Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 439

An dakatar da shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara Tukur Danfulani

Shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Galadima a karamar hukumar Gusau jihar Zamfara sun sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar Tukur Danfulani.

16 daga cikin 27 na jiga-jigan jam’iyyar a mazabar ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwar, inda suka alakanta hakan da rashin shugabanci nagari da suke zargin shi Danfulani da yi.

Sannan su na zarginsa da haddasa rudani da rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar

Mu tunkari matsalolin mu kada mubari sufi karfin mu-sarkin musulmi

Mu tunkari matsalolin mu kada mubari sufi karfin mu-sarkin musulmi

Maimartaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su amince da kalubalen da suke fuskanta, su kuma yi kokarin magance su.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake karbar bakuncin ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar a fadarsa a ranar Juma’a, sarkin yace bai kamata mubari wasu suyi nasara a kan mu ba,domin idan babu tsaro, ba za mu iya samun komai ba.

Ya ce ministan tsaro ya san nauyin da Allah ya dora masa,kuma ya yi imanin yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki don taimaka masa wajen yaki da matsalar tsaro a fadin kasar nan.

Akwai kalu bale, amma masu ruwa da tsaki koda yaushe suna tuntubar juna domin samun mafita a al’amura da dama da suka shafi harkokin tsaro.

Sarkin Musulmi ya bada tabbacin cewa sarakunan gargajiya za su yi duk mai yiwuwa don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Sai dai ya yi kira da a ci gaba da tallafa wa jami’an tsaron da su ka sadaukar da rayuwarsu domin zaman lafiya a kasar nan.

Cutar kyanda tayi sanadiyyar mutuwar su yara 49 a jihar Adamawa.

Cutar kyanda tayi sanadiyyar mutuwar su yara 49 a jihar Adamawa.

Adadin wadanda suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar kyanda a jihar Adamawa ya kai 49.

Hakan ya fito ne a daidai lokacin da jami’an gwamnatin jihar ke bayar da bayanai kan kokarin dakile cutar yayin da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi jawabi ga manema labarai a birnin Yola kan ka’idojin bayar da rahoto na gaskiya kan cutar.

A yayin taron wayar da kai na WHO a ofishin ta na Yola, masanin cutar kanjamau na jihar Adamawa, Kadabiyu Jones, ya ce kawo yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 49, yayin da 143 daga cikin 818 da ake zargin sun kamu da cutar kyanda ya tabbatar da sun kamu da cutar.

Ya ce wadanda abin ya shafa yara ne da ke tsakanin shekara 1 zuwa 14, kuma yawancinsu ba a taba yi musu allurar riga-kafi ba.

Ya tabbatar da cewa jihar ta tura jami’an sa ido domin gano bullar cutar kuma tana aiki tukuru don ganin kawo karshen kamuwa da cutar ta hanyar rigakafin da ake yi.

Majalisar Dattawan Nijeriya za tayi doka kan albashin jami’an shari’ar a kasar.

Majalisar Dattawan Nijeriya za tayi doka kan daidaita albashin jami’an shari’a na tarayya da na jihohi.

Majalisar dattijai ta yi zaman karatu na biyu, kan kudirin dokar da za ta tsara albashi, da alawus-alawus da na ma’aikatan shari’a a Nijeriya.

Kudurin wanda dan majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya gabatar, wanda yasamu  karatu na biyu biyo bayan muhawarar da sanatocin suka gabatar a zauren majalisar.

A yayin muhawarar , Bamidele ya bayyana cewa, kudirin doka ce ta zartarwa, wanda shugaba Bola Tinubu ya mikawa majalisun tarayyar guda biyu, bisa tanadin sashe na 58 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka gyara.

A cewar sa, daya daga cikin kudirorin dokar shine hada kan tsarin albashi da alawus-alawus na masu rike da mukaman shari’a a matakin tarayya da jihohi.

Mai karamin karfi a Nijeriya na bukatar sama da Naira 615,000 mafi ƙarancin albashi – Joe Ajaero

 Mai karamin karfi a Nijeriya na bukatar sama da Naira 615,000 mafi ƙarancin albashi – shugaban NLC Joe Ajaero

Kungiyar kwadago ta tabbatar da kudirin ta na biyan N615,000 mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar.

Shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Joe Ajaero ya bayyana haka a jiya a ziyarar da ya kai hedikwatar kungiyar da ke Legas.

 

 Ajearo ya samu rakiyar wasu daga cikin  jami’an majalisar kungiyar ta jihar zuwa helkwatar kungiyar a birnin Legas, wadan da suka hada da shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE), Ambali Akeem Olatunji; Shugaban NLC na jihar Legas Funmi Sessi da kuma amintaccen NLC na kasa, Akporeha Williams.

Tawagar ta samu tarba daga manyan jiga-jigan editoci karkashin jagorancin Manajan Darakta/Babban Editan Victor Ifijeh.

Ajaero ya duk da cewa kungiyar kwadago ba ta adawa da batun biyan albashin ma’aikata da aka yi sulhu, amma tattalin arzikin da ke kan gaba ya sanar da matakin da ta dauka na gabatar da shawarwarin neman albashin N615,000 ga kwamitin sassa uku na gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashi.

Yace al’ummar kasar nan na fama da wahalhalu da dama hakan yasa akwai bukatar ma’aikata susamu albashin da zai rage wahalhalu da ake ciki.

Babu dalilin da zai sa Nijeriya ta dogara da shigo da abinci daga wasu kashashe-Inuwa Yahya

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce da yawan filayen noma da yawan al’umma, Nijeriya ba ta da dalilin dogaro da shigo da abinci daga kasashen waje.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wajen kaddamar da wani kamfanin taki da sinadarai a jihar.

Gwamnan wanda ya bayyana kudurin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa harkar noma a jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan  Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce,  za su ci gaba da bunkasa harkar noma a Gombe ta hanyar tallafa wa wadannan masana’antu.

Yace gwamnatin su ta himmatu 100% don bunkasa noma, babbar ma’aikata ta jiha da kasa. Kuma tun lokacin da m su ka hau kan karagar mulki a shekarar 2019, samar da abinci ya zama babban abin da ya fi mayar da hankali a gare su.

Babu dalilin da zai sa Nijeriya ta dogara da shigo da abinci daga wasu kasashe dole a jajirce wajen noma abinda za aci a kasa.

Majalissar wakilai ta Nijeriya ta umurci babban bankin kasar CBN da ya janye batun cajin kaso biyar a hahadar tura kudade a bankunan kasar nan

 Majalissar wakilai ta Nijeriya ta umurci babban bankin kasar CBN da ya janye batun cajin kaso biyar a hahadar tura kudade a bankunan kasar nan.

Majalisar wakilai ta umarci babban bankin Nijeriya (CBN) da ya janye takardar da ta umarci bankunan kasuwanci da su fara cire harajin da ake sakawa ta yanar gizo kan duk wata hada-hadar kasuwanci da ‘yan Nijeriya ke yi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke nuna rashin jin dadinsu kan wannan harajin da kungiyoyin kwadago da kungiyoyin kwararru da dama na kasuwanci da kuma daidaikun mutane ke yi.

‘Yan majalisar sun ce babban bankin ya yi wa tanadin dokar mummunar fassara, don haka ya kamata a gaggauta sake fitar da wata takardar domin wannan bata dace ba kamar yadda doka ta tanada.

Harajin 0.5% akan duk ma’amala ta banki, bisa ga Sashe na 44 na Dokar Canza Laifukan Intanet, 2024, ana sa ran ‘yan kasuwa da masu kula da harkokin kasuwanci da Dokar don ba da gudummawar Tsaro ta Intanet ta Kasa, Asusun zai kasance a cikin CBN, kuma ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ne ke gudanar da shi.

‘Yan bindiga sunyi awon gaba da dalibai a jami’ar kimiyya da fasa a Kogi.

 ‘Yan bindiga sunyi awon gaba da dalibai a jami’ar kimiyya da fasa a Kogi.

A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindiga suka kai hari Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (CUSTEC), Osara, Okene a Kogi, suka yi awon gaba da wasu dalibai.

Wani shaidar gani da ido ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki jami’ar ne da misalin karfe 9:00 na dare. yayin da daliban ke karatun jarabawar da za su yi.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigan sun shigo ta cikin daji ne, suka shiga dakunan karatu uku, suka fara harbin iska.

Sun kama daliban a cikin zauren karatun, suka fara daukar su,makarantar ta shiga cikin rudani, yayin da daliban da suka firgita a wasu dakuna suka yi ta tururuwa, ta bangarori daban-daban a cikin makarantar.

A lokacin da jami’an tsaro na cikin gida da jami’an tsaro na yau da kullun da ke bakin kofar suka shigo  barayin, tuni suka yi nasarar sace wasu dalibai. Amma kokarin da jami’an su ka yi ya rage barnar da aka yi saboda maharan ba su wuce dakunan farko guda uku ba,

A cewar majiyar, daliban na shirye-shiryen jarabawar semester ta farko da ake sa ran za a fara a ranar Litinin 13 ga watan Mayu, lokacin da ‘yan bindigar suka far musu.

Kungiyar ƙwadago ta kudiri aniyar yin zanga-zanga ranar 12 ga watannan na Mayu idan ba’a janye batun karin kuɗin lantarki ba

 Kungiyar ƙwadago ta kudiri aniyar yin zanga-zanga ranar 12 ga watannan na Mayu idan ba’a janye batun karin kuɗin lantarki ba

Kungiyoyin kwadago a karkashin inuwar kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC da (TUC) sun rubuta wasikar zanga-zanga zuwa hedikwatar hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NERC.

Kungiyar, a cikin wasikar, wacce ke da hadin gwiwar shugaban kungiyar NLC, Comrade Joe Ajaero da shugaban TUC, Comrade Festus Osifo, hadi da sunayen sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ministan kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya! Ministan wutar lantarki na tarayya da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DISCOs), sun ba da wa’adin ranar 12 ga Mayu, 2024 cewa, NERC ta sauya daga maganar karin kudin wutar lantarki a Nijeriya.

Kungiyoyin biyu sun ba da misali da mawuyacin halin da karin kudin zai tura talakawa a matsayin dalilin kiran a koma baya.

Wasikar ta ce mun yi imanin cewa wannan matakin ba wai kawai abin zargi ba ne idan aka yi la’akari da matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu,

hakan yasa ba za mu zura ido ba, domin ana cin zarafin talakawa da ma’aikata irin wannan abin da ba za a amince da shi ba.

Wannan dalilin yasa muka rubuta wannan takardar domin ankarar da hukuma cewa muddin ba a janye wannan mataki ba,munshirya tsaf domin gabatar da wannan Zanga-zangar.

Kwastam za su tsaurara bincike don kamawa tare da hukunta wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar jami’insu a Katsina

Babban kwantrolan hukumar kwastam ta kasa Bashir Adewale Adeniyi ya yi fatar cewa za su yi duk mai yiwuwa don ganin kama tare da hukunta wadanda suka kashe jami’insu Auwal Haruna a jihar Katsina.
Bashir Adewale Adeniyi a lokacin da wata tawaga ta musamman ta ziyarci garin marigayin Kayawa na karamar hukumar Dutsi a jihar domin ziyarar ta’aziyya, ya ce ba za su yi kasa a guiwa ba wajen bin diddigi don gano wadanda suka yi wannan aika-aikar dom su ma su girbi abin da suka shuka.
Auwal Haruna dai, jami’in kwastam ya rasa ransa a lokacin da wasu gungun mutane da ake kyautata zaton ‘yan sumogal ne suka farmake shi a lokacin da ya ke bakin aiki a kauyen Gamjin Makaho kan titin Katsina zuwa Dankama a karamar hukumar Kaita ta jihar a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024.
Bashir Adewale da ya samu wakilcin babbar tawagar karkashin jagorancin kwantrolan hukumar kwastam mai kula da jihar Katsina, Muhammad Umar, ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan lamari, har ma ya tabbatar da cewa idan aka gano su, to kuwa sai sun girbi abin da suka shuka.
Tawagar bayan ta’aziyya ga iyaye da sauran al’ummar garin Kayawa, sai da suka ziyarci makabartar da aka binne Auwal Haruna, inda suka yi masa addu’o’i na neman Allah Ya gafarta masa.
Wannan tawagar da ta hada kwantrolan hukumar da ke kula da shiyyar ta 4 wato FOU Zone 4, da mai kula da simtirim kan iyakar kasa ta Joint Boarder Patrol Team, sun ziyarci Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, inda suka gabatar masa da ta’aziyyar babban kwantrolan hukumar na kasa bisa wannan rashi na ma’aikacinsu da suka yi. Kazalika, sun kuma ziyarci Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruq Umar a fadarsa, shi ma suka yi masa ta’aziyyar wannan rashi da aka yi ma Auwal Haruna da ya rasu a lokacin da ya ke kokarin kare martabar kasarsa.