DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 423

Tinubu ya rufe ƙofa hatta ministocinsa ba su iya samun damar ganinsa – Ali Ndume

Dan majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana damuwarsa kan tsadar rayuwa da karancin abinci da kasarnan ke fuskanta.

Hakan na a cikin wata hira da BBC Hausa tayi da Sanata Ndume, ya ce gazawar gwamnatin tarayya na magance wadannan matsaloli babban kalubale ne, inda ya kara da cewa wasu ministoci sun kasa ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu domin tattaunawa kan lamarin.

Sanatan ya kara da cewa hukumar samar da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar ‘yan Najeriya miliyan 82 za su fuskanci karancin abinci nan da shekaru biyar masu zuwa.

Ndume ya yi magana ne jim kadan bayan da abokin aikinsa Sanata Sunday Steve Karimi, ya gabatar da kudirin neman magance matsalar karancin abinci a kasar.

Sanatan ya ce makasudin gabatar da kudirin shi ne jawo hankalin gwamnati kan tsananin karancin abinci da ke addabar ‘yan Najeriya da dama.

Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar abinci

Majalisar dattawan Nijeriya ta tabka zazzafar muhawara a ranar Talata, inda tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta magance matsalar yunwa da ake fama da ita a kasar.

Majalisar ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki matakan yaki da matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar ta hanyar zayyana wasu matakan yaki da lamarin.

Majalisar dattijai ta yi nuni da cewa, a cikin ‘yan watannin da suka gabata an samu hauhawar farashin kayan masarufi a kasar nan, lamarin da ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

Filayen jiragen sama uku ne daga cikin 22 ke samun riba a Nijeriya – FAAN

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya FAAN, ta ce filayen tashi uku ne kawai daga cikin filayen jiragen sama 22 da Nijeriya ke samun riba.

Manajan Daraktan FAAN, Olubunmi Kuku ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.

Ta yi nuni da cewa, ana bayar da tallafin filayen jiragen sama 19 ne saboda ba sa samun zirga-zirgar fasinja daidai da kudin da ake kashewa.

A cewarta, akasarin filayen tashi da saukar jiragen sama 22 da FAAN ke kula da su na bukatar a inganta muhimman ababen more rayuwa a cikin su.

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tinubu tayi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tinubu tayi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA

Bayan wani kudiri na gaggawa wanda mambobin majalisar wakilai 88, suka suka gabatar, majalisar wakilan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar ta Samoa har sai an gama bincike.

Da yake gabatar da kudirin a ranar Talatar nan, dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Dala a kano, Aliyu Madaki, ya ja hankali kan batun da ke nuna “daidaitan jinsi” tare da duk wasu batutuwa dake dake haifar da cece kuce.

Majalisar ta kuma umarci kwamitocin dake da alaka da yarjejeniya ta kasa da kasa da su binciki kudurorin yarjejeniyar da ke cike da ake ta cece-kuce akai.

Takaddama dai ta kunno kai kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta rattaba hannu da kungiyar Tarayyar Turai, inda da dama suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin Nijeriya ta amince da yarjejeniyar.

Yarjejeniyar ta Samoa ta haifar da cece-kuce a yanar gizo tare da wasu da dama da ke adawa da yancin LGBT, wanda ya sabawa dokar hana auren jinsi da ma’auratan da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa a shekarar 2014.

Shugaban Laberiya ya rage albashinsa da kashi 40

Shugaban Laberiya ya rage albashinsa da kashi 40%

Shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai ya bayyana cewa zai rage albashin da yake karba da kashi 40 cikin dari.

A kwanakin baya ne dai al’ummar kasar Laberiya suka koka bisa tsadar rayuwa da ‘yan kasar ke fama dashi wanda hakan yasa ake bincike kan albashin manyan ma’aikata dake kasar.

Kusan mutane biyar suna iya rayuwa a kasa da $2 (£1.70) a rana a cikin kasar dake yammacin Afirka.

Mista Boakai ya bayyana a watan Fabrairu cewa albashinsa na shekara yakai $13,400 ne,kuma zai rage shi zuwa $ 8,000.

Matakin na Boakai ya yi daidai da na magabacinsa, George Weah, wanda ya rage kashi 25 cikin 100 na albashinsa,wanda

wasu daga cikin al’ummar yammacin Afirka sun yaba da matakin na Mista Boakai, amma wasu na tunanin ko sadaukarwa ce da ganin cewa shi ma yana samun wasu abubuwa kamar alawus-alawus na yau da kullum.

Jami’ar FUDMA ta zargi wani ma’aikacinta da kwarmata wa ‘yan bindiga bayanan sirrin jami’ar

Jami’ar FUDMA ta zargi wani ma’aikacinta da kwarmata wa ‘yan bindiga bayanan sirrin jami’ar

Shugaban jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) ta Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Bichi, ya yi zargin cewa wasu ma’aikatan jami’ar suna bai wa barayin daji bayanai ne.

Bichi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina a ranar Talata, ya ce ma’aikatan da ake zargin an baiwa wata hukumar tsaro domin ci gaba da bincike akai.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar da ake zargin sun kai hari a yankin, inda suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikatan jami’ar da kuma ‘yan uwansu.

Wani harin da aka kai kwanan nan wanda ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin ma’aikatan jami’ar ya sa abokan aikinsa gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin tsaro da yake karuwa.

A cewar shugaban jami’ar, hukumar gudanarwar makarantar na yin duk mai yiwuwa don hana afkuwar irin wannan lamari amma lamarin sai kara ta’azzara yake yi.

Bichi ya ce, Wannan batu na masu ba da bayanai ga ‘yan bindiga abin damuwa ne, don haka, mun binciki wadanda muke zargi da bayar da bayanan abokan aikinsu da daliban.

Mun same su kuma mun mika ga daya daga cikin jami’an tsaro domin ci gaba da bincike akai

Firgici ya kunno kai a Rano da ke Kano bayan da wasu masu kama da ‘yan daba suka mamaye fadar masarauta

Firgici ya kunno kai a Rano da ke Kano bayan da wasu masu kama da ‘yan daba suka mamaye fadar masarauta

A cikin wata wasika da aka rubuta wa kwamishinan ‘yan sandan jihar, jaridar SolaceBase ta rawaito cewa ‘yan dabar sun yi sansani a fadar Sarkin Rano tun a ranar Lahadi da wasu da ba a tantance ko suwaye ba.

Ta ce har yanzu ba a san dalilan wadannan mutane masu dauke makamai ba, ana daukar zaman nasu a matsayin barazana ga tsaron rayuka da dukiyoyi al’ummar yankin.

A cewar wasikar, mazauna masarautar Rano mutane ne masu zaman lafiya da kullum suna gudanar da harkokinsu ba tare da haifar da tarzoma ba.

Ta ce a tsawon shekaru masarautar Rano ta samu zaman lafiya ba tare da wata matsala ba kuma hukumomin tsaro na iya shaida wannan tarihin da masarautar ke da shi.

An saka lokacin sake kidayar yawan al’ummar Nijeriya

An saka lokacin sake kidayar yawan al’ummar Nijeriya

Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta ce zatayi kidayar ‘yan kasar a watan Nuwamba, 2024, don kidayar yawan al’umma da gidaje a Nijeriya.

Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai na bikin ranar yawan jama’a ta duniya na shekarar 2024, shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra, ya ce shawarar hakan ta kasance bisa amincewar shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kwarra, wanda ya bayyana cewa hukumar ta shirya kashi 70 cikin 100 na gudanar da kidayar, ya ce jinkirin da Nijeriya ke samu na samun bayanan al’ummarta ba zai hana kasar samun nasarar kidayar yawan jama’a da gidajen dake kasar ba.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekaru 100 a duniya

Ya dai kwashe shekaru 76 yana gabatar da tafsirin Alqur’ani mai tsarki. Yana da ‘ya’ya 100, jikoki 406 da tattaba-kunne 100 kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Daga cikin ‘ya’yansa 100, 78 sun haddace Alqur’ani, jikokinsa sama da 199 su ma sun haddace Alqur’ani. 
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gudanar da aikin hajji sau 55, Umrah 205.

Kura ta kufce daga hannun jami’an gwamnati a Jos

 

Hukumar kula da yawan shakatawa ta jihar Filato da ke Nijeriya ta sanar da kufcewar wata kura daga gandun daji mallakin jihar da ke a Jos. 

A sanarwar da hukumar ta fitar ta ce ta baza jami’anta domin nemo dabbar a sassan jihar, inda ta ce za ta yi amfani da jirgi mai sarrafa kansa a kokarin gano kurar.

Hukumar ta shawarci mutane da ka da su yi wa kurar komai, a duk inda suka ganta su sanar da jami’anta ta lambar waya 09026927620 ko kuma 09131000945