ya gabata da aka sai da N105,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos.

Sai Kasuwar Mai’adua jihar Katsina aka sai da buhun masara N98,000 a satin nan, amma satin da ya shuɗe N95,000, nan ma an samu karin N3,000 a sati guda.
To a kasuwar Gombi jihar Adamawa N95,000-98,000 kuɗin buhun yake a makon nan, yayin da a makon jiya aka sai da N90,000 -95000.
To a jihohin Kano da Kaduna N90,000 daidai ake sayar da buhun masara mai cin tiya 40 a makon nan, sai dai farashin makon jiya ya banbanta a kasuwannin da ke Arewacin Najeriya, inda aka sai buhun N87,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano, amma a kasuwar Giwa jihar Kaduna N90,000 aka sai da buhun a makon jiya ma.
To a bangaren Shinkafar Hausa kuwa, ta fi sauki a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka sayar da buhunta N140,000 cif a makon nan, haka nan aka sai da a makon jiya.
A kasuwar Karamar Hukumar Girie jihar Adamawa N160,000 ake sai da buhun a satin nan, haka batun yake a satin da ya gabata.
Sai Kasuwar Mile 12 International Market Legos ake sayar da shinkafar Hausa N155,000 a makon nan, amma a makon jiya N160,000 ne kuɗin buhun yake a kasuwar.
N150,000 cif ake sayar da buhun shinkafa ‘yar gida a kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan makon.
Hakazalika an sayi buhun Shinkafar Hausa N150,000 daidai a kasuwar Dawanau jihar Kano a satin nan, farashin dai bai sauya zani ba dana makon jiya.
To wannan makon ma Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da ake saidawa N95,000 a wannan makon, yayin da a makon jiya aka saya N90,000.
Sai dai shinkafar Bature ta fi sauki a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ke kudancin Najeriya da aka saya N78,000, amma a satin da ya kare N80,000 cif aka sai da buhun.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna an sayi buhun Shinkafar waje N88,000 a makon jiya, amma a satin nan N86,000 ake sai da buhun, an samu sauƙin N2000 kenan a sati guda.
To Mai’adua jihar Katsina an sayi buhun N85,000 a makon nan, yayin da a makon jiya aka saya N82,000.
N78,000 aka sai da buhun shinkafar waje a kasuwar Zamani jihar Adamawa a makon nan, haka aka sai da a makon da ya gabata.
Ga masu cin garau-garau ko alala koma kosai, farashin wake fari N250,0000 ne a kasuwar Mile 12 International Market Legos a makon nan, haka yake a satin da ya gabata.
N180,000 ake sai da buhun farin wake a kasuwar Giwa jihar Kaduna a satin nan, farashin dai bai sauya ba da na makon jiya.
To jihar Adamawa N170,000 daidai ake sayar da Buhunta a satin nan da ke shirin karewa, inda a makon jiya aka saya N165,000.
Ita kuwa kasuwar Dawanau jihar Kano an sayi buhun wake kan kudi N178,0000 a satin nan,sai dai N170,000 cif aka sai da Buhunta a makon daya shude.
To a kasuwar Mai’adua jihar Katsina N180,000 ake sayar da Buhunta a satin nan da ke dab da ƙarewa, bayan da a makon daya gabata aka saya N175-180,000.
Farashin taliya ma dai ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Legos da aka sai da kwalin N18,000 a satin nan, hakan kuwa aka sai da a satin da ya gabata.
A jihohin Adamawa da Kaduna N17,500 ake sayar da kwalin taliya,sai dai a makon jiya N16,000 cif ake sayar da kwalinta a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, yayin da a kasuwar Giwa jihar Kaduna aka saya N15,000 daidai.
To a jihar Katsina kwalin taliyar ya kara N500 a satin nan da aka sai da N16,000, inda a makon jiya kuwa aka saya N15,500.
To sai dai farashin kwalin taliyar ya ki sauki a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano da ake saidawa N14,000 a satin nan,yayin da a makon jiya aka saya N16,000 cif,an samu sauƙin N2000 kenan a wannan makon.
DCL Hausa A’isha Usman Gebi.

Kotu ta tura tsohon ministan Buhari gidan Yãri

Wata babbar kotu a Abuja ta tura tsohon ministan wutar lantarki Sale Mamman gidan Yãri da ke Kuje kafin a duba yiyuwar bada belin shi, kan zargin da ake masa na almundahana da kuɗin ƙasa, zargin da shi kuma ya musanta.

Hukumar EFCC ta yi ƙarar tsohon ministan tana buƙatar kotu ta bincike shi kan salwantar wasu kuɗaɗen da suka kai sama da Naira biliyan 30.

Lauyan tsohon ministan Femi Ate ya fadawa alkali James Omotosho cewa ya nemi belin wanda ya ke karewa, saidai alkalin ya ce a lokacin wannan zama na sauraron ƙarar bai kai ga samun wannan bukata ba.

Za mu karya farashin kayan abinci a watan Junairu – Gwamnatin Tinubu

Ministan harkokin noma na Najeriya Abubakar Kyari yana albashir ga ‘yan Najeriya kan batun karya farashin kayan abinci da gwamnatin shugaba Tinubu ta daura ɗamarar yi a watan Junairu da ke tafe.

Ministan ya ce matakin cire haraji kan wasu kayayyakin abinci ga gwamnatin shugaba Tinubu ta amince wa yan kasuwa shigo da su Najeriya da kuma ƙoƙarin gwamnati na shigo da tan dubu 500 na Alkama da Masara su ne manyan dalilan gwamnati na karya farashin a watan ɗaya na shekara mai zuwa, kuma ya ce gwamnati zata ƙaiyade farashi da za’a riƙa sayar da kayan na abinci.

Kyari ya ce sun samu kwarin gwiwar yin hakanne bayan shawara da ƙungiyar manoman Najeriya ta basu cewa yin hakan ne kadai zai sa a samu saukin rayuwa, saboda a cewar ƙungiyar manoman ta AFAN abinci da ake nomawa ba zai isa ba.

Wannan mataki na gwamnatin tarayya na zuwa shekara guda bayan cire tallafin man fetur, abin da wasu ke ganin kamar ya zo a makare, sannan ina ma ace a wannan lokaci na damuna za’a aiwatar ba wai har nan da kwanaki 180 ba.

Gwamnatin Tinubu ta yi nasara kan gwamnoni a kotun ƙoli

Kotun ƙoli a Najeriya ta kawo ƙarshen alakar gwamnonin ƙasar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

A wani zama na yanke hukunci ta kotun ta yi Alhamisɗinnan ƙarkashin jãgorancin mai Shari’a Emmanuel Agim ta ce daga yanzu kowace ƙaramar hukuma a ƙananan hukumomin Nigeria 774 ce kadai ke da hurumin sarrafa kuɗaɗen ta.

Kotun ƙolin ta Najeriya ta ce dama dai tsarin mulkin ƙasar matakai uku na gwamnati ya sani wato gwamnatin taraiya, gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi kuma daga yanzu gwamnoni bazasu sake nada kantomomi  ƙananan hukumomi ba saboda a cewar kotun gwamnoni suna nada wadan da zasu iya cire su ne kaɗai.

Gwamnonin na Najeriya dai dama sun kulibalanci hurumin kotun na yin Shari’a kan wannan batu, amma a hukuncin da ta yanke kotun ta ce ministan shari’a yana da hurumin shigar da ƙara a gaban ta dan kare kundin tsarin mulkin ƙasar.

Kwastam ta yi gwanjon litar man fetur 55,164 a Sokoto

Hukumar Kwastam mai kula da shiyyar Sokoto da Zamfara, a ranar Laraba, ta yi gwanjon litar man fetur 55,164 da ta kama daga hannun masu fasa-kwauri a Sakkwato.

Yayin da yake kaddamar da shirin Kwanturolan hukumar Kamal Muhammed, ya ce an gudanar da gwanjon ne bisa umarnin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale.

Ya kuma danganta matsalar karancin man fetur da ake fama dashi a fadin kasar nan da safarar shi da wasu suke, inda ya ce hukumar za ta dakile hakan domin inganta tattalin arzikin Najeriya.

Jihar Kaduna ta kammala jigilar kwaso Alhazanta daga kasa mai tsarki

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta ce ta kammala jigilar dawowa da alhazanta sama da 4000 daga kasar Saudiyya zuwa Nijeriya.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Mohammed Abdullahi, ya ce jirgin karshe na dauke da mutane 56 a jirgin Max Air, wanda galibin su jami’an hukumar ne.

Kakakin ya kara da cewa jihar Kaduna ce ta fi yawan alhazai wanda yakai 4,767, duk kuwa da asarar rayuka da aka yi a kasa mai tsarki.

Sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar Malam Salihu .S. Abubakar ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa jajircewarsa kan 

Gawar tsohon shugaban majalisar dattawa ta iso Nijeriya bayan shekaru uku da rasuwarsa.

Gawar tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Joseph Wayas, ta iso Nijeriya bayan kimanin shafe shekaru uku da rasuwarsa a turai.

Joseph Wayas, wanda ya kasance Shugaban Majalisar Dattawa tsakanin 1 ga Oktoba, 1979 zuwa 31 ga Disamba, 1983, ya rasu a wani asibiti a Landan a ranar 30 ga Nuwamba, 2021, yana da shekaru 80 bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Matarsa ​​ta farko ta rasu bayan kwanaki 12, da rasuwarsa, an cigaba da ajiye gawar dan siyasar a dakin ajiye gawa har zuwa wannan lokaci.

Ganduje, matarsa, wasu mutane shida za su gurfana a gaban kotu ranar Alhamis

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da mai dakinsa, da wasu mutane shida na shirin gurfana a gaban wata babbar kotu a jihar Kano ranar Alhamis mai zuwa.

Suna fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi cin hanci da rashawa da karkatar da ƙuden kudade da suka kai biliyoyin Naira.

Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da karar a gaban mai shari’a Amina Adamu Aliyu.