Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 436

Jami’an DSS sun musanta kutsawa fadar Sarkin Kano

 Jami’an DSS sun musanta kutsawa fadar Sarkin Kano 

Hukumar tsaron DSS ta musanta mamaye fadar Sarkin Kano, kamar yadda daraktan hukumar a Kano Muhammad Alhassan ya shaida wa manema labarai.

Muhammad Alhassan ya ce sun aike da jami’ansu ne don tarbar uwargidan shugaban kasa Sanata Oluremu Tinubu da za ta ziyarci fadar.

Amma dai ya ce tuni sun janye jami’an nasu biyo bayan samun labarin cewa an dage zuwan uwargidan shugaban kasar, bayan samun labarin cewa Sarkin ba ya gari.

Zan ci gaba da tsayawa takarar shugaban kasa,muddin Ina raye-Atiku Abubakar

 Zan ci gaba da tsayawa takarar shugaban kasa,muddin Ina raye-Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya sha alwashin ci gaba da tsayawa takara muddin yana cikin koshin lafiya.

Atiku ya bayyana haka ne lokacin da yake hira da sashen hausa na Muryar Amurka a Abuja.

Da yake tsokaci kan rikicin da ke faruwa a jam’iyyarsa ta PDP, ya ce akwai bukatar jam’iyyar ta hada kai tare da kulla kawance da sauran kungiyoyin siyasa domin lashe zaben shugaban kasa a 2027 mai zuwa.

A cikin hirar ta sa Atiku ya ce: tabbas zai ci gaba da tsayawa takara muddin yana da rai da lafiya.

Yace ko da tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln ya yi takara sau bakwai kafin daga bisani ya yi nasara.

To sai dai idan aka yi la’akari da halin da jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu, a bayyane yake cewa yunkurin hannu daya ba zai wadatar ba wajen lashe zaben. Ana buƙatar goyon baya mai ƙarfi da haɗin gwiwa tare da sauran jam’iyyu.

Majalisar dokokin jihar kano ta amince da dokar soke karin Masarautu guda 4 a jihar

Majalisar dokokin jihar kano ta amince da dokar soke karin Masarautu guda 4 a jihar.

Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da dokar majalisar masarautu ta Kano ta shekarar 2024 bayan kammala karatu na uku.

Dokar ta soke kafa sabbin masarautu guda 4 a jihar.

Dokar ta ce duk ofisoshin da aka kafa a karkashin dokar da aka soke, sabuwar dokar ta rushe su.

Haka zalika duk hakimai da aka karawa matsayi ko aka nada a karkashin dokar da aka soke za su koma kan mukamansu na baya.

Shugaban masu rinjaye kuma memba mai wakiltar mazabar Dala, Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ne ya gabatar da kudirin gyaran sabuwar dokar a gaban zauren majalisar dokokin jihar Kano

Jihar Zamfara za ta fara biyan mafi karancin llbashi N30,000 a watan yuni.

 Jihar Zamfara za ta fara biyan mafi karancin llbashi N30,000 a watan yuni.

Gwamnan jihar zamfara Dauda Lawal ya ce a watan yuni za a fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikatan jihar.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugabannin kungiyar kwadago reshen jihar Zamfara a Gusau.

Gwamnan yace aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 da nufin zaburar da ma’aikatan jihar da kara musu karfin gwiwa.

Ya bayyana wasu tsare-tsare daban-daban da gwamnati ta yi na inganta jin dadin ma’aikata, da suka hada da biyan albashin watanni uku da ba a basu ba, tallafin hutu, da sauran alawus-alawus.

Jami’an tsaron Nijeriya sun kubutar da ‘ya’yan da majalisar Zamfara da aka sace bayan watanni 17.

Jami’an tsaron Nijeriya sun kubutar da ‘ya’yan da majalisar Zamfara da aka sace bayan watanni 17.

Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) da ‘yan sanda sun ceto ‘ya’yan dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Aminu Ardo bayan shafe watanni 17 a hannunsu.

Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Isuku Victor, a lokacin da yake mika ‘yan matan ga mahaifinsu, ya ce, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya dauki nauyin ceto ‘yan matan, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro.

A watan Nuwambar shekarar 2022,ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki gidan Aminu Ardo da ke Jangebe, Jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da matarsa da ‘ya’yansa guda hudu.

Mahaifiyar da wasu yaran biyu sun yi nasarar tserewa a lokacin da aka yi garkuwa da su, inda suka bar Maryam da Nana Asma’u tare da wadanda suka yi garkuwa da su.

Tinubu ya nada Shehu Mohammed a matsayin shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa Road Safety

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya amince da nadin Shehu Mohammed a matsayin shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa Road Safety.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin tarayya George Akume, ta ce an amince da nadin Shehu ne bisa kundin tsarin mulki a sashe na 7 karamin sashe na 1 na doka ta 2007 da ta kafa hukumar.
Wannan nadi ya fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Mayu, 2024 kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Za a fara jigilar maniyyatan jihar Kano ranar Juma’a mai zuwa

Babban darakta a Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Baba Danbappa, ya ce za a fara jigilar maniyyatan jihar ranar Juma’a 24 ga watan Mayu, 2024.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka naɗa mataimakin Gwamnan jihar Kano, Commarade Aminu Abdussalam Gearzo a matsayin Amirul Hajj.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan yayin wani shiri na aikin hajji da aka gudanar a sansanin Alhazai yau Litinin.

NLC, TUC sun ba da wa’adin mako biyu ga jihohin da basa biyan mafi ƙarancin albashi

Kungiyoyin kwadagon da suka hada da NLC da TUC sun umarci sassan jihohin kasar da su bayar da wa’adin makonni biyu ga jihohi da su aiwatar da tsohon tsari mafi karancin albashi na N30,000.

Kungiyoyin sun dauki wannan matakin ne yayin wani taron majalisar zartarwa ta kasa da suka gudanar a ranar Litinin.

Sarki Salman na Saudiyya ya kamu da cutar Hunhu

Sarkin Saudiyya Salman ya kamu da cutar hunhu, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
An yi wa sarkin mai shekaru 88 magani kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya ruwaito.
Sarki Salman na fama da rashin lafiya tun bayan hawansa karagar mulki alokacin yana da shekaru 79 a duniya.

Kotu ta ki amincewa da bukatar Tukur Mamu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da bukatar Tukur Mamu, ta neman a dauke shi daga hannun Hukumar DSS zuwa gidan gyaran hali na Kuje.

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Inyang Ekwo, ya yi watsi da bukatar Mamu saboda rashin tsaro a gidan yarin.

Mai shari’a Ekwo, ya jaddada umarnin da ya bayar tun farko cewa a bar Tukur Mamu ya samu damar zuwa wurin likitansa domin jinya bisa kulawar jami’an lafiyan DSS.