Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 442

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar daga N40,000 zuwa N70,000.

 Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar daga N40,000 zuwa N70,000.

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikata a jihar daga N40,000 zuwa N70,000.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da sabuwar katafaren sakatariyar ma’aikata da aka gina na kungiyoyin kwadago a jihar, a kan titin Temboga, Ikpoba-Hill, a cikin birnin Benin.

Ya kamata NAHCON ta fitar da lokacin fara jigilar mahajjatan Nijeriya zuwa kasar Saudiyya – IHR

Kungiyar nan mai zaman kanta da ke wayar da kan mutane game da aikin hajji mai suna International Hajj Reporters IHR ta bukaci hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON da ta gaggauta sanar da lokacin da za a fara jigilar mahajjatan bana zuwa kasar Saudiyya.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake kiyasin cewa bai wuce kwanaki 10 da za a fara jigilar mahajjatan zuwa kasar Saudiyya daga kasashen duniya da ke zuwa aikin hajjin a kasar.
Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar IHR na kasa Alhaji Ibrahim Muhammad da DCL Hausa ta samu kwafi da ke cewa kusan dukkanin kasashen da ke zuwa aikin hajji a kasar Saudiyya sun rigaya sun sanar da lokuttan da za a fara jigilar alhazansu zuwa can.
Sanarwar ta ce ya zama kamar al’ada ga hukumar ta NAHCON tana sanar da rana da jihar da za a fara kaddamar da jigilar mahajjatan.
“Abin bai yi mana dadi ba, ganin cewa kwanaki kalilan suka rage a fara jigilar mahajjatan da kuma rufe shafin ba da takardar izinin shiga kasa ta visa, amma hukumar NAHCON har yanzu ba ta sanar da ranar da za a fara jigilar mahajjatan Nijeriya ba”.
Alhaji Ibrahim Muhammad ya ce manyan kasashe 5 da suka fara sanar da lokacin daukar maniyyatan su ne kasar Indonesia da za a fara daukar maniyyatanta a ranar 12/05/2024. Sai kasashen Bangladesh da Pakistan da suka saka ranar 9/05/2024. Kasar Malaysia kuwa za ta fara jigilar mahajjatan a ranar 11/05/2024. Ghana kuwa ta saka ranar 18/05/2024.

Anyi zargin gwamnatin kano nada Hannu wajen zanga zangar da akeyi na nuna rashin amincewa da shugabancin Ganduje.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano ce ke daukar nauyin zanga-zangar da ake yi ta nuna sai ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyar  (NNPP) da ke jagorantar gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a zanga-zangar nuna adawa da shi a Abuja.

Sai dai gwamnatin jihar ta musanta cewa tana da hannu a rikicin.

An yi zanga-zangar neman a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, inda kungiyoyi da jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta tsakiya ke kan gaba.

Ganduje a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta hannun mataimakinsa na musamman kan kungiyoyin farar hula, Kwamared Okpokwu Ogenyi, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano na daukar nauyin masu zanga-zanga a tituna, galibi ‘yan Kwankwasiyya ne, wadanda wasu daga cikinsu sun fito ne daga yankin Arewa ta tsakiya. domin neman Ganduje yayi murabus.

Sanarwar ta kara da cewa, “Muna da sahihan bayanai cewa Gwamnatin kano na aiki tare da wasu daga shiyyar Arewa ta tsakiya tare da bayar da makudan kudade ga wasu mutane domin ci gaba da nuna rashin amincewa da shugabancin Ganduje wanda manufasu shine a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Mutane da yawa sun makale yayin da gini ya ruguje a Kano.

Mutane da yawa sun makale yayin da gini ya ruguje a Kano.

Yanzu haka dai wasu ma’aikata da ba a tantance adadinsu ba sun makale a wani gini da ya rufta a unguwar Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.

Wata majiya ta bayyana cewa, akalla mutane 11 ne suka makale a karkashin baraguzan ginin.

Jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) sun garzaya da wasu mutane biyu da aka ceto zuwa asibiti.

A halin yanzu ana ci gaba da tono wasu gawarwaki da

Har yanzu ba a tantance adadin su  ba.

‘Yan Bindiga sun hari garin Maradun na jihar Zamfara

‘Yan Bindiga sun kai hari garin Maradun na jihar Zamfara inda Sun halaka mutanen 2, tare da sace,mutum 30.
https://drive.google.com/uc?export=view&id=11jdk7ctr5oP_oQDsKoQGfyYolgZZsedX
Mazauna garin Maradun, mahaifar karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, sun shiga cikin zullumi yayin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin da safiyar Juma’a.
Rahotanni sun bayyana  cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin ne da misalin karfe 2:00 na dare kuma an kwashe kusan sa’o’i biyu ana harbe-harbe tare da lalata  gidajen mutane.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, duk da cewa har yanzu ba a tantance ainihin adadin mutanen da aka sace ba a lokacin harin, amma adadin ya kai kusan 30 da suka hada da mata da yara da manya idan aka yi la’akari da adadin gidajen da abin ya shafa.
Wani basaraken gargajiya da ‘yan fashin suka yi wa gidan sa kawanya ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda matsalar tsaro ke karuwa a garin.

Watanni 11 bayan da gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur ‘yan Nijeriya na ci gaba da kokawa kan halin da ake ciki na karancin man fetur da dogayen layukan da ake samu a gidajen mai a fadin kasar.

 Watanni 11 bayan cire tallafin man fetur ‘yan Nijeriya har yanzu na fuskantar karancin man fetur, tare da gama da dogayen layi.

Watanni 11 bayan da gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur ‘yan Nijeriya na ci gaba da kokawa kan halin da ake ciki na karancin man fetur da dogayen layukan da ake samu a gidajen mai a fadin kasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar man fetur suka yi ta zargin karancin man fetur da ake fama da shi a halin yanzu yayin da ake ci gaba da samun layukan man fetur a manyan biranen kasar nan duk da tabbacin da Kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL) ya bayar na cewa ana samar da man a kai a kai.

Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur gaba daya a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a lokacin rantsar da shi, kuma farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a fadin kasar nan.

Wannan cire tallafin man fetur ya kamata ya bude kofar shigo da mai zuwa kamfanoni masu zaman kansu a matsayin wani bangare na tanadi a cikin dokar masana’antar mai ta 2021, don haka ya dauki nauyin shigo da mai daga NNPCL.

Sai dai kuma NNPCPL ya kwashe watanni da dama ya kuma zama shi kadai ke shigo da mai a Nijeriya, saboda kamfanonin mai masu zaman kansu ba sa iya samun kudaden kasashen waje don shigo da su daga kasashen waje.

A baya dai hukumar NNPCPL ta sanar da cewa ba ita kadai ce ke samar da albarkatun man fetur a kasar ba, amma lamarin ya sauya sakamakon karancin man fetir.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da janye jami’an ta na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

 Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da janye jami’an ta na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano,ta tabbatar da janye jami’anta daga hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).

Rundunar ‘yan sandan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Abdulahi Haruna Kiyawa, ta ce janyewar jami’an ta na da nufin gudanar da bincike kan ma’aikatan da nufin gano ainihin adadin jami’an ‘yan sandan da hukumar ta amince da su tare da gano irin ayyukan da kowane dan sanda ke yi tun lokacin da aka tura shi hukumar a shekarar 2015.

Hakan ya biyo bayan rahotannin da aka samu ta sashin amsa korafe-korafe na rundunar ‘yan sanda (CRU), inda ke nuna ‘yan sandan da ke da alaka da hukumar a matsayin masu rike da madafun iko tare da kaucewa aikin da ake sa ran na samar da gadi da sauran ayyuka a hukumar.

Jama’a su lura cewa, abin da ake ci gaba da yi na ma’aikata shi ne magance yawan korafe-korafe kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito.

Daukar matakin ya zama wajibi, domin a gyara kura-kurai da ke fitowa fili a cikin ayyukan Hukumar kamar yadda aka fara amfani da Jami’an ‘yan sanda da aka tura zuwa gadi da sauran ayyuka wajen kamawa da gudanar da bincike a kan kararraki wanda a fili ya saba wa nasu na asali. wajabcin da aka sanya kuma dole ne a gyara.

Matakin shine tabbatar da ingancin aikin na ƴan sanda ba tare da cin zarafi don wani ko wata a cikin al’umma ba.

Jami’an tsaro a jihar Kebbi sun kama wasu bamabamai da ake ƙoƙarin shigo da su Nijeriya

 Jami’an tsaro a jihar Kebbi sun kama wasu bamabamai da ake ƙoƙarin shigo da su Najeriya sakaye a cikin buhuna da kwalaye.

Jami’an tsaron kan iyaka na Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya Kwastam (NCS) dana hukumar shige da fice ta Nijeriya, Ma’aikatar Harkokin waje da sojojin Nijeriya karkashin jagorancin babban Sufeton Kwastam, A.A. Ibrahim, wanda yanzu mataimakin kwanturola na hukumar Kwastam da ke kan titin Yauri-Jega a jihar Kebbi ya kama kwali 40 da buhuna dauke da ake zargin bama-bamai ne.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Kwanturolan hukumar kwastam na jihar, Iheanacho Ernest Ojike, ya ce bayan gwajin da jami’an hadin gwiwa suka gudanar, an gano kayayyakin da ake zargin dauke da kwalaye 40 da kuma buhuna guda 6,240 na bama-bamai waɗanda akai lodi a kan farar Canter/ babbar mota mai lamba Zur 882ZY tare da lambar babur Haejue JEG-562 UQ.

Kwanturolan ya ce an kama wasu mutane biyu da hukumar kwastam ta tsare su a Birnin Kebbi tare da mika kayayyakin da aka kama ga jami’an tsaro na jihar.

Masara ta fara komawa daidai aljihun talaka a Nijeriya

A wannan makon dai, Masara ta fi sauki a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa sama sauran kasuwannin Sassan kasar nan, inda ake sayar da buhun Masara N45-47,000, bayan da makon da ya gabata aka sayar akan kudi N55-57,000, an samu sauƙin N10,000 daidai a wannan makon.

Ita ma dai Kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuɗin Masarar ta kara sauka a satin nan, a makon da ya shude an sayar da buhun masarar kan kudi N62,000, yayin da a makon nan ake sayarwa kan kudi N54,000.
A kasuwar Kashere a jihar Gombe, an saida buhun masara N45-50,000 a Mako na biya kenan cikin watan Shawwal, Saɓanin na makon jiya da aka sai da N56-58,000 a kasuwar.
Hakazalika Farashin Buhun Masarar ya sake sauka makon nan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka sayar N58000, yayin da a makon da ya wuce aka sayar N60,000 an samu sassaucin N2000 kenan a kasuwar.
Ana dai ci gaba da samun rahusar kayan abinci a wannan makon, Inda ake sayar da buhun masara N60,000 cif a Kasuwar Mile 12 International Market dake Legos, bayan da makon da ya gabata aka sayar kan kuɗi N63,000.
A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, kudin buhun Masara a makon nan N,53,000 ake saidawa, yayin da a makon jiya aka sayar N55,000.
A bangaren Shinkafar Hausa kuwa, ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kaduna da Adamawa, inda ake sai da buhun N125,000 a kasuwannin, sai dai farashin buhun Shinkafar na makon da ya gabata ya sha banban a kasuwannin, an sai da buhun, N136,000 a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa a makon da ya shude, ita kuwa kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, N130,000 aka sai da a makon da ya gabata.
An sai da buhun Shinkafar Hausa N105-115,000 a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, Sai dai a makon jiya N120-130,000 ne kuɗin buhun Shinkafa a kasuwar.
Ita ma dai kasuwar Mile 12 International Market a jihar Legas farashin Buhun Shinkafar ya sake sauka a satin nan, ana sayar da Shinkafar Hausa N120,000, amma a makon da ya wuce N130,000 aka sayar an samu sauƙin N10,000 a makon nan.
Shinkafar Hausar ta fi sauki a makon nan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da aka sai da buhun N105,000, bayan da a makon da ya kare aka sayar N110,000
Nan ma an samu ragowar N5000 kenan a makon da ke shirin karewa.
Sai dai kuma Farashin buhun Shinkafa ‘yar gida ya ɗan tashi a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano da aka sai da buhun N113,000 a makon nan, yayin da a makon da ya shude aka saida N110,000 daidai.
To a bangaren Shinkafar Bature kuwa, ta fi tsada a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, inda ake sai da buhun kan kuɗi N70,000 a satin nan, sai dai fa duk da haka farashin ya fi sauki kan na makon jiya da aka sai da N78,000.
Haka nan Shinkafar Baturen N68,000 ake sayarwa a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, amma a makon da ya kare an sayar da buhun kan kuɗi N70,000 daidai a kasuwar, an samu sauƙin N2000 kenan a makon nan.
N62-63,000 ake sayar da buhun shinkafar waje a kasuwar Kashere da ke karamar Hukumar Akko na jihar Gombe, sai dai kuma N75,000 aka sayar da buhun a makon da ya shude, an samu canjin N12,000 kenan a mako ɗaya kacal a kasuwar.
Ita kuwa Kasuwar Dawanau da ke jihar Kano an samu karin N1000 guda kan farashin buhun Shinkafar na baya, da aka sai da N62,000, amma a makon nan an sayi buhun Shinkafar Bature N63,000.
Hakazalika a kasuwar Mai’adua jihar Katsina an samu kari a farashin shinkafar waje a makon nan da aka sayar N62,000, inda makon da ya wuce aka saida N58,000, an samu karin N4000 kenan.
To bari mu kammala Farashin Shinkafar Baturen da Kasuwar Mile 12 International Market dake Legos, an sayi buhun Shinkafar N65,000 a kasuwar, a wannan da ke dab da ƙarewa,bayan da a makon daya gabata aka sayar N63,000, hakan na nuni da cewa an samu karin N2000 kenan a wannan makon nan.
Ga ma’abota cin Taliya kuwa, Spaghettin ta fi tsada A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, inda ake sai da ko wani kwali na tafiyar N14,500 a makon da ya shude, Yayin da a makon nan aka sai da N14,000 daidai.
A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano,farashin kwalin a wannan makon N13,000 ne,sai dai a makon jiya N13,500 ne kuɗin Kwalin taliyar,
Kwalin Taliyar tafi sauki a kasuwar Kashere dake jihar Gombe a makon nan,da aka sayi kwalin N12,600,yayin da a makon daya gabata aka sayar N13,000 cif,an samu sauƙin N400 kenan a makon.
Bayan da DCL Hausa ta leka kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuwa,ta taras da cewa 
Farashin kwalin taliyar sake Hawa ya yi a kasuwar,inda a makon jiya aka sai da N12,000 daidai,sai dai a makon nan N13,500 ake sai da kwali guda na taliyar.
Ita kuwa kasuwar Zamani dake jihar Adamawa farashin kwalin taliyar bai sauya zani ba,inda a makon daya gabata ake saidawa kan kuɗi N13,000 daidai,haka nan aka sai da a makon dake yi mana bankwana.
To bari ƙarƙare farashin kayan abincin na wannan makon da farashin Taliya a kasuwar Mile 12 International Market Legos dake kudancin kasar,inda kuɗin kwalin ya kama N13,500, sai dai fa wannan makon an samu sauƙin N1000 guda kan farashin makon jiya da aka sai da N14,500.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.

Masu ruwa da tsaki a APC sun bukaci Ganduje ya yi murabus

 Masu ruwa da tsaki a APC na son Ganduje ya yi murabus

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC da suka fito daga shiyyar Arewa ta tsakiya sun rubutawa kwamitin ayyukan jam’iyyar na kasa (NWC) inda suka neman shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mohammed Mahmud Saba ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Inda tuni aka aika kwafin wasikar ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.