DCL Hausa Radio
Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 435

Umurnin kotuna na cin karo da juna kan takaddamar sarautar Kano

Bayan umarnin babbar kotun jihar Kano na bukatar Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya fice daga ƙaramar fãda dake Nassarawa a Kano, da kuma umarnin wata babbar kotun tarayya a Kanon da ta bukaci jami’an tsaro su fitar da Sarki Sunusi shi ma daga babbar fadar Sarkin Kano, sai ga wani umarni kuma daga babbar kotun jihar Kano har ila yau, wadda ya haramta wa jami’an tsaro aiwatar da umarnin kotun taraiyar kan sarki Sunusin.

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu wacca ta bada wannan umarni, ta kuma haramta wa jami’an tsaron duk wani yunkuri na kama ko cin mutuncin Sarki Sunusin.

Sarki Sunusi shi da madakin Kano da makaman Kano tare da Sarkin Dawaki da kuma Sarkin Bãyi suka shigar da kara a babbar kotun ta Kano.

Kotun ta ɗage zama kan wannan batu zuwa ranar 13 ga watan Yuni.

Atiku da Kwankwaso da Peter Obi za su yi magana ga yan Najeriya ranar bikin Dimakuradiyya

A ƙoƙarin ganin an karɓe mulkin Najeriya daga shugaba Tinubu, wata tawagar da ta kira kanta ta ‘yan kishin Najeriya wato “The Patriots” a turance, ta tsara yadda zata haɗa tsofaffin ‘yan takarar shugabancin Najeriya na manyan jam’iyun adawa uku a ƙasar su yi wa ‘yan Najeriya bayani a ranar bukin dimakuradiyya a Legas, jihar shugaba Tinubun.
Duk da dai wannan ba shine karon farko ba da ‘yan takarar Atiku Abubakar na PDP, da Kwankwaso na NNPP da kuma Peter Obi na Leba party ke hada hanya a siyasance amma daga bisani kowa ya kama tasa, a wannan karon, wannan tawagar ta ‘yan kishin Najeriya da alamu tana ƙoƙarin jifar tsuntsu biyu ne da dutse guda, saboda a sanarwar da ta fitar ta hannun Farfesa Anthony Kila, ta ce a wannan taro za kuma su nemi a samar da kundin tsarin mulki da kowa zai more shi.
Wannan sanarwa ta nuna cewa a babban taron na ƙasa kan bikin dimakuradiyyae Najeriya, za’a karkata sosai kan batun samar da kundin tsarin mulkin Nijeriya da kowa zai amfana da shi, haka ne ma ya sa aka yi wa taron lakabi da “Samar da makoma mai ma’ana ga ‘yan Najeriya ta hanayar samar da tsarin mulki irin na jama’a” inji kwamitin tsare-tsaren wannan taro.
A baya-bayanan dai Atiku Abubakar da Peter Obi sun gãna tare da tattaunawa kan yadda za su haɗa karfi wurin karɓe mulki daga shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, saidai a iya cewa idan dukkanin tsofin ‘yan takarar uku suka kasance a taron da za ayi ranar 12 ga wannan wata na Yuni, to shine karon farko da zasu kasance tare kan manufa guda ta siyasa tun bayan shan kaye a zaɓen shekarar 2013 na shugaban kasa da ya gabata a Najeriya.

Majalisar dattawa a Najeriya ta tabbatar da ƙudirin dokar sauya taken ƙasa daga wanda aka saba.

Wannan na zuwa ne washe garin da ministan shari’a na ƙasar ya nuna buƙatar a ji ra’ayin sauran ‘yan Najeriya kan wannan sauyi Na taken ƙasa wato national anthem a turance a lokacin da ya halarci taron jin bahasin masu ruwa da tsaki a harabar majalisar dokokin kasar.

Ƙudirin dokar ya wuce dukkan matakai da suka kamata a majalisun biyu na Najeriya wato ta wakilai da ta dattawa, abin da yanzu ya rage kadai shi ne sa hannun shugaban ƙasa.

Sai dai bisa kalaman ministan na Shari’a da yiyuwar a samu tsaiko wurin sanya hannun shugaban ƙasa kan dokar wacca ke buƙatar a koma amfani da tsohon taken Najeriya da aka maye gurbin sa a shekarar 1978.

Magagin tsufa ne ke damun Obasanjo -Jamiyar APC

Jami’ya mai mulki a Nigeria wato All Progressive Congress ta bakin ɗaya Daraktan yãɗa labaran ta Bala Ibrahim ta yi raddi ga tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo bisa sūkar gwamnatin Tinubu da yayi cewa ba ta amfani da kuɗin tallafin man fetur ta hanyar da ta dãce.

Bala Ibrahim wadda ya baiyana Obasanjo a matsayin mai halin kunshe jama’a, ya ce alamun magagin tsufa sun fara baiyana daga Obasanjon wadda a cewar sa tun daga lokacin da ya rasa samun nasarar yin ta zarce a mulkin Najeriya wa’adi na uku ya ɗau gaba a zuciyar sa.

Ya ce wannan hali na Obasanjo ba yanzu ya fara a kan wannan gwamnati ta Tinubu ba saboda tsofin shugabanni irin su Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan bai bar su ba a zamanin da su ke mulki, sai dai ya baiyana cewa shi Obasanjo ne ma a zamanin mulkin sa ya rikirkita tattalin arzikin ƙasar.

A wata sanarwar da kakakin Obasanjo Kehinde Akinyemi ya fitar a ‘yan kwanakin nan ne tsohon shugaban kasan ya ce koda ya ke matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka sun zama wãjibi, amma kuma gwamnatin tasa bata yin abin da ya dãce wurin aiwatar da matakan, musamman a ɓangaren sarrafa kuɗaɗen tallafin man fetur da ta cire.

Gwamnatin Nijeriya za ta kafa cibiyoyin fasaha da kirkire kirkire guda 24 a fadin kasar.

Gwamnatin Nijeriya za ta kafa cibiyoyin fasaha da kirkire kirkire guda 24 a fadin kasar.

Gwamnatin tarayya ta ce ta kuduri aniyar samar da cibiyoyin fasaha da kirkire-kirkire 24 a fadin kasar nan. 

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin bikin tunawa da ranar yara ta bana mai taken “Haɓaka rayuwar yaran Nijeriya ta hanyar ingantaccen ilimi da haɓaka ƙwarewa.

Ya ce gwamnatin ta bullo da muhimman tsare-tsare masu kawo sauyi domin samar da ingantaccen yanayin koyo a fadin kasar nan. 

 

Tinubu, wanda ya samu wakilcin karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa kan duk wani abu da ya shafi walwala da ci gaban yaran Nijeriya baki daya.

 

 Ya ce gwamnatin tarayya ta kafa tsarin bayanan ilimi na kasa, ta amince da bunkasa fasaha ga dukkan matakan ilimi da kuma horar da malamai a kan fasahar dijital. 

 

Ya Kara da cewa,Gwamnati ta himmatu wajen samar da cibiyoyin fasaha da kirkire-kirkire guda 24 da cibiyoyin kasuwanci a fadin kasar nan.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin bikin tunawa da ranar yara ta bana mai taken “Haɓaka rayuwar yaran Nijeriya ta hanyar ingantaccen ilimi da haɓaka ƙwarewa da fasa.

Gwamnatin ta bullo da muhimman tsare-tsare masu kawo sauyi domin samar da ingantaccen yanayin koyo a fadin kasar nan. 

 

Tinubu, wanda ya samu wakilcin karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa kan duk wani abu da ya shafi walwala da ci gaban yaran Nijeriya baki daya.

Gwamnatin Nijeriya ta himmatu wajen samar da cibiyoyin fasaha da kirkire-kirkire guda 24 da cibiyoyin kasuwanci a fadin kasar nan.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada mukaddashin shugaban Gidan Talabijin na ARTV.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada mukaddashin shugaban Gidan Talabijin na ARTV.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Hajiya Hauwa Isa Ibrahim a matsayin mukaddashin darakta na gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV).

SolaceBase ta ruwaito cewa nadin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa manajan daraktan gidan Mustapha Indabawa.

Wasikar mai dauke da sa hannun Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jihar Kano tare da kwanan watan 27 ga watan mayu 2024,

wasikar ta umurce ta da ta karbe harkokin gidan talabijin da radiyon nan take.

Har zuwa nadin nata, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ita ce mataimakiyar darakta a gidan talabijin na Abubakar Rimi.

Tinubu ya koka da halin da kananan hukumomi ke ciki a Nijeriya.

Tinubu ya koka da halin da kananan hukumomi ke ciki a Nijeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa kan tabarbarewar harkokin kananan hukumomin kasar nan, yana mai alakanta hakan da koma bayan ci gaba da kuma kasa shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasa.

Da yake jawabi a wajen wani taron kasa na kwana guda kan kalubalen tsaro a Nijeriya da kuma shugabanci nagari a matakin kananan hukumomi, shugaban ya jaddada cewa shugabanci nagari a dukkan matakai na da matukar muhimmanci wajen samar da ci gaba da rage rikice-rikice a tsakanin al’umma.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan tsaro,Badaru Abubakar, ya ce jihar da ke da kyakkyawan shugabanci ta fi dacewa da magance matsalolin cikin gida kamar yaki da bata gari, tada kayar baya, da rikicin kabilanci da sauransu.

Haka zalika ya ce rashin shugabanci nagari yana haifar da cin hanci da rashawa, rashin zaman lafiya, siyasa, rashin daidaiton tattalin arziki, da kuma tashe-tashen hankula a cikin al’umma wanda ba wai kawai na gurgunta tsaron lafiyar al’umma ta hanyar hana mutane bukatun su na yau da kullun, har ma babbar barazana ce ga tsaron kasa ta hanyar samar da yanayi maikyau ga ‘yan kasa.

Jirgin farko na alhazan Kano ya tashi zuwa kasa mai tsarki.

Jirgin farko na alhazan Kano ya tashi zuwa kasa mai tsarki.

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na alhazan jihar Kano domin zuwa kasa mai tsarki dan gudanar da aikin hajjin bana.

Solace Base ta rawaito cewa, jirgin ya tashi da misalin karfe 11:41 na safiyar ranar litinin, tare da adadin mahajjata 578 a cikin jirgin Max Air B747 da ma’aikatansa 20, wanda ya nufi filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jeddah.

Gwamna Abba Kabir ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari na jihar da ma Nijeriya a kasa mai tsarki tare da yi wa jihar da kasa baki daya addu’a.

A nasa bangaren, Darakta Janar na Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya ce mahajjatan da ke cikin jirgin sun fito ne daga kananan hukumomi hudu na jihar da suka hada da Gwale,Dala,Fagge da kuma Ungoggo.

Mataimakin gwamnan Kano ya janye zargin da ya yiwa Nuhu Ribadu.

Mataimakin gwamnan Kano ya janye zargin da ya yiwa Nuhu Ribadu.

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya janye zargin da ya ke yi wa Nuhu Ribadu,mai ba da shawara kan harkokin tsaro kan rikicin masarautar Kano.

Gwarzo ya yi zargin cewa Ribadu ne ya sa aka dawo da Aminu Bayero, wanda aka tube daga sarautar Kano, ta hanyar ba shi jiragen sama guda biyu masu zaman kansu tare da rakiyar jami’an tsaro.

Bayan dawo da Muhammadu Sanusi II,kan karagar mulki,Aminu Ado Bayero ya koma masarautar ranar Asabar,inda ya koma gidan sarki na nassarawa a Jihar.

Gwarzo yace batun cewa an rako tsohon sarki Aminu Ado da jirage biyu tare da rakiyar jami’an tsaro da sukai zargi basu fahimci batun daidai ba.

Sai dai a wata wasika da ya musanta zargin ta hannun lauyoyinsa, Aliyu & Musa Chambers, Ribadu ya bukaci mataimakin gwamnan da ya nemi afuwa.

Wasikar tace wanda suke karewa tare da ofishinsa sun dauki abin da mahimmanci dan haka suna bukatar abasu cikakkiyar hujja akan zargin.

Mun gano wasu na kokarin tayar da tarzoma a kano-CP Gumel.

Mun gano wasu na kokarin tayar da tarzoma a kano-CP Gumel.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano wani shiri na tayar da tarzo ma a jihar kan rikicin masarauta.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano,CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a daren Litinin .

Gumel ya ce gwamnatin jihar ta na kokarin daidaita batun masarauta kuma duk wani rashin jituwa ana sa ran za a warware shi a kotu ga duk wanda yake da korafi.

Yace mu a matsayinmu na jami’an tsaro muna tsayawa kan doka kuma za mu aiwatar da ita.

Ya kara da cewa sun samu sahihan bayanai game da bata gari da ke kokarin tayar da tarzoma a wurare, musamman Majalisar Dokoki da sauran muhimman wurare a cikin Jihar, majiyoyi da yawa sun tabbatar da hakan.

Duk wanda ke son ta da tarzoma, jami’an tsaro suna da karfin da za su iya dashi. Mun kammala shirye-shiryen fara sintiri sossai da gano wuraren da aka sanar da mu cewa miyagun na wajen.