Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 44

Yoweri Museveni ya lashe zaben shugabancin kasar Uganda karo na 7

Hukumar zaɓe ta ƙasar Uganda ta sanar da cewa Shugaban ƙasa Yoweri Museveni ya sake lashe zaɓe, inda aka sake zaɓarsa zuwa wa’adi na bakwai.

Museveni, mai shekaru 81, ya samu kashi 71.65 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, a cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Asabar.

Ya doke babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine, ɗan shekaru 43 — wanda sunansa na gaskiya Robert Kyagulanyi — wanda ya samu kashi 24.72 cikin 100 na ƙuri’un, kamar yadda sakamakon ya nuna.

Gwamnatin Kano ta musanta rahoton dakatar da harkokin mulki

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke ikirarin cewa wani umarni daga Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dakatar da harkokin gudanar da mulki a jihar.

A cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Musa Tanko Muhammad, ya fitar, gwamnatin ta ce umarnin da aka bayar na wucin gadi ne kuma na kariya, wanda aka dauka bisa ka’idojin kudi da bin doka.

Sanarwar ta bayyana cewa umarnin, wanda ya dakatar da mikawa gwamna wasu fayil-fayil na wani dan lokaci, an bayar da shi ne a karshen watan Disamba, lokacin da kasafin kudin 2024 ya kare, yayin da kuma kudirin kasafin kudin 2025 ke gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Gwamnatin ta jaddada cewa matakin bai shafi gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati ba, tare da tabbatar wa al’umma cewa harkokin mulki a jihar na ci gaba da tafiya yadda ya kamata.

Tarayyar Turai ta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke da haɗarin hada-hadar kuɗi

Tarayyar Turai (EU) ta sanar da cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ake kallon suna da haɗarin aikata laifukan kuɗi, a karkashin tsarin yaki da halatta kudaden haram (AML) da kuma dakile tallafawa ta’addanci (CFT).

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar Nigeria Financial Intelligence Unit (NFIU) ta fitar, inda ta ce dokar Tarayyar Turai mai lamba EU C (2025) 8460, wadda aka amince da ita a ranar 4 ga Disamba, 2025, ta yi daidai da sabbin matakan da Kungiyar FATF ta dauka a taronta na Oktoba 2025.

Sanarwar ta ce wannan mataki zai fara aiki daga ranar 29 ga Janairu, 2026, inda aka kuma cire kasashen Burkina Faso, Mali, Mozambique, Afirka ta Kudu da Tanzania daga jerin, bayan da suka cika sharuddan da FATF ta gindaya wajen gyara matsalolin da aka gano a fannin yaki da safarar kudaden haram da tallafawa ta’addanci.

‘Yan sandan Uganda sun ƙaryata kama jagoran adawa yayin da Museveni ke tunkarar sake lashe zaɓe da rinjaye

Rundunar ‘yan sandan Uganda ta musanta ikirarin da jam’iyyar adawa ta NUP ta yi cewa an kama jagoranta, Bobi Wine, a daidai lokacin da Shugaba Yoweri Museveni ke gab da sake lashe zaɓen ƙasar da rinjaye.

Jam’iyyar National Unity Platform (NUP) ta Bobi Wine ta ce a daren Juma’a wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojoji ya sauka a harabar gidansa da ke Kampala, inda suka “tilasta shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.” Sai dai kamfanin dillancin labarai Reuters ya ce bai samu damar tabbatar da wannan ikirari nan take ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ƙasar, Kituuma Rusoke, ya bayyana a wani taron manema labarai da aka watsa kai tsaye cewa Bobi Wine yana gidansa kuma yana da ‘yancin motsi.

Har lokacin rubuta wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin Bobi Wine ko wakilan jam’iyyar NUP ba.

Jihar Kebbi ta ayyana 11 da 14 ga Fabrairu a matsayin ranakun bikin Kamun Kifi na Argungu na duniya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar da cewa za a gudanar da Bikin Kamun Kifi na Duniya na Argungu daga 11 zuwa 14 ga Fabrairu na wannan shekara.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Martaba Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera ya bayyana wa ’yan jarida, bayan wani taro da aka yi da Kwamitin Tsare-tsaren Bikin na Jiha da Kwamitin Shirya Biki na Masarautar Argungu, a Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi ranar Juma’a, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Sarkin Argungu ya bayyana cewa bikin kamun kifin ya samo asali ne a matsayin matakin samar da zaman lafiya tsakanin ’yan jihadin Daular Usmaniyya ta Sakkwato da Masarautar Kanta, kafin daga bisani ya zama wani babban bikin al’adu.

Ya ƙara da cewa, saboda muhimmancin tarihin bikin, UNESCO ta amince da shi a matsayin bikin al’adu na kasa da kasa, sannan bayan Yaƙin Basasar Nijeriya, an yi amfani da bikin wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.

Yadda muke shiga haɗari wajen tsallakawa Jamhuriyar Nijar saboda barazanar Turji — Mazauna Sokoto

Wasu ‘yan gudun hijira daga Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sokoto sun koka kan ƙaruwa hare-haren ‘yan bindiga a yankin, inda suka ce ‘yan uwansu na shiga mummunan haɗari wajen tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar domin tsira da rayukansu.

Sun shaida wa Saturday PUNCH cewa ‘yan uwansu sun tsere zuwa ƙasar makwabciya ne bayan sabbin barazana da hare-hare daga ‘yan bindigar da ke biyayya ga shahararren shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji. Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta a makon nan ya nuna jama’a na guduwa daga wasu ƙauyuka, lamarin da hukumomi suka tabbatar.

Sakataren Kungiyar Raya Yankin Gabashin Sokoto, Farfesa Mu’azu Shamaki, ya ce fara wannan kaura ya biyo bayan barazanar da Turji ya yi wa wasu ƙauyuka da ke kewaye da Tidibali, wani gari a cikin ƙaramar hukumar.

Ya ce tun daga ranar Juma’ar da ta gabata, jama’a da dama ke tururuwa zuwa hedikwatar ƙaramar hukumar domin kai ƙorafi, inda ya ƙara da cewa fiye da kauyuka 20 suka riga suka yi hijira saboda tsoron hare-haren.

A hirarraki daban-daban, tsoffin mazauna yankin sun ce iyalai da ‘yan uwansu na tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar. Wani daga cikinsu, Mohammed Saleh, wanda ke Dole Kaina — wani yankin kan iyaka tsakanin Nijeriya da Nijar a Sabon Birni — ya ce mutane da dama na ɗaukar haɗarin tsallaka iyaka domin neman mafaka da tsaro.

Nijeriya na fuskantar matsananciyar yunwa cikin shekara 10 — Majalisar ɗinkin duniya

Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ta yi gargaɗin cewa Nijeriya na fuskantar yunwa mafi tsanani cikin kusan shekara goma, yayin da rage tallafin agaji ke ƙara tsananta matsalar rashin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabas.

A cewar WFP, a Jihar Borno kaɗai, kusan mutane 15,000 na fuskantar barazanar ƙarancin abinci mai tsanani, yayin da ake hasashen fiye da yara miliyan 13 a Arewa maso Gabas za su kamu da matsalar rashin abinci mai gina jiki a bana.

Hukumar ta ce rikice-rikice, gudun hijira da matsin tattalin arziki sun daɗe suna haddasa matsalar ƙarancin abinci, amma rage tallafin agaji yanzu ya kai al’umma masu rauni matakin da ba za su iya jurewa ba.

Mataimakiyar daraktar WFP na yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka, Sarah Longford, ta ce raguwar kuɗaɗen tallafi da aka samu a shekarar 2025 ya ƙara tsananta yunwa da rashin abinci mai gina jiki a fadin yankin Arewa maso Gabas.

’Yan Majalisar Rivers sun ƙuduri aniyar ci gaba da tsige Fubara

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers sun jaddada ƙudurinsu na ci gaba da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara, bayan wasu ’yan majalisa huɗu da suka ja da baya tun farko sun sake mara wa shirin baya.

’Yan majalisar huɗun — Sylvanus Nwankwo (Omuma), Peter Abbey (Degema), Barile Nwakoh (Khana I) da Emilia Amadi (Obio/Akpor II) — sun bayyana a tsakanin Litinin da Laraba cewa sun fice daga shirin tsige gwamnan ne domin tattaunawa da sulhu.

Sai dai a zaman majalisa da aka gudanar ranar Juma’a, ’yan majalisar huɗun sun janye matsayinsu na baya, suna zargin gwamnan da mataimakinsa da ci gaba da nuna adawa, tare da yin watsi da kiran da ake yi na shiga tattaunawa.

Bayan haka, majalisar ta kaɗa ƙuri’a baki ɗaya inda ta amince da ci gaba da shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara, lamarin da ke ƙara tsananta rikicin siyasar da ke addabar jihar Rivers.

Tinubu na shimfiɗa tubalin bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa — Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma na Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shimfiɗa tubali mai ƙarfi domin bunƙasar tattalin arziki na dogon lokaci da walwalar al’umma baki ɗaya.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi mambobin ƙungiyar Grassroots Advocacy for Tinubu (GAT) 2027 da suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja, kamar yadda wata sanarwa daga Mataimaki na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Rabiu Ibrahim, ta nuna.

Alhaji Mohammed Idris ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu tsauri, wasu ma masu wahala, domin daidaita harkokin ƙasa da sanya Nijeriya kan hanya mai ɗorewa ta fuskar tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, alamu na fara bayyana na farfaɗowar tattalin arziki a muhimman fannoni, yana mai jaddada cewa manufofin gwamnatin na nufin samar da ci gaba mai dorewa da romon dimokuraɗiyya ga ’yan Nijeriya gaba ɗaya.

Gwamnan Jihar Plateau, Muftwang ya yi ta’aziyyar Limamin da ya tseratar da Kiristoci 262 a jihar

0

A cikin makon nan, kasashen Turai da dama sun fara tura sojoji zuwa Greenland a matsayin martani ga barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya maimaita na niyyar mallakar tsibirin ko da ta hanyar amfani da ƙarfi, lamarin da ya janyo rikicin siyasa da tsaro a yankin Arctic. 

Sojojin daga kasashen Denmark, Faransa, Jamus, Sweden, Norway, da Birtaniya sun isa Greenland domin wani aikin atisaye na haɗin gwiwa da ake kira Operation Arctic Endurance, wanda ƙasashen suka tsara domin ƙarfafa tsaron yankin da nuna goyon baya ga ikon Denmark a kan tsibirin. 

Kodayake yawan sojojin da aka tura ba shi da yawa, tura su yana da mahimmanci a matsayin sako ga duk wani yunkurin mamaye ko cin zarafin ‘yancin Greenland, wanda ke ƙarƙashin ikon Denmark kuma tushen tattaunawa cikin ƙungiyar NATO. 

Ma’aikatar tsaron Denmark ta ce manufar aikin atisayen ita ce inganta ƙarfin aiki a yanayin Arctic da kuma tabbatar da tsaro na haɗin gwiwa tare da abokan kawance. Hakanan an ba da sanarwar cewa za a iya ci gaba da matsawa da karfafa wannan rundunar tare da karin hadin kai daga ƙasashen kungiyar NATO a cikin shekarar 2026.