Hisbah ta haramta caca da harkar mata masu zaman kansu a fadin jihar Katsina
Jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Katsina na nuna wa juna yatsa
![]() |
| Sanata Lado da Dr Mustapha |
Kotu ta umarci Sadiya Farouk ta faɗi yadda aka kashe naira biliyan 729 don raba wa talakawan Najeriya tallafi a 2021
Kotu ta umarci Sadiya Farouk ta faɗi yadda aka kashe naira biliyan 729 don raba wa talakawan Najeriya tallafi a 2021
Babbar kotun tarayyar da ke Legas ta umarci tsohuwar minsitar jinƙai, Sadiya Umar Farouk, da ta yi bayanin yadda aka kashe naira biliyan 729 na tallafin da aka raba wa talakawan ƙasar na tsawon wata shida.
Cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Deinde Isaac Dipeolu ya kuma umarci tsohuwar ministar ta wallafa sunaye da bayanan mutanen da suka amfana da tallafin da jihohin da aka raba, da yawan kuɗin da aka raba akowace jiha.
Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da rashawa ce ta gurfanar da Sadiya Farouk a gaban kotun, inda ta buƙaci kotun ta tilasta mata bayar da bayanan, kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta ‘yancin samun bayanan.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ɗin ta ce ta samu kwafin hukuncin da kotun da yi ranar Juma’a.
Alƙalin kotun ya ce kotu ta tilasta wa tsohuwar ministar bayar da bayanan, kasancewa kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadin bayar da bayanai ga kowane ɗan ƙasa ciki har da SERAP.
Don haka kotu ta umarci tsohuwar ministar ta yi bayanin yadda ta kashe naira biliyan 729 wajen raba wa talakawan Nijeriya miliyan 24.3 a shekarar 2021, kamar yadda hukuncin ya nuna.
Mai shari’a Dipeolu, ya kuma ce dole ne tsohuwar ministar ta yi wa SERAP cikakkun bayanan hanyoyin da aka bi wajen zaɓo mutanen da suka amfana da tallafin.
An bude taron ECOWAS karo na 65 a Abuja
An bude taron ECOWAS karo na 65 a Abuja
Gabanin cikar wa’adin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban hukumar ta ECOWAS a ranar 9 ga watan Yulin 2024, a halin yanzu shugabanni da wakilan kasashe mambobin kungiyar suna taro a cibiyar taro na fadar gwamnati dake Abuja. .
An ce taron shi ne babban taron shugabannin kasashen yankin karo na 65,taron na iya sanar da sabon shugaban kungiyar shiyyar Afirka ta yamma da zai jagoranci al’amuransu na tsawon shekara guda.
Sai dai babu wani abin da ya tabbata sai an kammala taron da aka fara da a yau.
Zaman shugaba Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS ya kasance da juyin mulkin da aka yi a wasu kasashe mambobin kungiyar, inda har yanzu ake kokarin dawo da Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso cikin kungiyar kasashen yankin.
Duk kokarin da kungiyar ECOWAS ta yi na dawo da kasashen ya ci tura inda shugaban hukumar Omar Touray ya nuna rashin jin dadinsa a kwanan baya kan kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar na kin komawa cikin kungiyar kasashen yankin.
APC ce ke juya akalar PDP a Nijeriya – Mustapha Inuwa
![]() |
| Nyesom Wike da Mustapha Inuwa |
Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar, Mustapha Muhammad Inuwa, ya zargi jam’iyyar APC da juya akalar jam’iyyar PDP ta hannun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Inuwa ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar, wanda ya gudana Katsina a karshen mako.
Tsohon sakataren gwamnatin wanda ya yi takarar Gwamna a jam’iyyar APC kafin zaben fitar da gwani, ya kuma zargi wasu ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP a jihar da yi mata zagon-kasa.
Yace “Ba su bukatar jam’iyyar ta yi nasara a dukkanin zabuka, su dai burinsu kawai a ce suna takara, idan za a je taron jam’iyya a Abuja su amso kudin ‘daliget’, haka kuma idan za a yi zabe sai su amso kudin zabe, idan za a je kotu, sai su amso kudin su sa aljihu”.
Mustapha Inuwa ya kara da cewa rikicin da jam’iyyar PDP ke ciki a jihar Katsina ƙirƙira shi aka yi, domin wasu dalilai.
An kara wa masu sana’ar POS wa’adin kwanaki 60 da su yi rijista da CAC
An kara wa masu sana’ar POS wa’adin kwanaki 60 da su yi rijista da CAC
Hukumar Kula da Kamfanoni da kungiyoyi (CAC) ta kara wa’adin yin rajistar duk masu gudanar da tallace-tallace da karin kwanaki sittin domin daukar wasu da ba su samu damar yin rijistar ba saboda wasu matsaloli na fasaha.
Daily Trust ta ruwaito cewa tun farko hukumar ta bada wa’adin ranar 7 ga watan Yulin 2024 a matsayin ranar da za ta rufe rijistar
A cikin wani sakon da hukumar ta fitar a shafin ta na X, ya bayyana cewa an kara wa’adin da kwanaki sittin wato watanni biyu kenan.
Hukumar Kula da Kamfanoni ta sanar da masu sana’ar (POS) cewa an tsawaita wa’adin farko na 7 ga Yuli, 2024 da aka bayar don yin rajistar na tsawon kwanaki sittin. daga 7 ga Yuli, 2024 zuwa 5 ga Satumba 2024.
Wannan shi ne don ba da isasshen lokaci ga Ma’aikata musamman waɗanda ke cikin lungunan da za su iya fuskantar ƙalubalen hanyar sadarwa don haka su yi rajista kuma su ci gaba da kasuwancinsu.
Ku mai dawa ma’aikata kudaden goran sallah da muka basu wanda ku ka karkatar- gwamnan Sokoto
Ku mai dawa ma’aikata kudaden goran sallah da muka basu wanda ku ka karkatar- gwamnan Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya umurci jami’an hukumar ilimi na kananan hukumomi da da su mayar wa ma’aikatan jihar da aka karkatar kudin alawus din su na sallah Naira 30,000 ko kuma su fuskanci hukunci.
Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da magoya bayansa a gidan gwamnati, da ke sokoto.
Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu jami’an kudi musamman a matakin kananan hukumomi suka hana ma’aikatan su naira 30,000 da gwamnatin jihar ta amince da aba su a matsayin kyautar Sallah.
Yace wadanda suka karkatar da wadannan kudade dole ne su dawo da su cikin gaggawa idan ba haka ba za mu dauki tsauraran matakan ladabtarwa a kansu.
Za mu tabbatar da cewa masu laifin sun girbi abin da suka shuka domin ya zama izina ga wasu.
Gwamnan ya tuhumi dukkan shugabannin hukumomin da ake tafka ta’asa da cin hanci da rashawa da su gaggauta tattara duk ma’aikatan da abin ya shafa tare da tabbatar da an mayar wa da mutanen kudadensu.
Wani Asibiti a jihar Legas ya bayyana cewa suna amsar haihuwar sabbin jarirai 2,500 a kowane wata
Wani Asibiti a jihar Legas ya bayyana cewa suna amsar haihuwar sabbin jarirai 2,500 a kowane wata
Babban daraktan asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas (LASUTH), Farfesa Adetokunbo Fabamwo, ya ce sashin kula da masu juna biyu na asibitin suna ansar haihuwar sabbin Jarirai 2,500 a wata.
Fabamwo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya, NAN a Legas.
Yace gidan Ayinke gidane da ake kula da lafiyar mata masu juna biyu da ke cikin harabar asibitin kuma ana yimai lakabi da babban asibitin haihuwa a Nijeriya bayan da aka gyara shi daga maicin gadaje 80 zuwa gadaje 170 da aka samar da na’urorin kiwon lafiya na zamani.
Yace a bangaren ana baiwa mata masu juna biyu ilimin kiwon lafiya a lokacin da ake kula da masu juna biyu sannan kuma ana basu shawarwari kan tsarin iyali da kuma tazarar haihuwa bayan haihuwa a asibitin.
Kasar Uruguay ta lallasa Brazil a bugun Fanareti na a gasar cin kofin Nahiyar Amurka
Kasar Uruguay ta lallasa Brazil a bugun Fanareti na a gasar cin kofin Nahiyar Amurka
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu da ‘yan uwansu a jihar Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan jarida biyu da ‘yan uwansu a jihar Kaduna
‘Yan bindigar sun kai farmaki kauyen Danhonu da ke garin Millennium a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kai farmaki gidajen ‘yan jaridar The Nation, Alhaji AbdulGafar Alabelewe da na jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu da matansu da ‘ya’yansu.
Wani dangin daya daga cikin wadanda abin ya shafa Taofeeq Olayemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba kafin su aiwatar da aikin na su.
Ya ce sun yi garkuwa da Alhaji Alabelewe da matarsa da ’ya’yansa biyu, yayin da aka yi garkuwa da Alhaji Aodu da matarsa, inda suka bar ‘yarsu da ba ta da lafiya.
Kafin shigarsu gida jen sun farfasa musu kofofinsu da tagoginsu tare da cire duk wani abu da zai hana su shiga gida jen.









