DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 431

Majalisar dattawan Nijeriya ta amince da kudirori 25 a cikin shekara 1

Majalisar dattawan Nijeriya ta amince da kudirori 25 a cikin shekara 1

Majalisar dattawa ta amince da 25 daga cikin kudirori 447 da aka gabatar a zaurenta tun bayan kaddamar da majalisar dattawan ta 10 a shekarar 2023.

Sanata Opeyemi Bamidele, ne ya bayyana hakan a ranar alhamis a Abuja, inda ya ce majalisar ta amince da kudurori 115.

Haka zalika kudurorin 25 da aka amince da su gaba daya zuwa doka, idan aka kwatanta, sun kai kashi 5.24 cikin 100 na dukkan kudurorin da aka gabatar a cikin wa’adin shekarar

A cewarsa, baya ga cikakkun dokoki guda 25 da aka samar, an karanta kasa da kudurori 275 wanda yayi dai dai da kusan kashi 57.65 a karon farko cikin shekarar.

Kungiyar kananan hukumomi tace ba za ta iya biyan dubu N62,000 a matsayin mafi karancin albashi ba

Kungiyar kananan hukumomi tace ba za ta iya biyan dubu N62,000 a matsayin mafi karancin albashi ba.

Kungiyar Kananan hukumomin Nijeriya (ALGON) ta ce kananan hukumomin kasar ba za su iya biyan mafi karancin albashin da kungiyar kwadagon ke nema ba.

Shugaban kungiyar na kasa, Aminu Muazu-Maifata, ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels Television.

Ya ce da kason da ake samu daga asusun gwamnatin tarayya, babu wata karamar hukuma da za ta iya biyan ma’aikata mafi karancin albashi na ₦62,000 da gwamnatin tarayya ke yi balle ma kungiyar kwadagon ta bukaci ₦250,000.

Muazu-Maifata ya ce wasu kananan hukumomin ba su fara biyan ma’aikatan su dubu ₦30,000 da aka amince a matsayin mafi karancin albashi tun a shekarar 2019 ba, kananan hukumomi da dama har yanzu ana biyan ma’aikata ₦18,000 a mafi karancin albashin.

Haka zaka sanya mafi karancin albashi mai yawa haka ba wani abu bane da zai dore domin da dama zai yi musu wahalar biya .

‘Yan sanda sun yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zarginsu da kai wa yan bindiga makamai da alburusai a jihar Katsina

‘Yan sanda sun yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zarginsu da kai wa yan bindiga makamai da alburusai a dazukan jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna kaiwa ‘yan bindiga makami makamai da alburusai a dajin Katsina.

Wadanda ake zargin su ne sun hada da Haladu Isah na kauyen Tsaskiya, karamar hukumar Safana, Abubakar Ahmed  Sha’iskawa, Barhim, Katsina; da Adamu Musa Ba’ude a Jamhuriyar Nijar.

a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq, kamen ya biyo bayan bayanan da aka samu a ranar 6 ga Afrilu, 2024, a ofishin ‘yan sanda da ke Kaita kan munanan ayyukan mutanen uku.

A wata sanarwa da ya fitar ya ce cikin gaggawar ‘yan sanda sun kai dauki tare da samun nasarar gano wadanda ake zargin tare da cafke su a hanyar Dankama a karamar hukumar Kaita.

an gano wadan da ake zargin a hannunsu da kudi naira miliyan daya da dubu dari biyu da uku (N1,203,000.00k) da ake zargin na alburusai ne

An sake saka ranar ci gaba da sauraren shari’ar Ganduje kan shugabancin APC

Kotun tarayya ta sake saka ranar da za ta cigaba da sauraren karar da aka shigar da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje 

Babbar Kotun tarayya da ke ta sake saka 26 ga wannan watan na Yuni, 2024 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren karar da ‘yan yankin arewa ta tsakiya suka shigar da ke neman a cire Abdullahi Umar Ganduje a Sha jam’iyyar APC ta kasa.
‘Yan yankin na arewa ta tsakiya dai na neman a cire Ganduje a ba su shugabancin jam’iyyar kasancewar kamar yadda suka ce, gurbin na yankin ne, bayan da Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukamin.

Sarki Aminu ya nemi karin jami’ai na musamman daga ‘yan sandan Kano

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya samar da tsaro na musamman gabanin bukukuwan Sallah Babba.

Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike ma kwamishinan yan sandan jihar, mai dauke da kwanan watan 10 ga Yuni 2024.

A cewar wasikar Sarkin ya gode wa ‘yan sanda kan tabbatar da zaman lafiya a jihar biyo bayan rikicin da ya biyo bayan dawo da Sarki Sanusi Lamido kan karagar mulki.

Har yanzu bamu cimma matsaya ba kan mafi karancin albashi a Nijeriya – kungiyar kwadago

Kungiyoyin Kwadago sun yi watsi da ikirarin shugaban kasa Bola Tinubu na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaba Tinubu ya yi ikirarin cewa an cimma matsayar ne kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana ja-in-ja tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago a kasar.

A jawabinsa na bikin ranar dimokuradiyya a wannan shekarar ta 2024 da ya gudana a Abuja ranar Laraba, Tinubu ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka ga majalisar dokokin kasar domin ta amince da mafi karancin albashi.

Shugaban ya jaddada cewa gwamnatinsa ta zabi tsarin dimokuradiyya wajen magance bukatun kungiyoyin kwadago a kasar.

Ba ni da alaka da fastocin da ake likawa ni da El-Rufai a Kaduna – Akpabio

Ba ni da alaka da fastocin da ake likawa ni da El-Rufai a Kaduna – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriaya, Godswill Akpabio, ya musanta cewa yana da hannu a yada fastoci a jihar Kaduna da ke nuna kawancen siyasa da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Hakan na a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Majalisar Godswill Akpabio shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Eseme Eyiboh ya fitar a ranar Laraba yana mai cewa yada fastocin aikin wasu mutanene da basa sun zaman lafiya.

Eyiboh ya ce Akpabio ba shi da niyar neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa shida El-rufai a shekarar 2027.

Shugaba Tinubu ya yi tuntube ya fadi a filin taro na Eagle Square

Shugaban kasar dai na kan hanyarsa ta zuwa kusa da motar da za ta dauke shi domin zagaya masu faretin murnar Ranar Dimokradiyya da ake yi a Larabar nan 12 ga Yuni, 2024 a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.
Jami’an tsaro da sauran mataimakansa na musamman dai sun zagaye sun tattare inda shugaban kasar ya yi tuntube kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
A Wani faifan bidiyo da gidan talabijin na TVC ya wallafa mai tsawon dakika 25 ya nuna yadda Shugaba Tinubu ya yi tuntuben a lokacin da ya so kamo karfen mota ya zame bai iya kamowa ba.
Shugaban kasar da ke sanye da fararen kaya da kalar hular da ya saba sanyawa, ya yi ta kokarin ya ruko karfen motar da ke kusa da shi, amma ya gaza, samar sai da ya kai kasa, yayin da mataimakansa da sauran jami’an tsaro da kai masa dauki

Sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci hakimai da su shiga Kano don shiryen shiryen sallah

Sarkin kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya umarci hakimai da su shigo Kano ranar asabar domin shirye-shiryen gudanar da Hawan Sallah.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi ya sanyawa hannu kuma aka turawa hakimai.

Sanarwar ta umarci hakimai da su tabbata sun Isa fadar sarkin dake gidan sarki na Nasarawa a ranar asabar mai zuwa domin gudanar da taron da za a sanar da su yadda hawan sallar zai kasance.

Takardar mai dauke da kwanan wata 10 ga watan yuni 2024, Wanda ya yi dai-dai da 4 ga watan zul-hijja 1445 bayan hijira, tace tun masarautar Kanon ta sanar da shugabannin kananan hukumomin jihar kano yadda zasu taimakawa hakiman don gudanar da bikin sallah babbar cikin lumana.

Mahajjaciya daga jihar Borno ta haihu a wani asibiti da ke birnin Makka

Mahajjaciya daga jihar Borno ta haihu a wani asibiti da ke birnin Makka

Wata Hajiya ‘yar shekara 30 ta haifi da namiji a wani asibitin kasar Saudiyya dake birnin Makkah.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA, mahajjaciyar ta isa dakin gaggawa na Asibitin ne bayan ta yi fama da ciwon nakuda.

Nan take jami’an agajin suka duba halin da take ciki sannan suka kaita dakin haihuwa, inda ta haifi yaron nan take.

Yayin da mahaifiyar ke samun sauki, jaririn mai suna Mohammad yana samun kulawa ta musamman, a cikin asibtin.

Kamar yadda jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito, wannan shine karo na farko da mahajjaciya ta haihu a lokacin Hajjin shekarar 2024.

A halin da ake ciki, Shugaban Hukumar Kula da Lafiya ta NAHCON na aikin Hajjin 2024 a kasar Saudiyya, Dakta Abubakar Ismail ya tabbatar da cewa Mahajjaciyar mace ‘yar jihar Borno ce.

Ya ce kungiyar likitocin ta kasa ta samu rahoto kan ci gaban da aka samu daga kungiyar likitocin jihar Borno inda ta ce matar ta kaucewa aikin tantance lafiyar da ya wajaba a Nijeriya.