Sama da gidaje dubu 9,733 suka zube sakamakon guguwar iska a Adamawa – NEMA
Sabon Fira Ministan Birtaniya Starmer ya yi taron majalisar ministoci na farko
Sabon Fira Ministan Birtaniya Starmer ya yi taron majalisar ministoci na farko
Fira Minista Keir Starmer ya gudanar da taron majalisar ministocinsa na farko bayan samun nasara da yayi a zaben da ya tabbatar dashi a matsayin sabon Fira Ministan Birtaniya
Starmer ya yi maraba da sabbin ministocin, yana mai cewa muna da ayyuka da yawa da za mu yi, don haka yanzu zamu ci gaba da aikinmu.
Daga cikin matsalolin da suke fuskanta sun hada da bunkasa tattalin arzikin kasa mai durkushewa, gyara tsarin kiwon lafiya.
Wani farfesa, a fannin siyasa a Jami’ar Queen Mary ta Landan Tim Bale, ya ce saboda jam’iyyar Labour ta samu gagarumin rinjaye ba ya nufin cewa duk matsalolin da gwamnatin Conservative ta fuskanta sun tafi.
Nijar, Mali da Burkina Faso ba za su koma kungiyar ECOWAS ba – Janar Tiani na Nijar
Nijar, Mali da Burkina Faso ba za su koma kungiyar ECOWAS ba – Janar Tiani na Nijar
Shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya bayyana cewa, al’ummar kasarsa, tare da makwabciyarta Mali da Burkina Faso, sun juya wa kungiyar ECOWAS baya.
Ya bayyana hakan ne a yayin bude taro dake gudana a birnin Yamai tsakanin kasashen yankin Sahel uku da suka fice daga babbar kungiyar a farkon wannan shekarar.
Shugaban hukumar ta ECOWAS, Dr Omar Alieu Touray, a ranar Alhamis din da ta gabata, ya koka da cewa, duk da kokarin da kungiyar kasashen yankin ke yi na dawo da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, amma kasashen uku ba su nuna wata alamar dawowa ba.
A yayin da yake jawabi a wajen bude taro karo na 92 na majalisar ministocin kungiyar a Abuja, ya ce har yanzu kungiyar ECOWAS ba ta kafa tsarin tattaunawa da mahukuntan kasashen Sahel din uku kan matakin da suka dauka na janye mambobinsu daga kungiyar ba.
A ranar 28 ga watan Junairun da ya gabata ne dai mahukuntan kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar suka sanar da ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.
KEDCO ta mayar da lantarkin jami’ar Aliko Dangote bayan biyan wani kaso na tarin bashin da ake bin jami’ar
KEDCO ta mayar da lantarkin jami’ar Aliko Dangote bayan biyan wani kaso na tarin bashin da ake bin jami’ar
Kamfanin Rarraba wutar lantarki ta Kano, KEDCO, ya maida wutar lantarki a jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, bayan biyan Naira miliyan 100.
Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Musa Yakasai, ya tabbatar da maido da wutar lantarki ga kamfanin dillancin labaran Nijeriya a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Juma’a.
Ya ce an dawo da wutar lantarki a cibiyar da misalin karfe 4 na yamma bayan an biya kusan Naira miliyan 100.
An katse wutar jami’ar ne sakamakon bashin Naira miliyan 248 da kamfanin na KEDCO ke bin jami’ar.
Kamfanin ya dauki matakin ne duk da biyan Naira miliyan 20 daga cikin Naira miliyan 60 da jami’ar ta jihar ke biyan duk wata.
Mista Yakasai ya alakanta hakan ne da tsoma bakin gwamnatin jihar Kano da gidauniyar Dangote, inda suka fara biyan Naira miliyan 100 ga KEDCO.
Gwamnatin jihar ta kuduri aniyar daidaita wasu basussuka, yayin da gidauniyar Dangote ta binciko mafita mai dorewa kamar kananan grid masu amfani da hasken rana.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta nuna godiya ga duk wanda aka samu da hannu tare da bukaci jami’ar
Sarkin musulmi ya bayyana ranar Lahadi a matsayin ranar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan hijira
Sarkin musulmi ya bayyana ranar Lahadi a matsayin ranar sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 bayan hijira
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Lahadi 7 ga Yuli, 2024, a matsayin ranar farko ga watan Muharram, a daidai lokacin da aka shiga shekarar Musulunci ta 1446 bayan Hijira.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar Sarkin Musulmi, Sambo Junaidu, a ranar ya fitar a ranar juma’a.
Ya bayyana cewa babu wani rahoton ganin watan da kwamitocin ganin wata na kasa da suka samu a fadin kasar.
Sanarwar ta ce, Kwamitocin ganin wata na kasa daban-daban a fadin kasar nan ba su samu rahoton ganin jinjirin watan Al-Muharram ba a ranar juma’a wato 29 ga watan Zulhijja shekara ta 1445 bayan hijira. Asabar 6 ga Yuli, ita ce 30 ga Zulhijja.
Sarkin Musulmi ya taya musulman Nijeriya murnar shiga sabuwar shekara,ya bukace su da su ci gaba da yi wa Nijeriya addu’o’in zaman lafiya da ci gaba.
‘Yan Nijeriya miliyan 82 na iya fuskantar yunwa nan ba da jimawa ba, in ji MDD
‘Yan Nijeriya miliyan 82 na iya fuskantar yunwa nan ba da jimawa ba, in ji MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa ‘yan Nijeriya miliyan 82, kusan kashi 64 cikin 100 na al’ummar kasar za su iya fama da yunwa nan da shekara ta 2030, inda ta yi kira ga gwamnati da ta magance matsalolin da kasar ke fuskanta.
Hasashen ya zo ne sakamakon hauhawar farashin kayan abinci da ake ci gaba da yi a kasar.
A cewar hukumar kididdiga ta kasa, hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya ya kai sama da kashi 40.66 cikin 100 a watan Mayun 2024, wanda ya zarce na watan da ya gabata.
A shekarar 2023, hukumar abinci da aikin noma ta yi hasashen cewa akalla ‘yan Nijeriya miliyan 2.6 a jihohin Borno, Sokoto da Zamfara, da kuma Abuja na iya fuskantar matsalar abinci tsakanin watan Yuni zuwa Agusta 2024.
Ya kamata masu zuba jari a Nijeriya su fadada tunanin su- Kashim Shettima
Kotu ta saka ranar da Ganduje zai san makomarsa a shugabancin APC
Rundunar sojojin Nijar ta hallaka ‘yan ta’adda sama da 100 a sabon farmaki
Makonni uku a jere buhun Masara ya gaza sakkowa daga naira 100,000
Buhun masara ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market jihar Legos da ke kudancin Najeriya, ana sayar da buhunta kan kuɗi N105,000, inda a makon da ya shude aka saya N100,000.







