Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 444

Irin ukubar da ‘yan fanshon jihar Katsina ke sha kan layin tantance su cikin rana

Wasu dattijai da shekarunsu ya haura 65, galibi da rashin lafiya tattare da su, sun nuna rashin jin dadinsu kan tsarin da ake bi wajen tantance su musamman a garin Malumfashi da ke jihar Katsina.
A ziyarar gani da ido da DCL Hausa ta kai Malumfashin ta gane wa idanunta yadda tsofaffi galibi masu fama da rashin lafiya ke bin layin fiye da mutane dubu 1 cikin tsananin rana.
Wani daga cikin yan fanshon da muka zanta da shi ya bayyana mana yadda ya tarawa kansa bashi, la’akari da yadda yake kashe fiye da Naira 1,500 a kudin mota cikin sama da kwanaki 4 da ya shafe yana zuwa ba tare da ya samu an tantance shi ba.
Ko da wakilan DCL Hausa suka ci gaba da yunkurin jin bahasi, sun lura da yadda yaran wasu tsofaffin ke goyo su sannan su ajiye su kan rashin lafiya cikin tsananin zafin rana a Galadima Primary School da ke garin na Malumfashi.
Kawo yanzu dai an sallami ‘yan fanshon ba tare da kammala tantance su ba tare da ba su umurnin sake komawa ranar Laraba don sake kafa layin da wasu ke fara bi tun da safe.

Nijeriya za ta karfafa hadin gwiwa da sauran kasashe domin yaki da ta’addanci a Africa.

 Nijeriya za ta karfafa hadin gwiwa da sauran kasashe domin yaki da ta’addanci a Africa.

Shugaba Bola Tinubu ya ce Nijeriya za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da jagoranci wajen daukar matakan dakile ayyukan ta’addanci a Afirka.

Tinubu ya bayyana haka ne a wajen wani babban taron yaki da ta’addanci na kasashen Afirka da aka yi ranar Litinin a Abuja mai taken “Karfafa hadin gwiwar yanki da gina cibiyoyi don magance ci gaban barazanar ta’addanci a Afirka”.

Ya ce an inganta ayyukan yaki da ta’addanci a Nijeriya ta hanyar kafa dokar hana ta’addanci da kafa cibiyar yaki da ta’addanci ta Kasa, NCTC.

Shugaban ya ce, duk da haka dole ne nahiyar Afirka ta bi diddigin abubuwan da ke haifar da ta’addanci ta hanyar gudanar da shugabanci nagari, bin doka da oda, adalci da kuma hada kai.

Ya ce dole ne a baiwa ‘yan kasar tabbacin tsaron lafiyarsu ta hanyar tsare-tsare masu karfi da nufin kawar da matsalar ta’addanci.

Yaki da ta’addanci na bukatar cikakken tsari. Dole ne mu magance tushen abubuwan da ke haifar da tsatsauran ra’ayi, kamar talauci, warewar jama’a, da rashin adalci a cikin al’umma inji Tinubu

Mun kori biyu daga cikin dakarun mu dan tabbatar da mutunci da kwarewar aikin soja a Nijeriya -kakakin rundunar sojojin Nijeriya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da sallamar wasu daga cikin sojojin ta bayan samun su da laifi dumu-dumu na satar wasu wayoyin lantarki a matatar Dangote a daidai lokacin da ya kamata su kasance a bakin aiki.

Jam’in hulda da jama’a na rundunar sojojin, Manjo janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da korar sojojin biyu Kofur Innoson Joseph da Kofur Jacob Gani bayan gurfanar da su a kotun soji inda suka gagara musanta Laifuka da aka zarge su da aikatawa.

Ya ce an same su da laifin gaza gudanar da aikin su na soja kamar yadda dokar aikin soja sashe na 57 ya tanadar da kuma aikata wasu laifuka irin na farar hula ƙarƙashin tanadin kundin na 114 ƙaramin sashe na ɗaya a kundin dokokin aikin soja mai lamba A20 na shekarar 2004 a Najeriya.

Su dai korarrun sojojin biyu sun shiga hannu ne a sanadin wani mai suna Smart, wanda ya bukaci su raka shi ya ɗauki wadannan wayoyi da aka bari a kamfani, saidai da ya ga alamun zasu shiga hannu sai ya tsere ya bar su da jangwam.

Ƙirƙirar yan Sandan jihohi zai zama silar ƙãrin sãɓani a tsakanin ƙabilu-Sufeta janar na yan sandan Najeriya

Sufeta janar na yan sanda a Najeriya Olukayode Egbetokun ya ce Najeriya bata kai matsayin da zata yi ‘yan sandan jihohi ba saboda za’a riƙa samun umurni daga ɓangarori biyu wato bangaren gwamna da na sufeta janar.

Sufeta janar Olukayode yayi zargin akwai yiyuwar gwamnoni a Najeriya suyi amfani da yan sandan jihohi su wuce gona da iri da kuma take hakkokin yan Adam.

Olukayode Egbetokun ya baiyana cewa jihohi basu da wadãtar da zasu samar da irin ‘yan sandan da ƙasa ke bukata domin a kowace shekara ana buƙatar ɗaukar sãbin yan sanda dubu 30 kamar yadda majalisar ɗinkin Duniya ta bukaci a yi dan samar da ‘yan sanda na zamani.

Ya ce maimakon kirkiro yan sanda na jihohi, ƙãra gwamnati ta haɗe jami’an tsaro na civil defence dana hukumar kare haɗura ta ƙasa road safety wuri guda da yan sanda, ta yadda civil defence ɗin da jami’an roadsafty zasu zamo wasu sassan rundunar yan sanda.

Mu na so ka sake rage Naira 300 a farashin dizil a Najeriya

Bayan zabge Naira ɗari biyu da hamsin (250) a farashin ma’aunin lita guda na dizil, ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya IPMAN ta buƙaci matatar mai ta Dangote ta maida farashin litar ta dizil zuwa Naira ɗari bakwai (700).

Mataimakin shugaban kungiyar a Najeriya Hammed Fashola ya ce tunda yanzu babu maganar biyan kuɗin dakon man a jigin ruwa da kuma biya Kwatsam da sauransu, saboda a gida Najeriya ake haƙo tare da tãce man, akwai bukatar farashin ya sauƙa zuwa Naira 700.

Baya ga nuna farin cikin ƙungiyar ta IPMAN kan ragin Naira 250 da matatar Dangote ta yi a kuɗin na dizil, Mammed Fashola ya kuma ce la’akari da yadda darajar Naira ke ƙaruwa, babban dalili ne na rage kuɗin na dizil zuwa 700.

Matatar man ta Ɗangote dai ta fara rage kuɗin na dizil ne daga Naira 1,600 zuwa 1,250 makwanni biyu da suka gabata, sannan a mako da ya gabata kuma ta sanar da sake zabge Naira 250 a makon jiya.

Mutun sama da 4000 aka kashe da kuma garkuwa da su a farkon shekarar 2024.

Mutane sama da dubu biyu da ɗari biyar aka kashe, aka kuma yi garkuwa da wasu mutanen fiye da dubu biyu a watanni uku na farkon wannan shekara a Najeriya a cewar binciken da wani kamfanin da ke samar tsaro da kuma tattara bayanai kan lamurran tsaron a Najeriya mai suna Beacon Security and Intelligence limited.
Saidai ƙididdiga da kamfanin ya bayar na nuna cewa kaso 80 cikin ɗari na kashe-kashen da aka yi a arewa suka auku, sa’annan kaso 94 na garkuwa da mutane da aka yi daga watan Junairu zuwa Maris sun auku ne a yankin Arewacin Najeriyar.
Wannan ƙididdiga na kamfanin Beacon Security ya baiyana cewa a kullu yaumin ana kashe rayukan mutane 28, ana kuma yin garkuwa da aƙalla Mutane 24 a kowa ce rana.
Toh saidai wannan himma na gano yawan mutuwa da garkuwa da ake yi da mutane da wannan kamfani ya yi, ya ci karo da bayanan mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro malam Nuhu Ribadu, wanda ya nuna cewa an samu raguwar aukuwar mace-mace da kuma garkuwa da mutane da kamfanin na Beacon ke fadi cewa sun auku a farkon shekarar nan ta 2024.

An sake dakatar da Ganduje a APC daga mazabarsa, an ce ba ya biyan kudin harajin jam’iyya

Rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Kano ya sake daukar sabon salo, inda wasu shugabannin jam’iyyar a matakin mazaba suka bulla, inda suka sake sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Umar Ganduje.
Jaridar Solacebase ta ba da labarin cewa sabon tsagin shugabancin jam’iyyar a mazabar Ganduje cikin karamar hukumar Dawakin Tofa sun ce su ne halastattun shugabannin jam’iyyar daaka zaba a 31 ga watan Juli, 2021.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Kano, Sakataren jam’iyyar na mazabar Ganduje Ja’afar Adamu, da ya yi magana a madadin sauran shugabannin jam’iyyar 11, ya ce dakatar da Ganduje a jam’iyyar ya zama wajibi biyo bayan zarginsa da yin ‘Anti Party’ wato yi wa jam’iyya zagon kasa musamman a zaben da ya gabata da ba ta yi nasara ba.
Ja’afar Adamu wanda dan’uwa ne na jini ga tsohon Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje, ya zargi mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa da kitsa wutar rikici da ta yi sanadiyar tabarbarewar lamurran jam’iyyar da yawa.
Sakataren jam’iyyar ya ma yi zargin cewa Abdullahi Umar Ganduje na ya biyan kudin harajin jam’iyyar na ‘statutory party dues’. Ya yi zargin cewa wadancan mutanen da ke kiran kansu shugabannin jam’iyyar APC a mazabar, na bogi ne.

Shugaban Nijeriya Bola ya amince da wasu tsare-tsare guda hudu don inganta fannin ilimi a kasar

Tsarin zai yi wa fannin ilimi garambawul don inganta koyo da bunkasa fasahar zamani.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma Ajuri Ngelale ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya ce manufofin da aka amince sun hada da (DOTS),ma’ajin adana bayanai ga malamai, mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta, koyarda malamai fasahar zamani domin inganta koyo da koyarwa.
Mista Ngelale ya ce shirin zai kunshi dukkan makarantu tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantun sakandire.

Tsanar da ake yi wa ‘yan sanda na shafar tsaron Nijeriya in ji PCRC

Kwamitin abokai da masu hulda da jami’an ‘yan sanda ta PCRC ta hannun shugabanta Magaji Olaniyan ta yi kira da a kawo karshen abin da ta kira da irin tsanar da ake yi wa jami’an ‘yan sandan Nijeriya.
Olaniyan ya ce akwai takaici cikin wannan tsana da ake nuna wa ‘yan sanda, da ya ce hakan na shafar batun tsaron da jami’an ‘yan sandan ke bayarwa.
Ya yi Allah-wadai da irin nuna kyama da tsanar ‘yan sanda da ya ce ana samu nan da can a Nijeriya, inda ya ce kwamitinsu na abokan ‘yan sanda zai ci gaba da yaukaka danganta a tsakani.

Kishin arewa ya sa Shugaba Tinubu ya ba ‘yan yankin mukamai masu muhimmanci – Nuhu Ribadu

 

Shugaba Tinubu na son a shawo kan matsalolin arewa shi ya sa ya nada ‘yan yankin mukamai masu muhimmanci in ji Nuhu Ribadu
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya soyayyar da ke tsakanin shugaba Tinubu da yankin arewacin Nijeriya ne ya sa ya nada mutanen yankin mukamai masu muhimmanci.
Ya ce an yi hakan ne domin a taimaka a shawo kan duk wasu matsalolin da yankin ke fuskanta.
Malam Nuhu Ribadu na magana ne a Sokoto inda ya ce shugaban kasar na sane ya zabo mukamai masu gwabi ya nada ‘yan arewa don su taimaki yankinsu.
Ya ce ko talaucin da ke damun yankin na da ban tsoro, inda shugaban kasar a lokacin kafa jami’an gwamnatinsa, ya ce zai yi duk abin da ya dace don ganin an ceto yankin daga halin da ya ke ciki.
Daga cikin mukamai masu gwabin da shugaba Tinubu ya nada ‘yan arewa akwai na tsaro, aikin gona, ilmi, harkokin waje da lafiya.