DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 434

Za a ci gaba da amfani da VAR a gasar firimiya

 Kungiyoyin da ke buga gasar firimiyar kasar Ingila sun amince a ci gaba amfani da VAR bayan kada kuri’a.

An kada kuri’a a wannan Alhamis din nan inda aka cimma matsaya a ci gaba da amfani da VAR din.

Kungiyar Wolves ce kadai ta zabi a daina amfani da VAR.

Kotu ta fara zaman Shari’ar rikicin masarautar Kano

 Babbar kotun tarayya da ke Kano ta fara zaman sauraron karar da aka shigar a kan hukuncin da majalisar dokokin jihar Kano da gwamnatin jihar suka yanke na mayar da Kano zuwa masarauta guda daya da kuma cire dukkan sarakunan da gwamnatin baya ta kirkira.

NDLEA sun kama mahajjata da hodar iblis a Legas

 NDLEA sun kama mahajjata da hodar iblis a Legas 

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA a Nijeriya sun kama mahajjata hudu masu niyya zuwa Saudiyya da hodar iblis a Legas.

Kakakin hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja. 

Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kai samame wani otal mallakin Emerald, Ladipo, Oshodi, jihar Legas, a ranar 5 ga watan Yuni inda suka cafke mahajjatan bayan samun bayyanan sirri.

An kama mahajjatan Nijeriya hudu a Saudiyya

 An kama mahajjatan Nijeriya hudu a Saudiyya

Mahajjatan dai sun fito ne daga babban birnin tarayya Abuja, inda aka kama su bisa laifin kin sanya katin shaidar su na NUSUK. Mahajjatan dai na a jirgi na 5,6,7 da na 8 a alhazan Abuja. An kama su ne a bakin masaukansu.

Obasanjo ya shawarci gwamnoni su samar da Abinci don a samu saukin rayuwa

 Obasanjo ya shawarci gwamnoni su samar da Abinci don a samu saukin rayuwa

Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci gwamnonin jihohi da su mai da hankali kan samar da abinci tare da yin kira gare su da su ba da fifiko kan manufofin da suke inganta rayuwar mutane. 

Obasanjo ya ba bayyana hakan ne a ranar Laraba a Sokoto a wajen kaddamar da rukunin gidaje 136 da gwamnatin jihar Sokoto ta saya a kan kudi Naira biliyan 1.8. 

Tsohon shugaban kasar ya kasance a Sokoto a ziyarar kwanaki biyu don kaddamar da ayyukan da Gov. Ahmed Aliyu ya aiwatar yayin bikin cikarsa shekara daya kan mulkin jihar. 

Tafiya Mabudin Ilmi: Abin da ya faru da ni daga Kano zuwa Yola jihar Adamawa

Direban da ya dauke mu zuwa Yola jihar Adamawa mai shegiyar gardama ‘kamar makahon jaki’. Bayan motarmu ta cika a tasha ya fita za mu kama hanya ashe bai sha mai ba, yana fita tasha ya ga wani gidan man gwamnati NNPCL an bude, ga layi hada wadanda suka kwana a wurin, amma ya yanki layi daga tsakiya ya kutsa motarsa. Kan ka ce ‘kobo’ ya samu da ya shiga. Da ya ke masu azancin magana na cewa ‘mugu shi ne ya san makwantar mugu’ take tsagerun gidan man nan suka yi waje da mu duk kuwa runtsin da ke da akwai. Duk da taurin kansa, sai da ya sauka ya je da lalama da ban hakuri ya shiga layin ‘yan alfarma.
Jihohi uku ne ake shiga idan za a je Yola daga Kano, idan ka cire Kano din, sai Jigawa, Bauchi da Gombe. A kan hanya na yaba kokarin gwamnatocin jihar Jigawa na yadda suka shimfida tituna masu kyau (ba laifi). Hanya mai gargada kuwa sai mutum ya shiga yankin jihar Bauchi. Daga Darazo jihar Bauchi kafin mutum ya isa Gombe, sai ka ji kamar direba ya tsaya ka tafi a kafa, (ni kadai na ji abin da na ji).
Daga Gombe titin zuwa Yola jihar Adamawa.
Akko-Dukku-Kumo-Billiri-Kaltungo kafin a isa Ngurore zuwa Numan, na ga tsaunuka manya-manya da suka zagaye yankin.
Da ka fita Kaltungo kafin Ngurore, sai kwanoni hagu da dama, kafin ka gama ta hagu ka waiga a ta dama. Ga tsauni ga hawa da sauka. Mota na kwana a irin abin da Bafulatani da ya hau keken da ba birki, yana cewa kwaneri keke, da kwana ta kiya, sai ya ce to birkel. Haka motoci ke yi a wannan hanya.
A karamar hukumar Kumo ta jihar Gombe ne za ka ga yadda maza ke fita waje su shimfida tabarma ko darduma su sha iska, haka mata ke yi. Kazalika, yadda awaki ke yawo a cikin gari haka alade ke nasa yawon. Oh! Na ga abin mamaki, ko don hakan ya saba da al’adar da na tashi cikinta? Ga noma al’ummar yankin Kumo na yi na fitar hankali (kun san idan Bakatsine ya ce haka, to yabo ne) amma wata irin hudar noma na ga ana yi kamar ‘zamiyar-zakara’. Mutanen Kumo na jinjina muku. Mata a bisa babur roba-roba hada goyon biyu duk na gani a yankin Kumo ta jihar Gombe.
Kai jama’a, har sai da na tausaya wa kaina, ga bacci a idona, amma ina ido kifi ido bado, ina son in runtsa amma kuma Ina son ganin gari/hanya, tun da ban taba shiga Arewa ta gabas ba sai a wannan lokacin. Na dauka irin abin da bature ke cewa ‘i have seen it all in life’ ashe ban ga komai ba, sai da na ga direban da ya dauko mu ya aiki soja neman canjin 1k don ya bashi na-goro N50.Duk a cikin yankin jihar Gombe ne na an gina daki, an buga masa kwano, amma an yi bangon danga wato darni na cuci, (ban san ya suke kiransa a can ba).
Abin da na lura da shi, shi ne, akwai shingen jami’an tsaro a kan titin, kama daga sojoji, ‘yan sanda, jami’an kiyaye hadurra na Road safety, na binciken ababen hawa na VIO, Civil Defense, Immigration da Kwastam, amma babu wanda bai tambayarku katin shaidar zama dan kasa. Amma wasu daga cikin fasinjojin da muke tare sun ce duk salon karbar na-goro ne.
A iya abin da idona ya gani, a halin yanzu yankin arewa maso gabas ya fi arewa maso yammacin Nijeriya zaman lafiya da kwanciyar hankli. A nan ne za ka ga gidajen da ba su wuce biyar zuwa 10 ba, sun tayar da gari, kuma su na zamansu lafiya.
Abdullahi Garba Jani
agarbajani@gmail.com
04/06/2024

Tinubu ya shiga ganawa da ‘yan kwamitin karin mafi karancin albashin

 Tinubu ya shiga ganawa da kwamitin karin mafi karancin albashin 

Mambobin kwamitin da ke tattauna yadda za a fitar da sabon mafi karancin albashi a Nijeriya sun gana da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja. 

Taron na zuwa ne bayan dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki biyar da kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi na Najeriya Labour Congress, (NLC) da kungiyar kwadago, (TUC) suka yi.

 Majiyar DCL Hausa ta ce kwamitin ya ziyarci shugaban na Nijeriya ne domin ya sanar da shi yadda kungiyoyin kwadago suka bukaci a yi musu kari akan N60,000 na tayin da gwamnati ta yi.

Daga cikin matsayar da aka samar har da karin da kungiyoyin kwadago suka nema na a biya ma’aikata sama da Naira Dubu Sittin a matsayin sabon mafi karancin albashi.

Ana zargin sabuwar amarya da guntule al’aurar angonta a Kaduna

 Ana zargin sabuwar amarya da guntule al’aurar angonta a Kaduna

Wata sabuwar Amarya mai suna Habiba Ibrahim, ta guntule al’aurar angonta Salisu Idris, mai shekaru 40, yayin da yake barci.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kudan da ke jihar Kaduna tun a ranar 26 ga watan Mayu bayan ya dawo daga sallar asuba.

Rahotanni sun ce tuni ‘yan sanda suka kama ta. 

NLC da TUC sun janye yajin aiki a Nijeriya

 

NLC da TUC sun janye yajin aiki a Nijeriya 

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a Nijeriya sun sanar da janye yajin aikin da suka fara a ranar Litinin.

Shugaban kungiyar ta TUC Festus Osifo ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja bayan wani taron hadin gwiwa na majalisar zartarwa na kasa na hadin gwiwa na kungiyar.

Za a fitar da sanarwar nan ba da jimawa ba , in ji shugaban kwadagon.

A ranar Litinin ne kungiyoyin biyu suka tsunduma yajin aiki saboda korafe – korafensu kan karin kukldin wutar lantarki da kuma rashin cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi.

Ma’aikatar kwadago a Nijeriya ta bukaci NLC su janye yajin aiki

 Ma’aikatar kwadago a Nijeriya ta bukaci NLC su janye yajin aiki 

Ministar kwadago da samar da ayyukan yi a Nijeriya Nkeiruka Onyejeocha, ta yi kira ga kungiyoyin kwadago da su dakatar da yajin aikin da suke yi domin yana gurgunta harkokin tattalin arziki a fadin kasar

Onyejeocha ta ce Gwamnatin Tarayya ba ita kadai ke da alhakin yanke hukunci kan kayyade nawa zai zama sabon mafi karancin albashi ba saboda ya zama dole a ji ta bakin gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu.

A cewarta, har yanzu wasu gwamnatocin jihohin ba su iya biyan mafi karancin albashi na ₦30,000 da aka amince da shi a shekarar 2019 ba, ina ga sabuwar bukatar NLC na a mayar da mafi karancin albashin ya koma N494,000