Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 437

Muhimman bayanai kan shugaban kasar Iran, Marigayi Raisi

 

An nada mataimakin shugaban kasa Mohammad Mokhber a matsayin shugaban riko na Iran bayan tabbatar da mutuwar Shugaba Raisi a hatsarin jirgin sama

Dan shekaru 63, Ibrahim Raisi ya mutu ne a yayin da ake tsaka da yaki tsakanin Isra’ila da Falasdinawa da gwamnatin Raisin ta Iran ke goya wa baya.  Ya shafe kusan shekaru uku yana shugabancin kasar, kuma ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa.

Tsohon babban alkalin alkalan kasar ne.  Raisi ne ya maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei, shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci a Iran mai shekaru 85.

An haifi Raisi ne a garin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, cibiyar addini ta mabiya Mazhabar Shi’a. Ya yi karatun addini kuma ya samu horo a makarantar hauza da ke birnin Qum, inda ya yi karatu a gaban manya-manyan malamai ciki har da Khamenei.

Haka nan kamar Ayatollah, shi ma Raisi na amfani da bakin yadi domin yin rawani, wanda ke nuna cewa shi sayyidi ne – zuriyar Annabi Muhammadu, matsayi mai mahimmanci a tsakanin musulmi.

Raisi ya samu gogewa a matsayinsa na mai gabatar da kara a yankuna da dama kafin ya zo Tehran a shekara ta 1985. A babban birnin kasar ne a cewar kungiyoyin kare hakkin bil’adama, ya kasance cikin kwamitin alkalai da ke kula da zartas da hukuncin kisa kan fursunonin siyasa, abin da ya sa wasu suka yi masa da lakabi da Mahaucin Iran.

Marigayi shugaban kasar na Iran ya dade yana cikin majalisar kwararru, hukumar da ke da alhakin zabar wanda zai maye gurbin shugaban kasa idan ya rasu.

Raisi ya zama shugaban kasar Iran a shekara ta 2021 a cikin karancin fitowar masu jefa kuri’a da kuma rashin cancantar ‘yan takara masu neman sauyi da masu matsakaicin ra’ayi, kuma da alama ya samu kwakkwarar madogara ta sake zabe.

Kamar sauran manyan jami’an Iran, mafi munin kalamansa ya kebanta ga Isra’ila da Amurka, sai kuma kawayensu turawan Yamma.

Raisi ya yi jawabai da dama tun bayan fara yakin Gaza a watan Oktoba domin yin Allah wadai da kisan kare dangi da Isra’ila ke yi kan Falasdinawa, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su shiga tsakani.

Ya yi alkawarin daukar fansa kan Isra’ila bayan da ta yi wa ginin ofishin jakadancin Teheran da ke kasar Siriya hari tare da kashe ‘yan kungiyar kare juyin juya halin Musulunci IRGC guda bakwai, ciki har da janar-janar guda biyu na soja.

Zaman makoki da jimami ake cigaba da yi a kasar Iran da wasu karin kasashen Musulmi bayan sanarwar da hukumomi suka fitar cewa Shugaban kasar Ebrahim Raisi ya mutu a wani jirgin sama mai saukar ungulu wato helikwafta dauke da shi da wasu jami’ai bayan da jirgin ya yi hadari a wani yanki mai tsaunuka da dazuzzukan kasar.

Hatsarin dai ya faru ne kamar yadda hukumominn kasar suka sanar ta dalilin rashin kyawun yanayi.

Ma’aikatan NiMet sun dakatar da yajin aikin da suka shirya shiga

kungiyoyin kwadago na hukumar hasashen yanayi ta Najeriya sun dakatar da yajin aikin da suka shirya shiga yau Litinin, 20 ga Mayu, 2024.

Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a jiya Lahadi a wani zama na musamman da kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama da fasaha na majalisar wakilai tayi.

Yajin aikin dai na da nasaba da rashin cika masu alkawurra da gwamnati ta dauka.

Tsananin zafi ya yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla 200 a jihar Adamawa cikin makonni biyu

Akalla mutane 200 suka riga mu gidan gaskiya a lokacin da ake fama da matsanancin zafi a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wannan lamarin ya faru ne daga daya zuwa 13 ga wannan wata na Mayu.
Mazauna birnin da suka yi wa majiyar ta DCL Hausa karin haske, sun ce dumamar yanayi da tsananin zafn bazara da suka hadu ne ya sa aka samu kusan maki 47-50 da masana suka na da matukar hatsari.

Ba ma’aikacin da zai iya rayuwa da albashin kasa da N100,000 a Nijeriya – Shehu Sani

Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bukaci gwamnatin Nijeriya da ta kawo karshen maganar mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati, inda ya yi nuni da cewa babu wani ma’aikacin da zai iya rayuwa a kasa da albashin N100,000 a wannan marrar rayuwar da ake ciki.
Sanata Shehu Sani na magana ne kan wa-ka-ci-wa-ka-tashin da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta NLC kan batun mafi karancin albashi ga ma’aikatan Nijeriya a tashar talabijin ta Arise.
Tsohon dan majalisar ya ce gwamnatin tarayya na da kudin da za ta iya biyan abin da ya dace ga ma’aikatan kasar, inda ya ce tsarin biyan kudin wadatacci da za su ishi ma’aikaci da gwamnati ke shirin yi, abu ne mai kyau.

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin karkatar da kudin ‘yan fansho zuwa wani fanni.

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin karkatar da kudin ‘yan fansho zuwa wani fanni.

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin da ake cewa tana shirin karbar bashin N20tn na fansho domin bunkasa ababen more rayuwa.

Ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin Nijeriya Wale Edun, ya ce gwamnati za ta bi ka’idojin da aka kafa na asusun fansho domin yin abinda ya dace.

An ruwaito cewa ministan ya shaidawa manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na kwanaki biyu a fadar shugaban kasa a ranar Talata cewa, gwamnati za ta bayyana shirin yin amfani da kudaden kananan hukumomi da suka hada da asusun don samar da ababen more rayuwa.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis, Edun ya bayyana cewa,harkar fensho, tana da kayyadaddun tsarin doka ta musamman wajen tafiyar da ita.

An janye dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara Tukur Dan Fulani.

An janye dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara Tukur Dan Fulani.

Shugabannin jam’iyyar APC na unguwar Galadima da ke Gusau a jihar zamfara sun janye dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Dafulani.

Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, shugaban jam’iyyar na Unguwar  Galadima, Alhaji Sani Ibrahim, ya ce an janye dakatarwar ne bayan wani taron sulhu da aka yi da wasu ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya ce wasu ’ya’yan Unguwar da suka shiga cikin dakatar da shugaban jam’iyyar, sun shiga ciki ne domin kawo rudani a jam’iyyar.

Haza zalika, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Gusau, Abubakar Tijjani Dan’Aya, ya yabawa mambobin jam’iyyar da suka koka tare da kawo daidaito kan janye dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar.

Tinubu ya amince da biyan bashin kudin wutar lantarki N3.3tn.

Tinubu ya amince da biyan bashin kudin wutar lantarki N3.3tn.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da biyan basussukan da ake bin bangaren wutar lantarki a hankali a kan Naira N3.3tn.

Gwamnatin tarayya ta ce hakan na daga cikin matakan da za ta dauka na shawo kan matsalar rashin wutar lantarki a fadin kasar.

Haka zalika, kimanin N1.3tn da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki da kuma gwamnatin tarayyar za ta biya ne ta hanyar tsabar kudin da ta ayyana.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta fara biyan kudaden kashi na bashin N1.3tn da ake bin ta sannan ta kammala shirin biyan kashi na biyu ta hanyar takardar sheda a cikin wa’adin shekaru biyu zuwa biyar masu zuwa.

Shin me ke kunshe a cikin farashin abinci na wannan makon?

Manoman masara na ci gaba da darawa ganin yadda take daraja a kasuwa, domin kuwa a wannan makon an sayar da buhunta mai cin tiya 40 kan kudi Naira N70,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos da ke kudancin Nijeriya, a makon jiya aka sayar kan kudi N67,000, cikin kwanaki bakwai ta kara Naira dubu uku kenan. 
Amma a abin zas-sauki a jihar Adamawa, inda ake saidawa kan kudi Naira 52,000, amma a makon jiya an sayar da buhun masarar mai cin tiya 40 aka sayar kan kudi Naira N56-58, wato dai a wannan makon an samu saukin kusan Naira N4,000-6,000.
Can kuwa kasuwar Dawanau jihar Kano, Naira dubu N65,000 ake sayar da buhun masarar a wannan makon, a yayin da kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayarwa kan kudi N62,000, sai dai a makon jiya an sayar da masarar N59,000, ta kara N3,000. Sai a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ake sayar da buhun masarar mai cin tiya 40 kan kudi Naira N67,000 a yayin da a makon jiya aka sayar da masarar a Mai’adua jihar Katsina N64,000.
Ta bangaren shinkafar waje kuwa, a makon jiya an sayar da ita kan kuɗi N71,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, amma a wannan makon ta kara N7000 wato yanzu ta koma N78,000. A kasuwar Dawanau jihar Kano kuwa shinkafar baturen ta kama N80,000 daidai a wannan makon, amma a makon jiya an sayar kan kudi Naira N75,000, ta kara Naira dubu N5000 kenan. 
A kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuwa a makon jiya, an sayar da shinkafar wajen N68-69,000, amma a wannan makon ake sayarwa kan kudi Naira 73,500, nan din ma dai ta kara kudi.
Ita kuwa shinkafar ‘yar Hausa da aka fi sani da Jamila, N130,000 buhunta yake a kasuwannin Mile 12 International Market Lagos da Dawanau jihar Kano da Kasuwar Gombi jihar Adamawa a wannan makon, sai dai a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ana sayarwa kan kudi Naira N125,000, a yayin da kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayar da buhun jamilar N128,000 duk a wannan makon.
Amma a makon jiya, an sayar da buhun shinkafar Hausa din kan kudi Naira N142,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, sauran kasuwannin kuwa, yadda aka sayar makon jiya, haka aka sayar wannan makon.
Ta bangaren masu kosai da alale kuwa, ana sayar da buhunsa a kasuwar Mile 12 International Market Lagos kan kudi Niara N135,000 a wannan makon, N125,000 kuwa a kasuwar Dawanau jihar Kano, sai ake sayar da buhun waken kan kudi Naira 130,000 a kasuwar Gombi jihar Adamawa. Ita kuwa kasuwar Mai’adua jihar Katsina na sayar da buhun waken N112,000, kasuwar Giwa jihar Kaduna kuwa ake sayar da buhun wake farin da ake garo-garo, kosai, da alale kan kudi N110,000. Amma a makon jiya an sayar da buhun wake farin kan kudi N130,000, kasuwar Dawanau jihar Kano kuwa aka sayar a makon jiya kan kudi N113,000-120,000, sai a kasuwar Mai’adua jihar aka sayar da wajen kan kudi N117,000.
Ta fuskar taliyar Spaghetti kuwa a makon jiya, an sayar da ita kan kuɗi N14,500, aka sayar N14,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna sai aka sayar N13,500 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, a Dawanau jihar kuwa a makon jiya an sayar da kwalin taliyar N13,000. Amma a wannan makon an sayar da katan din taliyar kan kudi Naira 14,000 a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, a kasuwar Dawanau jihar Kano kuwa ana sayarwa kan kudi N15,500, sai kasuwar Gombi jihar Adamawa ake sayar da taliyar kan kudi N12,800. N16,000 ake sayar da katan din taliyar Spaghetti a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan makon, amma a kasuwar Giwa jihar Kaduna ana sayarwa a kan kudi Naira 14,000 cif-cif.
DCL Hausa
Abdullahi Garba Jani

Bai halatta gwamnati ta yi amfani da kuɗin fansho Naira tiriliyan 20 ba – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takara na babbar jami’ya mai adawa PDP Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaba Tinubu da yunkurin sake tafka wani almundahana ta anfani da Naira tiriliyan 20 na Fansho ta yi wasu ayyuka na daban.

Atiku ya ce wannan yunkuri na gwamnatin Tinubu abu ne mai matuƙar hadari, wadda kan iya haifar da matsanancin yanayi ga  ‘yan Najeriya waɗanda suka daɗe suna tãra kuɗin su na fansho domin su dogara da shi bayan yin ritaya daga aiki.

Atiku Abubakar ya ce maimakon yin hakan, kamata yayi gwamnatin ta Tinubu ta nemo masu saka jari dan gudanar ayyukan samar da kayakin more rayuwa da take ƙokarin yin amfani da kuɗin ‘yan fansho wurin aiwatar da su.

Gwamnatin taraiya ta bakin ministan tattalin arziki da na kudi ta sanar da wani sabon tsari na amfani da kuɗaɗen fansho da wasu kuɗaɗe wurin samar da kayan more rayuwa a Najeriya.

‘Yan siyasa suna raba kuɗin da suka sãta da ‘yan ƙasar.

Babban mai tsawatar wa na majalisar Dattawan Najeriya sanata Ali Ndume yayi zagin cewa ‘yan Najeriya ne ke tunzura ‘yan siyasar ƙasar yin almundahana da kuɗin ƙasar, saboda haka bai kamata su fuskanci wani hukunci ba.

Sanata Ndume ya nuna cewa idan aka kwatanta almundahana da ‘yan siyasa ke yi bai yi kusa da na wasu ba, yana mai cewa idan ‘yan siyasa basu raba kuɗi ba TOH tabbas baza su sake komawa kujerar da su ke riƙe da ita ba.

Ndume ya baiyana cewa idan ma za’a yanke hukuncin kisa ga masu laifin satar kuɗin gwamnati, bai kamata ace an kashe wanda ya saci Naira miliyan daya ko biliyan ɗaya ba, Wanda kamata a kashe shi ne wanda aka samu da laifin satar kuɗin gwamnati da ya kai Naira tiriliyan ɗaya.

Sanatan ya goyi bayan hukuncin kisa kuma ga masu safarar miyagun kwayoyi wadanda a cewar sa su suka fi cancanta da hukuncin kisa.