DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 432

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a Katsina

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da kakkausar murya ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Kankara da Dutsinma a jihar Katsina.
Da yake bayyana wannan sabon harin da cewa abin takaici ne, shugaban kasar ya tabbatar da cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma karya lagon masu aikata ta’addanci a sassan kasar.
Shugaban kasar ya umurci jami’an tsaro da su yi dukkanin mai yiwuwa don bi ma wadanda aka halaka hakkinsu ta hanyar yin maganin wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin jihar Katsina, iyalai da ‘yan’uwan wadanda harin ta’addancin ya rutsa da su, sannan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mr Ajuri Ngelale, wanda shi ne Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da DCL Hausa ta samu kwafi.

Gwamnantin tarayya ta bayyana ranar hutu domin tunawa da Dimokuradiyya.

Gwamnantin tarayya ta bayyana ranar hutu domin tunawa da Dimokuradiyya.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar dimokradiyya ta bana.

Ministan harkokin cikin gida, Hon. Dr. Olubunmi Tunji-Ojo shi ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar Dr. Aishetu Gogo Ndayako ta fitar.

Ya ce, Yayin da muke bikin ranar dimokuradiyya a cikin tarihin kasarmu mai daraja, bari mu yi tunani a kan kokarin iyayenmu da suka kafa mu kuma tabbatar da cewa Nijeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya, amintacciyar kasa, zaman lafiya da rashin rabuwa.

Yayin da yake taya ‘yan Nijeriya murnar wannan rana, ya bukace su da su dage kan tsarin mulkin dimokradiyya.

Ministan ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar kawo sauyi mai kyau domin farfado da tattalin arzikin kasa da inganta tsaro.

Wa’adin mulki sau ɗaya na shekara shida shi ya dãce ga gwamnoni da shugaban Najeriya – wasu yan Majalisa

Tawagar wasu ‘yan Majalissar wakilai a Najeriya sun tayar da wani sabon batu na buƙatar a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyara, yadda za’a mayar da shugabancin kasar tsarin karba-karba a tsakanin yankuna shida na ƙasar.

Waɗannan ‘yan Majalissa sun kuma buƙaci idan aka tashi yin gyaran fuskar na tsarin mulkin, a mayar da wa’adin shugaban ƙasa da na gwamnoni shekara shida sau ɗaya tal, sabili da hakan zai taimaka gãya wurin rage kashe kudin gudanar da harkokin mulki a ƙasar.

Bola Tinubu ya nada shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da nadin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda wato ‘Police Service Commission’.
Kazalika, shugaban kasar ya kuma amince da nadin Chief Onyemuche Nnamani a matsayin Sakataren hukumar da kuma DIG Taiwo Lukanu (Rtd) a matsayin mamba a hukumar.
Bugu da kari, shugaban kasar ya kuma amince da nadin Mohammed Seidu a matsayin shugaban asusun tallafa wa ‘yan sanda na ‘Police Trust Fund’.
Wadannan nade-nade na a cikin wata sanarwa daga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Mr Ajuri Ngelale da DCL Hausa ta samu kwafi.

Atiku da Kwankwaso da Peter Obi za su yi magana ga yan Najeriya ranar bikin Dimakuradiyya

A ƙoƙarin ganin an karɓe mulkin Najeriya daga shugaba Tinubu, wata tawagar da ta kira kanta ta ‘yan kishin Najeriya wato “The Patriots” a turance, ta tsara yadda zata haɗa tsofaffin ‘yan takarar shugabancin Najeriya na manyan jam’iyun adawa uku a ƙasar su yi wa ‘yan Najeriya bayani a ranar bukin dimakuradiyya a Legas, jihar shugaba Tinubun.

Duk da dai wannan ba shine karon farko ba da ‘yan takarar Atiku Abubakar na PDP, da Kwankwaso na NNPP da kuma Peter Obi na Leba party ke hada hanya a siyasance amma daga bisani kowa ya kama tasa, a wannan karon, wannan tawagar ta ‘yan kishin Najeriya da alamu tana ƙoƙarin jifar tsuntsu biyu ne da dutse guda, saboda a sanarwar da ta fitar ta hannun Farfesa Anthony Kila, ta ce a wannan taro za kuma su nemi a samar da kundin tsarin mulki da kowa zai more shi a Najeriya.

Wannan sanarwa ta nuna cewa a babban taron na ƙasa kan bikin dimakuradiyyar Najeriya, za’a karkata sosai kan batun samar da kundin tsarin mulkin Nijeriya da kowa zai amfana a ƙasar, haka ne ma ya sa aka yi wa taron lakabi da “Samar da makoma mai ma’ana ga ‘yan Najeriya ta hanayar samar da tsarin mulki irin na jama’a” inji kwamitin tsare-tsaren wannan taro.

A baya-bayanan dai Atiku Abubakar da Peter Obi sun gãna tare da tattaunawa kan yadda za su haɗa karfi wurin karɓe mulki daga shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, saidai a iya cewa idan dukkanin tsofin ‘yan takarar uku suka kasance a taron da za ayi ranar 12 ga wannan wata na Yuni, to shine karon farko da zasu kasance tare kan manufa guda ta siyasa tun bayan shan kaye a zaɓen shekarar 2013 na shugaban kasa da ya gabata a Najeriya.

Ba’a yi aikin da aka ware sama da Naira biliyan guda domin sa ba a zamanin Hadi Sirika – shaidan EFCC

Shaida na farko da ya baiyana a kotu kan shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar cewa har ya yi ritaya daga aikin gwamnati a watan Mayu na shekara ta 2023 ba’a aiwatar da aikin kwangilar da aka bayar na Naira miliyan dubu ɗaya da ɗari huɗu ba a filin sauƙa da tashin jirage na jihar Katsina.

Shaidan na EFCC mai suna Azubuike Okorie, wanda tsohon Darakta ne a ma’aikatar ta sufuri lokacin da Hadi Sirikan ya ke Minista, ya tabbatar da hakan saboda a cewar sa, a lokacin da Hadi Sirika ya ke Ministan, tare da shi su ke zagayawa suna duba dukkan ayyukan kwangila da ma’aikatar sufuri ta bada.

Shaidan na EFCC ya kuma ce Kamfanin Al-Buraq aka baiwa wancan kwangila na filin jirgi da ke Katsina, amma a lokacin da suka je duba aikin tare da kwamitin sa, wannan Kamfani na Al-Buraq ya tattara kayan sa ya yi gaba ba tare da yayi wani aiki ba.

Ana zargin Hadi Sirika da hada baki da surukin sa da ma ‘yar sa Fatima da wai kamfanoni wurin yin almundahana na kuɗaɗen kwangila da suka kai sama da Naira biliyan biyu.

Najeriya tana asarar biliyoyin Naira a fasa kwafrin man fetur da ‘yan sumoga

Shugaban hukumar kwatsam a Najeriya Bashir Adewale Adeniyi ya baiyana cewa masu fasa kwafrin man fetur zuwa ƙasashe makwafta su na janyo wa Najeriya rashin samun kuɗin shiga saboda ƙazamar riba da su ke samu idan suka fitar da man.

Shugaban na Kwatsam ya ce yanzu sun ƙirƙiri wata runduna ta sintiri da su ka laƙa wa suna “Operations Whirlwind” wanda a yanzu haka sun yi nasarar kwace mai sama da lita dubu 150 cikin makwanni biyu daga masu fasa kwafrin, wadda kuɗin su ya kai sama da Naira miliyan ɗari, ya na mai cewa wannan ƙalilan ne daga cikin haramtacciyar kasuwanci na biliyoyin Naira da ‘yan sumogan ke yi.

A yayin zantawa da yan jarida a Yola, jihar Adamawa daya daga cikin jihohi da ake fasa kwafrin man zuwa jamhuriyar Kamaru, yayi alwashin kawo ƙarshen wannan mummunar al’ada.

Gwamna Abba na Kano ya zargi Ganduje da sayar da makarantun Gwamnati

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yana zargin tsohuwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin jãgorancin Abdullahi Ganduje da mayar da wasu makarantun Gwamnati shaguna ta kuma sayar da wasu.

Gwamnan Kanon ya ce gwamnati da ta shude a Kano ta yi wa ɓangaren ilimi riƙon sakainar kashi saboda haka ne ya sanya shi aiyana dokar ta ɓaci a ɓangaren na ilimi a Kano.

Gwamna injiniya Abba Kabir Yusuf ya baiyan cewa zai haɗa kai da ƙungiyar malami NUT dan farfaɗo da ilimi a Kano, saboda da shi ake samar da cigaban al’umma.

Ya nuna damuwa matuƙa kan yawan yara da ke barin makaranta a Kano, ya kuma ce akwai wasu yara kusan miliyan guda da basu samu damar shiga makaranta ba.

Jihar Kano ita ce ta 18 a jerin jihohin Najeriya da suka fi cigaba ta ɓangaren ilimi mai kaso 48.9 na wadanda suka je makaranta inji hukumar kula da ilimi ta majalisar dinkin duniya UNESCO, amma kuma ita ce ta ɗaya a yawan al’umma, mai sama da mutane miliyan tara.

Wani kansila ya dauki nauyin mayar da yara 120 makarantun boko a Kano

Wani kansila ya dauki nauyin mayar da yara 120 makarantun boko a Kano

Kansila a unguwar Achika da ke kamarar hukumar wudil a kano,Bashir shehu Aliyu ya dauki nauyin maida yara 120 wadanda basa zuwa makaranta.

A wani taron bayar da tallafin karatu da akayi a garin, kansilan yace dukkan wayanda su kaci gajiyar tallafin marayune,kuma sunyi hakanne domin tallafawa tare da inganta rayuwar yaran.

A cewarsa, zai dauki nauyin wadanda suka ci gajiyar karatunsu tun daga karamar sakandire har zuwa babbar sakandare ko da kuwa ba ya rike da wani mukamin siyasa.

Ina ba ‘yan mata da ke sha’awar shiga harkar fim shawara da kada su shiga – Hadiza Gabon

Hadiza Gabon a cikin shirin da take gayyatar fitattu a bangarori daban-daban na Ganin Room Talk Show, ta ce idan mutum ya shiga fim, zai yi suna a duniya da hakan ke sanya bakin mutane ya yi masa yawa na ko da bai yi abu ba, za a ce ya yi.

Jarumar masana’antar ta Kannywood ta ce akwai ma mutane da yawa da ke yi wa ‘yan fim kallon ‘yan marasa tarbiyya. 
Wadannan da ma karin wasu hujjoji ne Hadiza Aliyu Gabon ta bayar game da shawararta ga mata masu tasowa da ke son shiga harkar fim a wannan lokacin.