Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 443

Fatima Mai Zogale: Fikirar Rarara da ta yi kama da ta Shata

Watarana ina sauraren wata hira da aka yi da Marigayi Mamman Shata (ba zan iya tuna kafar yada laban ba) na ji yana cewa “idan wakar ta zo, zan yi, idan kuwa ba ta zo ba, ba ni iyawa” (ba hakikanin kalmomin da ya furta ba kenan, amma kusan sakon abin da ya ke nufi kenan). Bayan na saurari tsakuren sabuwar wakar mawaki Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara mai taken Fatima Mai Zogale, sai wadancan kalaman na Marigayi Shata suka dawo min a rai.
Na kara tabbatarwa cewa waka ga duk wanda Allah Ya ba ilhamarta, to tana zuwar masa ne a daidai lokacin da Allah Ya so, ba lokacin da shi mawakin ya ga dama ba. Kamar yadda Adam Zango ya furta a wata wakarsa cewa “…..Waka ai baiwa ce,
            In ka iya ta ko, ka dace,
        Don jahili, ba ya waka”……..
Wannan dan waka na Adamu, na nufin Allah ne ke ba bawanSa baiwar waka, ba kuma kowa ne mutum ne ke da irin wannan baiwa ba.
Na tuna lokacin da muna jami’a, muna karatun digiri na farko, malaminmu (Allah Ya kara masa lafiya) Prof Haruna Abdullahi Birniwa, ya ba mu aikin gida cewa kowa ya kawo masa baitukan rubutacciyar waka biyar, sabuwa, wadda ba a taba yin irinta ba, ma’ana kada a kwaikwayi wani ko wata a wakar, a cikin mako daya. Amma cikin mu (dalibai) kusan 30, babu wanda ya iya kawo wannan aikin gida yadda ya kamata, (wataqila saboda duk a cikinmu babu wanda Allah Ya hore wa baiwar waka).
A hirarrakin Marigayi Shata daban-daban da na samu damar saurara ko kalla, na sha jin yana fadin cewa wani mutum ko wasu gungun mutane sun so ya yi musu waka, wasu har kudi sun sha bashi, amma idan wakar ba ta zo ba zai yi ba. Har yana cewa wasu na ganin kamar girman kai ne ko wani abu makamancin haka, amma ba girman kai bane, wakar ce ba ta zo masa. Amma idan wakar ta zo, to ko me ya tarar, zai wake shi, ko min kankantar darajarsa kuwa. Misali, wakar Marigayi Shata ta Dajin Rugu, Hawwa Mai Tuwo Matar Lado, Sarki Bakwai Na Sabon Birni da sauransu.
Wani zai yi mamakin jin Dauda Kahutu Rarara ya yi wa Fati Fatima Mai Zogale waka, ba sabon abu bane idan duk muka yi duba da irin abubuwan da suka faru da magabata a waka irinsu Marigayi Shata. Ko Marigayi Salihu Jan Kidi na taba karantawa a wani wuri (ba ni iya tuna littafin) yana cewa akwai lokacin yana bacci zai ji wakar ta zo, sai yi furgigit ya tashi, ya rubuta, ta yadda zai gabatar da ita idan gari ya waye ko kuma duk lokacin da ya bukace ta.
Sannan masu sukar diyan sabuwar wakar Dauda Kahutu Rarara cewa wai kalmomin ba su hau daidai ba, ai dama na daga cikin ka’idar waka ta karya dokar nahawu muddin kafiya za ta fita yadda ya dace.
Akwai wasu wurare a waka da aka hadu tsakanin Marigayi Shata da Dauda Kahutu Rarara, misali Shata na yin wakoki mabambanta a lokaci daya, ma’ana da ya kammala wannan ya dora kan waccan. Haka Dauda Kahutu Rarara ke kokarin yi, a zama daya yana iya waka daya mai hawa biyu ko uku. Misali lokacin da Shata ya yi wakar Malam Sidi Mijin Hotiho, bayanai sun ce ba ita ce ya zauna ya yi ba, ya yi wasu wakokin kafin Sidi Mijin Hotiho ya zo, bayan ya zo ne, sai Shata ya rero masa tasa.
A bangaren Dauda Kahutu Rarara a misalin wakar Sani Aliyu Danlami
Amshin hawa na farko na cewa’
“…..Hajji Sani dawo Danlami,
Dawo ba mu sake zabe na tumun-dare, hoto….”
Amshin hawa na biyu na cewa’
“…….Mai Raba Alkhairin nan,
Katsina dawo-dawo,
Sani Danlami mun gamsu da alkhairinka…..”.
Kada ku yi mamaki, akwai mutane da yawa (wataqila) da har gobe suke so Dauda Kahutu Rarara ya yi musu, wataqila sun ma bashi kudin, wasu ya amsa, wasu ya ki amsa, amma har yanzu wakar ba ta samu ba, saboda wakar irin tasu ba ta zo masa ba, sai su ga kamar girman kai ne ko raini ya sa bai yi ba. Amma ga shi ya buge da wakar Fati Fatima Mai Zogale da har wasu ke ganin kamar Alkiyamar wakokin Rarara ce ta tsaya. A iya fahimtata, ci gaba ne Rarara ya samu, tun da idan ka tsaya falen daya wato a wakar siyasa kadai, a irin wannan lokacin da ba a buga gangar siyasa ba, sai mawakin siyasa ya ci me? Ko so kuke yi ya koma bara/roko? Idan bai yi irin waɗannan wakokin ba, za a ce ai wakar siyasa kadai ya iya, don haka an gama da shi idan siyasa ta wuce. Amma ko Bahaushe na cewa “gida biyu maganin gobara” kuma idan hagu ta kiya, ai sai a koma dama.
Abdullahi Garba Jani
07034656392
agarbajani@gmail.com
25/04/2024

‘Yan bindiga sun hallaka shugaban jam’iyyar APC a Katsina

Wasu mahara da har lokacin hada wannan labarin ba a tabbatar da adadinsu ba, sun bindige Malam Sai’idu Jikan Basa wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na mazabar Mai Dabino ta karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.
Majiyar DCL Hausa ta tabbatar mata da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:37 na yammacin Larabar nan a kan hanyarsa daga Danmusa zuwa Mai Dabino.
Bayanai sun ce an kira jiga-jigan jam’iyyar APC na karamar hukumar Danmusa zuwa wani taro a hedikwatar karamar hukumar, inda daga kauyen Mai Dabino ya tafi Danmusa don halartar wannan taro.
Yana kan hanyarsa ta komawa Mai Dabino bayan kammala taron, wannan ibtila’in ya faru da shi, da wani mutumin kauyen Kokarawa da ya rago wa hanya zuwa kasuwar Mai Dabino da ke a ranar Larabar nan.
Majiyar ta ce an yi musu jana’iza bayan sallar la’asar din nan da yammacin Laraba.
Kauyen Mai Dabino na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro da ba su iya shiga hedikwatar karamar hukumar Danmusa sai sun zagaya ta karamar hukumar Kankara.

Emefiele ya yi amfani da N18bn wajen buga sabbin kudi N684.5m – EFCC

 Emefiele ya yi amfani da N18bn wajen buga sabbin kudi N684.5m – EFCC 

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sake shigar da Emefiele kara kan sabuwar tuhuma da take yi masa na amfani da zunzurutun kudade da yawansu ya kai N18bn waje buga sabbin kudi N684.5m

EFCC ta shigar da karar ne a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

A cikin takardar tuhumar da aka fitar a ranar Talata, EFCC ta yi zargin cewa Emefiele ya karya doka da nufin cutar da jama’a a lokacin da yake aiwatar da manufar musanya Naira a lokacin mulkin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika kan badakalar N8bn.

 EFCC  ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika kan badakalar N8bn.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, bisa zargin sa da hannu almundahanar  kudi N8,069,176,864.00.

Jaridar PUNCH ta rawaito  cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama da ake tuhuma ya isa babban birnin tarayya na hukumar EFCC da misalin karfe 1:00 na ranar Talata.

Wakilinmu Jaridar punch da ke ofishin hukumar EFCC na Wuse, ya bayyana isowar tsohin ministan a ofishin hukumar da ke Abuja a cikin rudani.

Bayan isowarsa hukumar, a halin yanzu Sirika yana ganawa da jami’an hukumar EFCC domin amsa tambayoyi kan badakalar kwangilar da ake zarginsa da badawa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakin kanin sa Abubakar Sirika.

Wasu majiyoyi da ba a iya tantance su ba, wadanda suka yi magana kan lamarin, saboda ba su da izinin yin magana, sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Ashirye nake na bayyana a gaban Kotu – Yahaya Bello

 Ashirye nake na bayyana a gaban Kotu – Yahaya Bello

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya roki wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta janye umarnin kama shi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (EFCC) ta yi masa a ranar 17 ga watan Afrilu.

Yahya Bello, ta bakin lauyansa Adeola Adedipe, SAN, ya gabatar da bukatar ne biyo bayan umarnin mai shari’a Emeka Nwite, inda ya umurci EFCC da ta aiwatar da tuhume-tuhumen da shaidu a kan babban lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed, SAN.

Kamfanin dillancin labarai a Nijeriya NAN ya ruwaito cewa tun da farko mai shari’a Nwite, ya umarci lauyan EFCC, Kemi Pinheiro, SAN, da ta yiwa Mohammed babban lauyan Bello aike da tarin tuhume-tuhume da hujjojin shaida a hukuncin da aka yanke a yau.

Sai dai jim kadan bayan yanke hukuncin, Adedipe ya bayar da hujjar cewa umarnin kamawar, tun da aka bayar kafin tuhumar ya kamata a ajiye su a gefe yazo(da kansa, ba tare da wata bukata daga bangarorin da abin ya shafa ba).

Lauyan wanda ake tuhumar Adedipe,yace wanda ake tuhuma yana son zuwa kotu amma yana tsoron cewa akwai umarnin kama shi da ya rataya a kansa.

CBN ya fara sayarwa da yan canji Dala akan N1,021.

 CBN ya fara sayarwa da yan canji Dala akan N1,021.

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake fitar da wata takardar sanarwa ga masu gudanar da ayyukan BDC, inda take sanar da su cewa su sayar da dalar Amurka kai tsaye a kan farashin Naira 1,021 kan kowace dala.

Sanarwar ta kara da cewa an rubuto ne domin sanar da cewa babban bankin Nijeriya (CBN) ya sayar da dala 10,000 ga BDC kan kudi N1,021/$1. BDCs kuma ana sanar da dukkan masu amfani da ita.

Don haka an umurci dukkan BDCs da suka cancanta su fara biyan kuɗin Naira zuwa Lambobin ajiya na CBN Naira daga Litinin 22 ga Afrilu, 2024, kuma su gabatar da tabbacin biyansu, tare da wasu takaddun da suka dace, don fitar da FX a CBN daban-daban. rassan sa.

Wannan dai na daga cikin matakan da bankin ya dauka na ci gaba da tafiyar da Naira yayin da ta fadi kan dala a kwanakin baya.

Dangin amarya sun hallaka dan bindiga, yayin da suka dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Zamfara

 Dangin amarya sun hallaka dan bindiga, yayin da suka dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Zamfara

‘Yanwata uwan wata amarya da gungun fasinjoji sun dakile yunkurin yin garkuwa da wani dan ta’adda a jihar Zamfara.

PR Nigeria ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindiga suka yi wa iyalan amaryar da wasu matafiya kwanton bauna a hanyar Talata Mafara zuwa Gusau.

Iyalan amaryar sun yi tafiyar ne don siyan kayayyaki da sauran kayan aure a Kano.

Wani ganau da ya zanta da PRNigeria ya bayyana cewa an mayar da martani ne cikin gaggawa, biyo bayan yunkurin ‘yan bindigar na sace fasinjojin.

Duk da cewa daya daga cikin ‘yan fashin ya yi nasarar tserewa, jajirtattun fasinjojin sunyi nassarar kama bindigu kirar AK-47 guda biyu.

Da yake ba da labarin yadda abin ya faru, wani mai shaidar gani da ido ya ce: “A lokacin da ake tafiya kilomita kaɗan daga shingen bincike na jami’an tsaro na Fangal Tama, matafiyan sun ji ƙarar harbe-harbe ta ko’ina abinda yaja hankalin fasinjonin kokarin nemo hanyar da zasu maida martani.

Dangote ya sake zaftare farashin man dizil, yanzu lita ta koma N940

 Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man dizal da na jiragen sama zuwa N940, N980 akan kowace lita.

Shugaban sashen sadarwa na rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, wanda ya tabbatar da wannan sabon farashin, ya ce hakan ya yi daidai da kokarin da suke yi na rage wahalhalu da matsin tattalin arziki a Nijeriya.

Chiejina ya bayyana cewa sabon farashin N940 ya shafi abokan cinikin da ke siyan lita miliyan biyar zuwa sama daga matatar yayin da farashin N970 na masu sayen lita miliyan daya zuwa sama.

Ya tabbatar da cewe matatar man Dangote ta shiga wani shiri na hadin gwiwa da gidajen mai da mai na MRS, domin tabbatar da cewa masu amfani da man sun samu siyan mai a farashi mai sauki, a dukkan tashoshinsu na Legas ko Maiduguri.”

Kuna iya siyan dizal mai ƙasa da lita 1 akan N1,050 da kuma man jiragen sama akan N980 a dukkan manyan filayen jiragen sama da MRS ke aiki kamar yadda ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa za a fadada hadin gwiwar ne ga sauran manyan ‘yan kasuwar man.

Idan dai ba a manta ba ko a makwannin da suka gabata Dangote ya sake rage kudin litar man dizal daga 1200,zuwa dubu 1000.

Yanzu-yanzu: Jirgin kamfanin Dana ya yi hatsari a filin jirgin sama na Lagos

Yanzu-yanzu: 
Jirgin kamfanin Dana ya yi hatsari a filin jirgin sama na Lagos

Wani jirgin saman kamfanin Dana Air ya yi hatsari a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke birnin Lagos da safiyar Talatar nan.
Rahotanni sun bayyana cewa ba a samu asarar rai ba kamar yadda Jaridar Leadership ta rawaito.
Har zuwa wannan lokacin ba a samu cikakkun bayanai da game  da afkuwar lamarin ba.

Tinubu ya tafi kasar Netherland domin ziyarar aiki.

Tinubu ya tafi kasar Netherland domin ziyarar aiki.
A yau ne shugaba Bola Tinubu zai fara wata ziyarar aiki a kasar Netherlands domin tattaunawa da firaministan kasar Mark Rutte.
A wata sanarwa da aka fitar a daren jiya a Abuja mai dauke da sa hannun mai bawa ahugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale, ya ce shugaban ya kai ziyarar ne bisa gayyatar firaminista Rutte.
Yayin da yake kasar Netherland, shugaba Tinubu zai gudanar da taruka daban-daban da Sarki Willem-Alexander, da Sarauniya Maxima,da babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya kan hada-hadar kudi don ci gaba kasa (UNSGSA).
Ka zalika Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na Nijeriya da Dutch, wanda ke da nufin samo damammaki na haɗin gwiwa da tsakanin ‘yan kasuwa na Nijeriya da Holland, musamman a fannin noma da kula da ruwa.
Daga baya shugaba Tinubu zai tafi birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na musamman na dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 28-29 ga watan Afrilu kamar yadda sanarwar ta ce.