Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 43

Jam’iyyar APC ta ce ba za ta bai wa Gwamnonin da suka shiga jam’iyyar tikitin takara kai tsaye ba

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta bai wa gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa cikinta tikitin takarar kai tsaye ba a zabe mai zuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnonin da ka iya rasa wannan dama dai akwai na Akwa Ibom, Umo Eno, Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, da kuma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wanda ake sa ran zai shiga a nan gaba.

Wani mamba na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa sauya sheƙa daga wata jam’iyya zuwa APC ba ya nufin samun tikiti kai tsaye.

Kazalika, daraktan yaɗa
Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya tabbatar wa da jaridar ta Punch cewa jam’iyyar ta dimokuraɗiyya ce, kuma kowa zai bi tsarin yadda ake yin takara bisa ka’ida.

SERAP ta maka Ministan Abuja Nyeson Wike da Gwamnoni a kotu

0

Ƙungiyar da ke fafutikar kare hakkin bil’adama a Nijeriya SERAP ta shigar da ƙara a gaban kotu kan gwamnonin jihohi da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, bisa zargin gaza yin bayani  kan biliyoyin naira da aka kashe a matsayin kuɗaɗen tsaro (security votes) tun daga 29 ga Mayu, 2023.

A cewar SERAP, an shigar da ƙarar ne sakamakon ci gaba da tabarbarewar tsaro a jihohi da dama da kuma birnin taraiyar Nijeriya Abuja, duk da manyan kuɗaɗen jama’a da ake warewa duk shekara don tsaro.

Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da ta bayyana shigar da ƙarar, wacce Mataimakin Daraktan SERAP Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu kuma aka miƙa wa PUNCH Online a ranar Lahadi.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/95/2026, wacce aka shigar a Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata, SERAP na roƙon kotu ta tilasta wa gwamnonin jihohi da Ministan Abuja su bayyana a bainar jama’a yadda aka kashe kuɗaɗen tsaro da suka karɓa tun daga 29 ga Mayu, 2023.

Ƙungiyar ta kuma nemi kotu da ta bayar da umarni da zai sa su gabatar da cikakkun rahotanni kan yadda aka ware, aka yi amfani, matakin aiwatarwa da kammala ayyuka da aka ɗauki nauyinsu da kuɗaɗen tsaro, tare da shirye-shiryen inganta kayayyakin tsaro a jihohinsu da kuma Abuja.

A cewar SERAP, sama da Naira biliyan 400 ake kasafawa duk shekara a matsayin kuɗaɗen tsaro a faɗin Najeriya, yayin da rahotanni ke nuna cewa akalla gwamnonin jihohi 10 sun ware kusan Naira biliyan 140 don wannan manufa a kasafin kuɗin shekarar 2026.

A cikin ƙarar, SERAP ta jaddada cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake amfani da kuɗaɗen jama’a da aka tanada domin kare rayuka da dukiyoyi, musamman a wannan lokaci da matsalar tsaro ke ƙara kamari.

Atiku ba zai iya kalubantar Tinubu ba, Kwankwaso da Peter Obi ne za su iya – Obasanjo

0

Obasanjo ya goyi bayan takarar shugabancin Nijeriya na Kwankwaso da Peter Obi a 2027 tare da cewa Atiku ba zai iya kalubantar Tinubu ba.

Wani babban jami’i a jam’iyyar ADC ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo shi ne ya fara tunanin hadin gwiwar siyasa tsakanin Mista Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa.

A cewar jami’in jam’iyyar, Cif Olusegun Obasanjo ba kawai ya amince da sauya sheƙar Mista Peter Obi zuwa jam’iyyar ADC ba kadai, har ma ya bukace shi ya yi aiki tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin su nemi tikitin shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Tsohon Shugaba Obasanjo ya fito fili yana goyon bayan Mista Peter Obi a zaɓen 2023, inda ya yi kamfe tare da tara masa magoya baya a faɗin Nijeriya domin ƙalubalantar ɗan takarar jam’iyyar APC Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

A wata budaddiyar wasiƙa da ya rubuta a ranar 1 ga Janairu, 2023, Cif Obasanjo ya bayyana cewa ko da yake babu wani ɗan takara da ya kasance tsarkakke gaba ɗaya, amma idan aka kwatanta halayya, tarihin aiki, fahimta, ilimi, da ƙwazon aiki, Peter Obi, wanda ya kira almajirinsa, ya fi sauran ‘yan takara cancanta wajen jagorantar ƙasar a halin da take ciki.

Ba harin ‘yan bindiga ba ne — rikicin CJTF da tsoffin ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar rasa rai a kauyen jihar Katsina – ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta musanta rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tuge inda suka harbe tare da jikkata mazauna yankin.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa abin da ya faru ba harin ‘yan bindiga ba ne, illa rikici da ya barke tsakanin wasu mambobin Civilian Joint Task Force (CJTF) da kuma wasu da ake zargin tsoffin ‘yan bindiga ne ‘yan asalin kauyen Tuge Mai Zuri da ke karamar hukumar Musawa a jihar Katsina.

A cewar DSP Abubakar Sadiq Aliyu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:35 na safiyar Asabar, 17 ga Janairu, 2026, lokacin da rikici ya kaure tsakanin bangarorin biyu, har aka yi musayar wuta. Hakan ya janyo jikkatar mutane hudu sakamakon harsasan da aka harba inda daya daga cikinsu ya rasu bayan an kai shi asibiti, yayin da sauran uku ke karbar magani.

Gwamnatin Lagos ta kama ’yan daba 281 dake hantarar matafiya kan hanya

Gwamnatin Jihar Lagos ta sanar da kama ƴan daba 281 da ake kira Omotaku a kokarin da take ci gaba da yi na dawo da tsaro da daidaito a wuraren jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, inda ya ce an riga an gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu.

Sanarwar ta ce aikin, wanda ya dauki tsawon mako guda, rundunar Taskforce ta jihar ta gudanar da shi a wurare da dama, ciki har da Lekki Phase 1, Ikoyi, Lekki–Ajah Expressway, Bourdillon, Akowonjo Road, Egbeda, Fadeyi, Costain, Funsho Williams Avenue, Victoria Island, Apongbon, Jibowu, Yaba, Lagos Island, Palmgrove, Ojuelegba da Surulere, da sauran hanyoyi a bangaren tsibiri da kuma babban birnin jihar.

Ana bikin cika shekaru 100 da maida birnin Yamai a matsayin babban birnin ƙasar Nijar

Hukumomin ƙasar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Mohamed Toumba, ne suka shirya bikin tunawa da cikar Yamai shekaru 100 da zama babban birnin ƙasar.

A baya dai birnin Zinder ne ke matsayin babban birnin Nijar, kafin a shekarar 1926 lokacin mulkin mallaka, Turawa suka mayar da fadar gwamnatin ƙasar zuwa Yamai.

An gudanar da wannan biki ne a babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke birnin Yamai, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta, ciki har da ministoci da sauran manyan masu ruwa da tsaki a gwamnatin Janar Abdourahamane Tiani.

Mali ta haramta mujallar Jeune Afrique a duk fadin kasar

Gwamnatin kasar Mali ta haramta yadawa ko rarraba wa da ma siyar da mujallar Jeune Afrique a duk fadin kasar.

Hukumomin Malin sun dauki wannan mataki ne sakamakon zargin karya marar hujja da na bata sunan kasar da suka ce jaridar ta Jeune Afrique ta yi wa kasar akan matsalar man fetur

Haka zalika hukumomin Malin sun zargin da jaridar ta yi musu ba shi tushe balle makama, ta kuma nuna son rai a yayin hada rahoton da kuma nuna rashin sanin makamar aikin jarida

Hukumomin sun ce duk wanda aka samu da bujerewa umarnin to zai fuskanci hukuncin doka

Mali ta haramta mujallar Jeune Afrique a duk fadin kasar

Gwamnatin kasar Mali ta haramta yadawa ko rarraba wa da ma siyar da mujallar Jeune Afrique a duk fadin kasar.

Hukumomin Malin sun dauki wannan mataki ne sakamakon zargin karya marar hujja da na bata sunan kasar da suka ce jaridar ta Jeune Afrique ta yi wa kasar akan matsalar man fetur

Haka zalika hukumomin Malin sun zargin da jaridar ta yi musu ba shi tushe balle makama, ta kuma nuna son rai a yayin hada rahoton da kuma nuna rashin sanin makamar aikin jarida

Hukumomin sun ce duk wanda aka samu da bujerewa umarnin to zai fuskanci hukuncin doka

Yoweri Museveni ya lashe zaben shugabancin kasar Uganda karo na 7

Hukumar zaɓe ta ƙasar Uganda ta sanar da cewa Shugaban ƙasa Yoweri Museveni ya sake lashe zaɓe, inda aka sake zaɓarsa zuwa wa’adi na bakwai.

Museveni, mai shekaru 81, ya samu kashi 71.65 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, a cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Asabar.

Ya doke babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine, ɗan shekaru 43 — wanda sunansa na gaskiya Robert Kyagulanyi — wanda ya samu kashi 24.72 cikin 100 na ƙuri’un, kamar yadda sakamakon ya nuna.

Gwamnatin Kano ta musanta rahoton dakatar da harkokin mulki

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke ikirarin cewa wani umarni daga Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dakatar da harkokin gudanar da mulki a jihar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Musa Tanko Muhammad, ya fitar, gwamnatin ta ce umarnin da aka bayar na wucin gadi ne kuma na kariya, wanda aka dauka bisa ka’idojin kudi da bin doka.

Sanarwar ta bayyana cewa umarnin, wanda ya dakatar da mikawa gwamna wasu fayil-fayil na wani dan lokaci, an bayar da shi ne a karshen watan Disamba, lokacin da kasafin kudin 2024 ya kare, yayin da kuma kudirin kasafin kudin 2025 ke gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Gwamnatin ta jaddada cewa matakin bai shafi gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati ba, tare da tabbatar wa al’umma cewa harkokin mulki a jihar na ci gaba da tafiya yadda ya kamata.