DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 433

Manoma a Nijeriya sun ce cire tallafin man fetur da matsalar tsaro na kawo musu cikas

Manoma a Nijeriya sun ce cire tallafin man fetur da matsalar tsaro na kawo musu cikas

Manoma sun yi hasashen matsalar karancin abinci za ta iya karuwa a nan gaba, inda su kayi zargin cire tallafin man fetur da rashin tsaro sune dalilin faruwar hakan.

Manoman sun yi hasashen cewa za a samu karancin abinci a nan gaba ga ‘yan Nijeriya game da matsalar hauhawar farashin kayan abinci da ake fama da ita a kasar.

Hakan dai na faruwa ne yayin da manoman suka dora laifin cire tallafin da ya kara tsadar safarar kayan amfanin gona, da rashin tsaro da ke ci gaba da kawo cikas ga noma a matsayin wasu dalilan da suka haddasa matsalar abinci a Nijeriya.

Manoman, sun yi kira ga ‘yan kasar da sai sun tashi tsaye don kara farashin kayan abinci, ya na nuni da cewa matsalar abinci na iya ci gaba da kasancewa har zuwa watan Agusta.

Tinubu ya fi Obi da Atiku cewar wani jigi a jam’iyyar Labour Party.

Tinubu ya fi Obi da Atiku cewar wani jigi a jam’iyyar Labour Party.

Tsohon darakta janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Doyin Okupe, ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su yi gaggawar hukunta gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A wata hira da aka yi da shi ranar a gidan talabijin na Channels, Okupe ya shawarci ‘yan kasar da su yi watsi da sukar gwamnatin Tinubu kamar gwamnatocin baya.

Ya ce shugaban kasar ya gaji matsalar tattalin arziki, inda ya kara da cewa ya hau kan karagar mulki ne a lokacin kasar tana cikin wani yanayi da ba a saba gani ba.

Don haka akwai bukatar a kara bashi dama domin a shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar.

NLC ta bukaci gwamnati ta amince da N250,000 a matsayin mafi karancin albashin

 NLC ta bukaci gwamnati ta amince da N250,000 a matsayin mafi karancin albashin 

Kungiyar kwadago ta NLC a Nijeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta amince da N250,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin sabanin N494,000 da ta bukata a farko.

An gudanar da taro domin samun matsaya tsakanin wakilan gwamnatin Nijeriya da kuma na kungiyoyin kwadago ta yadda za a cimma matsaya daya.

Sai dai wakilan gwamnati a yayin taron sun yi wa kungiyoyin kwadago karin N2,000 inda suka bukaci su amince da N62,000 a matsayin sabon albashin.

An gudanar da Sallar Nafila Kan tsadar rayuwa a Jigawa

 Al’ummar musulmi a garin Dutse Babban Birnin jihar Jigawa sun gudanar da Sallar Nafila da addu’o’i na musamman domin rokon Allah ya kawo karshen matsalar rashin tsaro da kalubalen tattalin arziki da ke Nijeriya ke ciki wanda ya haifar da matsananciyar wahala ga ‘yan kasar.

Kwankwaso ya maka EFCC a kotu

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya maka hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC kotu domin hana kama shi.
An gabatar da karar da aka shigar a babbar kotun Kano a gaban mai shari’a Yusuf Ubale.
Wata majiya ta bayyana cewa karar na da nufin hana hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC tsare shi.
Idan dai za a iya tunawa, EFCC na binciken zargin da ake yi wa Kwankwaso kan kudi naira biliyan 2.5 na kudaden yakin neman zabe da ke da alaka da jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a kan Kwankwaso.

Gwamnati na aiki don inganta tattalin arzikin kasa – George Akume

 Gwamnati na aiki don inganta tattalin arzikin kasa – George Akume,

Sakataren Gwamnatin tarayya

Sakataren gwamnatin tarayya,George Akume ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankulansu duk da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta, gwamnati na aiki don inganta tattalin arzikin kasar.

Tsabagen kishi zai hana na auri dan fim – Rayya Kwana Casa’in

 Tsabagen

kishi zai hana na auri dan fim – Rayya Kwana Casa’in

Fitattaciyar jaruma a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango da ke taka rawar Rayya ta ce kishi ba zai bari ta auri dan fim ba.

Rayya ta sanar da hakan ne yayin zantawa da jaruma Hadiza Gabon a shirin nan na Gabon show.

“Ba zan iya auren dan fim ba, saboda ina da kishi sosai” in ji Rayya Kwana Casa’in

Likitoci za su tsunduma yajin aiki a jihar Kano.

 Likitoci za su tsunduma yajin aiki a jihar Kano.

Kungiyar likitocin hakori ta kasa (NAGGMDP) reshen jihar Kano ta bayyana shirin fara yajin aikin gargadi na tsawon mako biyu domin nuna rashin amincewa da wasu matsaloli da su ka dabaibaye tsarin kiwon lafiyar jihar.

A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Dr Aminu Kabir Muhammad ya sanya wa hannu a ranar Laraba, kungiyar ta bayyana cewa za a fara yajin aikin a asibitocin fadin jihar daga karfe 12:00 na safe ranar 17 ga watan Yuni 2024.

‘Yan bindiga sun hallaka mutane kusan 30 a wani sabon hari a kauyen Katsina

‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Kunamawa na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina a ranar Laraba.
Harin kamar yadda majiyar DCL Hausa ta sanar ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 27 tare da raunata masu yawa.
Bayanai sun ce maharan sun je kauyen ne da yammaci, inda suka bude wuta su na harbin kan mai uwa da wabi kan mutanen gari, suka kashe masu karar kwana suka raunata masu tsautsayi kamar yadda majiyar ta tabbatar.
Kauyen Kunamawa bai fi nisan kilomita 10 ba daga hedikwatar karamar hukumar Safana ta jihar Katsina. 
Wata majiyar ta ce mutanen da suka rasu, sun kai 30, a yayin da wadanda suka samu raunuka suke kwance a asibiti karkashin kulawar likitoci.
Wasu bayanan sun ce matasan yankin sun gudanar da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga don neman agajin hukumomi kan yawaitar hare-haren tun bayan saukar ruwan sama.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu wata sanarwa a hukumance game da harin daga hukumomi.

Benin ta zargi jami’an gwamnatin Nijar da shiga wajen loda danyen man kasar ta barauniyar hanya.

Hukumomin Bénin sun zargi jami’an gwamnatin Nijar da suka tsare da shiga wajen loda danyen man Nijar ta barauniyar hanya

Babban gata mai shari’ar kasar Bénin ne a cikin wata takarda da ya fitar ya ce tawagar jami’an gwamnatin Nijar din su biyar karkashin jagorancin mataimakiyar daraktan kamfanin WAPCO ta shiga cibiyar loda danyen man na Nijar ne da ke Semé Kpodji ta barauniyar hanya ba tare da an tantance su ba don haka ne suka kama su

Tuni dai a nasu bangare hukumomin na Nijar suka dauki matakin dakatar da tura danyen man har sai hukumomin Bénin din sun jami’an nasu