Friday, April 10, 2026
Home Blog Page 441

CBN zai dinga cire kashi 0.5 cikin dari na kuɗaɗen da aka cire

Babban bankin Nijeriya CBN ya umurci bankunan ‘yan kasuwa da su rika cire wani kason kudi daga kwastominsu don samar da tsaro ga harkokin intanet.

CBN ya ba da sanarwar ne ta hannun daraktocin shi na sashen gudanar da biyan kuɗi, Chibuzor Efobi da Haruna Mustafa a ranar Litinin.

Sabuwar takun-saka ta kunno kai tsakanin kasashen Nijar da Bénin

Kasar Bénin ta sanar da toshe damar fitar da danyen man fetur din daga tashar jirgin ruwan ta zuwa kasuwannin duniya
Kafar yada labaran gidan radiyon France Internationale (Rfi) ne dai ya tabbatar da hakan 
A wata Aprilun da ya gabata nan ne dai hukumomin mulkin sojan Nijar din suka sanar da fara tura danyen man din kasar daga cibiyar sa ta Agadem zuwa tashar ruwan ta Seme ta hanyar bututun da aka gina da zummar fitar da danyen man Nijar din zuwa kasuwannin duniya da ya har ganga dubu 90 a ko wace rana
Sai dai wasu na ganin kasar ta Bénin ta dauki wannan mataki domin maidawa kura aniyarta sakamakon matakin Nijar na cigaba da kin bude iyakar ta da Bénin din duk kuwa da umarnin bude tasu bodar da Shugaba Patrice Talon ya bada tun bayan matakin kungiyar ECOWAS na cire wa kasar ta Nijar takunkumin da aka kakaba mata

Ci-gaban Nijeriya ne gaban Shugaba Tinubu, ba soki-burutsun Atiku Abubakar ba – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban Nijeriya ta yi martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar game da kalamansa da ya yi a ‘yan kwanakin nan.
A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan sadarwa da tsare-tsare ya fitar, ta ce dan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar PDP Atiku dama ya yi kaurin suna wajen kokarin bata suna da ba da bayanai masu rikitarwa don ya cimma wata manufa ta kashin kansa musamman don goga kashin kaji ga gwamnati mai ci.
Fadar shugaban kasar ta ce a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai na baya-bayan nan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da ya sha kaye ya yi kakkausar suka kan batutuwa da dama da ya kamata a gyara domin kada a yaudari jama’a wajen amincewa da karya a matsayin gaskiya.
Sanarwar ta ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi amannar cewa duk wani dan Nijeriya mai kishin kasa na hakika, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, ya kamata ya yi kokarin inganta hadin kan kasa da walwalar tattalin arzikin kasa, ba tare da nakasa hakikanin kokarin gwamnatin tarayya na karfafa zuba jari na cikin gida da waje ba.
Fadar shugaban kasar ta ce sabanin ikirarin na Atiku Abubakar, gwamnatin Shugaba Tinubu, a cikin shekara ta farko, ta samar da sama da Dala bilyan 20 a cikin tattalin arzikin ƙasar. Kazalika, yayin da shugaba Tinubu ke birnin New Delhi na kasar Indiya domin halartar taron kolin G20 a shekarar da ta gabata, shugabannin ‘yan kasuwar Indiya sun zuba sabbin jari na sama da Dala bilyan 14.
Sanarwar Bayo Onanuga ta ci gaba tana cewa a yayin ziyarar da Shugaba Tinubu ya yi a kwanan nan zuwa kasar Netherlands, Firayim Minista, Mark Rutte, ya ba da sanarwar saka sabon saka hannun jari na Dala milyan 250 na ‘yan kasuwar Holland a Nijeriya.
Kazalika, sanarwar ta ce bangarorin tattalin arziki daban-daban, musamman ta hanyar sadarwa, masana’antu, ma’adanai, mai da iskar gas, kasuwancin ta yanar guzo duk suna jawo sabbin hanyoyin zuba jari kai tsaye daga kasashen ketare.
Fadar shugaban Nijeriya ta ce ta ga abin mamaki ganin yadda Alhaji Atiku Abubakar zai iya zargin Shugaba Tinubu da rigima a kan ba da kwangilar gina babbar hanyar Lagos zuwa Calabar ga kamfanin Hitech Construction wanda ya ce mallakin gidan Chagoury ne saboda dan shugaban kasa, Seyi Tinubu, ya kasance cikin hukumar gudanarwar kamfanin, da ke garin Sagamu, jihar Ogun.
Sanarwar ta ce ya kamata ’yan Nijeriya, a yanzu, su saba da nuku-nuku irin na Atiku Abubakar a kan al’amuran kasa da dama. Sanarwar ta diga ayar tambaya, take cewa, shin ba abin mamaki ba ne a ce tsohon mataimakin shugaban kasar, mutumin da ya fito karara ya ce ya kafa kamfanin Intels Nigeria tare da wani dan kasuwa dan kasar Italiya a lokacin da ya ke aiki a Hukumar Kwastam ta Nijeriya, wanda hakan ya saba wa ka’idojin aikin gwamnati, a yanzu shi ne ke zargin wani?
Fadar shugaban kasa ta kara da cewa a lokacin da ya ke mataimakin Shugaban Nijeriya a tsakanin 1999-2007, ya ci gaba da huldar kasuwancinsa da Intels wanda ya yi manyan kwangiloli.
Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar din ta fito karara ta nuna cewa yana da kyau a bayyana a fili cewa Seyi Tinubu matashi ne dan shekara 38 wanda ke da ‘yancin yin kasuwanci a Nijeriya da kuma ko’ina a duniya bisa tsarin da doka ta tanadar. Kasancewar mahaifinsa a yanzu shi ne Shugaban Nijeriya bai hana Seyi ci gaba da harkokin kasuwanci na halal ba.

Ƴan bindiga sun hallaka mutane 24 Katsina

Malam Dikko Umar Raɗɗa 

Kimanin mutane 24 ne aka ce an hallaka tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a Unguwar Sarkin Noma da ke ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ‘yan bindigar sun kai farmaki a kauyuka hudu a wani mataki da ke nuni da ramuwar gayya kan farmakin da sojoji suka kai maboyar su.

Wadanda abin ya shafa yawancinsu ’yan banga ne wadanda rahotanni suka ce sun fito domin tunkarar maharan.

Wani jami’in tsaron yankin ya shaidawa Channels cewa, harin ya dauki kimanin sa’a guda ana fafatawa.

Ƴan bindigar sun kai farmakin ne a kauyukan Unguwar Sarkin Noma, Gangara, Tafi, da Kore a daren ranar Alhamis da misalin karfe 9:00 na dare.

‘Yan bindiga sun yi mummunan ta’adi a Dan Musa jihar Katsina

Wasu mahara da tsakar daren Lahadin wayewar Litinin din nan, sun farmaki kauyen Mai Dabino na karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka hallaka wani mutum daya tare da sassara karin mutum daya.
Lamarin ya faru da misalin karfe 2:30am na dare wayewar Litinin, kamar yadda majiyar DCL Hausa ta tabbatar.
Bayanai sun ce mutumin da ‘yan bindigar suka ji wa raunuka, sun sassare shi da wuka a idanu, da yanzu haka ana hanyar zuwa da shi Katsina don ceto ransa.
Kazalika, maharan sun kuma sace wata mata, inda suka nufi daji da ita da har lokacin hada wannan labarin ba a san halin da take ciki ba kuma ba su bugo waya don neman abin fansar ta ba.
Majiyar DCL Hausa ta ce maharan sun kuma barke wani shagon da ake cajin waya, inda suka saci wayoyi da cazoji da sauran kayan amfani a shagon.
Sannan kuma rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kori dabbobi a garin da har yanzu ba a iya tantance adadinsu ba.
Majiyar ta ce mutanen garin sun zaci cewa jami’an sa kan Community Watch Corps ne a lokacin da suka ji karar harbe-harben bindiga, sai daga bisani suka farga cewa ashe ‘yan bindiga ne.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin dai hukumomi ba su ce uffan ba game a da wannan lamari.
Kauyen Mai Dabino na daga cikin kauyukan karamar hukumar Danmusa da ke fama da matsalar tsaro, tare da kauyuka irinsu Dunya, Kaigar Malamai da sauransu.

Ana barazanar daina kai tumatir a kudancin Nijeriya daga arewa

Kungiyar dillalan tumatir da hadaddiyar kungiyar masu safarar kayan abinci da dabbobi ta Nijeriya, na barazanar daina kai tumatir a jihar Lagos. 

Hakan ya biyo bayan zargin wulakanta musu kaya da suka ce ana yi.
Alhaji Ahmad Alaramma, shugaban kungiyar dillalan tumatir din ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da suka kira a Zaria jihar Kaduna.
Ya ce lamarin da ya faru a kasuwar Oke-Odo a jihar Lagos ya jaza an lalata musu ‘kiret’ kusan 60,000 na tumatir, saukin ma, babu tumatir din a ciki.
Ya ce ana sayar da kowane ‘kiret’ daya na tumatir a kan kudi N6,000, da yanzu haka mambobin kungiyar sun yi asarar kudin da suka kai N360m.

Gwamnan kano ya nemi a gina makarantar soji ta mata a Kano.

Gwamna ya nemi a gina makarantar soji ta mata a Kano.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci a kafa makarantar sakandare ta ‘yan mata ta sojojin sama a Kano domin karawa akan makarantar sakandaren maza da ke Kwa, karamar hukumar Dawakin Tofa, a kan hanyar Kano zuwa Katsina.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar, Gwamna Abba ya yi wannan roko yayin ziyarar da shugaban hafsan sojin saman Nijeriya Air Vice Marshal Hassan Bala Abubakar ya kai gidan gwamnati a Kano.

Ya kuma nuna jin dadinsa a bisa kwarewa da kuma tarihin Air Marshal Abubakar, inda ya yaba da kokarin rundunar sojin saman kasar nan wajen magance kalubalen tsaro, musamman wajen yakar masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi, da sauran masu aikata laifuka a Kano.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tallafawa rundunar sojin sama da kuma ‘yan uwa jami’an tsaro, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan su wajen wanzar da zaman lafiya a Kano da kasa baki daya.

 A nasa jawabin Air Vice Marsha Hassan Abubakar, ya nuna damuwarsa kan yadda ake ci gaba da yankad filin jirgin saman NAF da matsugunin sa, inda ya bukaci a maido da filin da aka sadaukar domin fadadawa nan gaba.

Ya kuma nemi goyon bayan Gwamna Abba wajen hada cibiyar samar da ruwan sha ta jihar Kano da na matsugunin sojojin sama domin inganta samar da ruwan sha a Jihar.

Farashin abinci na kara ruda ‘yan Nijeriya

Farashin wasu kayan abinci na sauka na wasu na hawa a wasu kasuwannin sassan Nijeriya a daidai lokacin da al’umma da dama da ke faɗin ƙasar ke fama da karancin man fetur da rashin wutar lantarki da ma batun Dala da ya dabaibaye sassan rayuwa daban-daban.

A wannan makon masara ta fi tsada a Kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos da aka saida ₦65,000, yayin da a makon da ya gabata aka sayar ₦60,000 daidai, an samu karin ₦5000 a makon nan.
Sai kuma kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, inda a wannan makon aka sayi buhun Masarar ₦57-60,000, bayan da a makon jiya aka sayar ₦45-47,000.
A nan ma an samu karin kusan 13,000,a mako ɗaya kacal.
Ita ma dai Kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, ana sayar da Masara ₦57,000 a wannan makon da ke shirin karewa, amma a makon jiya ₦53,000 aka sai da buhun masarar.
To a kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuma ₦58,000 kuɗin buhun yake a makon da ya wuce, sai dai a makon nan kuɗin buhun ₦62,000 ne, an samu karin 4000, kenan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan mako.
Masara ta fi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe sama da sauran kasuwannin kasar a wannan makon, inda aka sai da buhun masara ₦55,000, sai dai makon jiya ₦50,000 kuɗin buhun yake a Kasuwar.
Haka nan a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma an samu karin 4000, kan farashin makon jiya da saida ₦54,000, amma a makon nan ₦58,000 kuɗin buhun yake a kasuwar.
Ita kuwa shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Kashere da ke karamar Hukumar Akko a jihar Gombe, da aka saida buhun ₦120-130,000, bayan da aka saya ₦105-115,000, a makon da ya wuce.
Amma a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa shinkafar Hausar ta ɗan sauka, an dai sai da buhun shinkafar ₦125,000 a makon jiya, yayin da a makon nan kuɗin buhun ya kama ₦120,000 cif, an samu ragowar ₦5000 kenan kan farashin na baya .
Shinkafar Hausar ta faɗi a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa da aka sai da ₦110,000, bayan da a makon jiya aka sayar ₦125,000.
Da DCL HAUSA ta leka kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos kuwa kuɗin buhun Shinkafar ‘yar gida ₦120,000 ne a wannan makon, yayin da a makon jiya aka sai da ₦125,000.
Hakazalika a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma ₦120,000 aka sai da buhun shinkafar a makon nan,sai dai a makon jiya ₦105,000 aka sai da buhun, hakan na nuni cewa shinkafar ta haura a makon nan.
To a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano an sayi shinkafar 113,000 a makon da ya gabata, amma a makon nan,₦118,000 aka sai da buhun, an samu karin ₦5000 kenan a makon nan da ke dab da ƙarewa.
Shinkafar waje kuwa ta fi sauki a wannan satin a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, da ake sayarwa ₦55,000, bayan da makon da ya gabata aka sai da ₦70,000 daidai.
A jihar Gombe da ke makwabtaka da jihar Adamawa, an sayi shinkafa ‘yar waje kan kuɗi ₦62-65,000
An samu karin ₦2000 kenan kan farashin makon da ya gabata da aka sai da ₦62-63,000.
₦65,000 ake sai da buhun shinkafar Bature a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a makon da ya shude, haka nan farashin bai sauya zani ba a wannan makon.
A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa, an sayi buhun Shinkafar waje ₦68,000 a makon da ya kare, amma makon nan ₦65,000 kuɗin buhun Shinkafar.
Sai dai fa a kasuwar Mai’adua kudin Buhun shinkafar Bature bai canza zani ba a satin nan,inda ake sai da buhun₦62,000 haka batun yake a wannan makon.
To bari mu kammala Farashin Shinkafar Baturen da Kasuwar Dawanau a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya,an sayi buhun Shinkafar waje ₦62,000 a makon jiya, sai dai a satin nan ₦71,000 aka sai da buhun, an samu karin kudi har ₦11,000 a mako guda kawai, wanda aka danganta hakan da tashin farashin CFA a kasar.
A bangaren Taliyar Spaghetti kuwa ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna, ina aka sayi kwalin taliyar ₦14,000 a kasuwar Dawanau a jihar Kano, hakan nan a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma ₦14,000 ne kuɗin Kwalin taliyar a makon nan,an samu karin dubu guda kenan kan farashin makon jiya a kasuwar giwa da ke jihar Kaduna, amma a kasuwar Dawanau kuwa₦13,500 ne ake sai da kwalin taliyar a makon jiya.
Kwalin taliyar ya fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da aka saya kan kuɗi ₦12,700 a makon nan,yayinda aka sayi kwalin ₦13,000 a makon daya shude,an samu sassaucin 300 kenan a kasuwar.
A Mai’adua jihar Katsina ₦13,700 ake saida kwalin taliyar a makon nan, amma a makon jiya ₦13,500 aka sai da, nan ma karin ₦200 kenan aka samu a satin nan.
Ita kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos ana sayar da kwalin taliyar ₦13,000 cif, bayan da a makon daya kare aka sayar ₦13,500.
A karshe sai kasuwar Kashere dake jihar Gombe, an sayi kwalin taliyar kan kuɗi ₦12,600 a makon nan, hakan batun yake a makon da ya kare.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.

‘Yan bindiga sun yi yunkurin kai harin ramuwar-gayya a Danmusa jihar Katsina

Wani rahoto da DCL Hausa ta samu na cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san adadinsu ba sun yi yunkurin shiga garin Danmusa, hedikwatar karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina cikin daren nan na Litinin.
Sai dai bayanai sun ce jami’an sun yi nasarar dakile wannan yunkuri hari da aka kira na ramuwar gayya. Yunkurin ‘yan bindigar ya biyo bayan wani aikin fatattakar ‘yan bindiga da jami’an tsaro aka sanar cewa sun yi a kauyen Katsira, inda bayanai suka ce jamian tsaro sun yi nasarar konawa tare da lalata mafakar ‘yam bindigar da dama.
Duk da dai a yayin samamen jami’an tsaron ba a ba da rahoton an kashe ko jikkata wasu ‘yan bindigar ba, amma wata majiya daga jami’an tsaro da ta nemi da kada a ambace ta, ta tabbatar da cewa an yi wa ‘yan bindigar barna mai yawa.
Hakan ne ma, kamar yadda majiyar ta sanar da DCL Hausa ya sa ‘yan bindigar suka yi zuga, da zummar ramuwar gayya a garin na Danmusa. Amma jami’an tsaro suka sake samun nasarar fatattakarsu.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin, mutanen garin na Danmusa dai sun firgita, da hakan ya sa har wasu suka fara tunanin ko ma ‘yan bindigar sun shiga garin, a lokacin da suka ji karar harbe-harben bindiga a bayan gari.

Tukur Mamu ya nemi a daukeshi daga hukumar DSS zuwa Kurkukun Kuje.

 Tukur Mamu ya nemi a daukeshi daga hukumar DSS zuwa Kurkukun Kuje.r

Wani wanda ake zargi da hannu cikin ayyukan bata gari a Nijeriya, Tukur Mamu,ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta dauke shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Ya roki mai shari’a Inyang Ekwo da ya sauya hukuncin daurin da aka yi masa na ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje maimakon tsareshi a hukumar DSS.

A ci gaba da shari’ar, Mamu ta bakin lauyansa, Abdul Mohammed, ya yi zargin cewa umurnin da kotu ta bayar a ranar 19 ga watan Disamba, 2023 na a ba shi damar zuwa wurin likitansa domin jinya, ba a bi umarnin kotun ba.

A cikin takardar bukatar da Mohammed ya gabatar, Mamu ya yi ikirarin cewa an ba shi damar ganawa da likitan sau daya inda aka mika rahoton cikakken binciken lafiyarsa ga hukumar ta DSS.

Tun bayan gabatar da rahoton, Mamu ya yi zargin cewa ba a ba wa likitan damar zuwa wurinsa ba, don haka yana bukatar a yi masa tiyata cikin gaggawa a duk wani asibiti da ke gundumar.