Masara ta yi tsada a sassan jihar Lagos
Masara ta yi tsada a sassan jihar Lagos
Gwamnatin kasar Benin ta hana lodar danyen man Nijar a ƙasar
Shugaban kasar Bénin Patrice Talon ya tabbatar wa duniya da matakin sa na hana lodar danyen man Nijar daga tashar jirgin ruwan kasar sa zuwa kasuwannin duniya
Shugaba Talon ya kuma nuna takaicinsa kan hawa dokin naki da hukumomin mulkin sojan Nijar suka yi na kin bude iyakar su da Bénin domin kuwa duk kokarin sa na neman samo masalaha a tsakanin kasashen biyu ya citura domin kasa samun gamsasshiyar amsa daga hukumomin na birnin Yamai sakamakon cewa har da ministan harkokin wajen shi ya tura wa mahukuntan na Yamai amma shiru
To amma ya ce a shirye yake ko a yanzu idan mahukuntan na Yamai suka amince suka bude iyakar su ya bar jiragen da suka zo domin daukar danyen man su dauka don ya ce yana fatan daidaituwar al’amura a tsakanin kasashen biyu aminan juna kuma ‘yan uwan juna
Marigayi Umaru Musa Yar’adua: Shi ake so ko halinsa….?
‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi da makami da karin masu aikata laifuka daban-daban a Katsina
Tinubu zai dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki a Turai
Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa shugaba Tinubu da mukarrabansa za su dawo Najeriya daga Turai a gobe Laraba.
Mashawarci na musamman kan bayanai da dabaru ga shugaban kasar Bayo Onanuga ne ya sanar a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X yau Talata.
Indai za’a iya tunawa a ranar 22 ga Afrilu, Shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa kasar Netherlands a wata ziyarar aiki da yakai.
Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar tantance lafiya kafin aure
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiyar masu son yin aure.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar na nufin daga yanzu babu wani aure da za a ɗaura shi a Kano ba tare da gabatar da sakamakon gwajin lafiya ba.
Hakan na nufin rage yiwuwar haihuwar yara masu wasu matsalolin kiwon lafiya kamar sikila, cutar kanjamau da ciwon hanta.
Jihar Katsina na duba yiwuwar fara daukar mata a kwalejinta ta horar da kwallo
APC ta zargi Kwankwaso da yiwa Ganduje zagon kasa gabanin zaben 2027
![]() |
| Kwankwaso |
APC ta zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Engr. Rabiu Kwankwaso da kitsa zagon kasa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, gabanin zaben 2027.
Mai baiwa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a Farfesa Abdulkarim Kana ne ya yi wannan zargin yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.
Abdulkarim yace shugabannin jam’iyyar NNPP na jihar Kano ke shirya zanga-zangar neman tsige Ganduje daga mukaminsa.
SERAP ta ba wa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 ta janye harajin CBN na 0.5%
Ƙungiyar kare hakkokin tattalin arziki ya yi gargadi ga Gwamnatin Tarayya da ta janye harajin kashi 0.5 cikin 100 da babban bankin Nijeriya CBN ya umurci bankunan ‘yan kasuwa da su rika cire wani kason kudi daga kwastominsu don samar da tsaro ga harkokin intanet.
SERAP ta kuma yi barazanar daukar matakin shari’a a kan gwamnati idan har bata janye harajin cikin wa’adin sa’o’i 48 da ta bada.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a ranar Talata a shafinta na X, inda ta yi kira da a gaggauta janye lamarin.




%20(13).jpeg)
%20(12).jpeg)