A yayin da Dala da CFA ke ci gaba da sauka a kasuwa, ana kara samun rahusa a kayakin abincin da ake shigo da su daga waje. Sai dai fa abincin da ake nomawa a kasar kuwa farashin bai sauka har yanzu.
Farashin kayan abincin waje ya fi sauki fiye da na gida a Nijeriya
Atiku da Wike sun hadu, karon farko tun bayan zaben 2023, sai dai babu tabbacin ko sun gaisa
A karon farko tun bayan zaben 2023, Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun hadu wajen guda don taron jam’iyyar PDP.
Fasinjoji sun yi sanadiyyar mutuwar wani jami’in kwastam a Katsina
Matsin tattalin arziki ya sa za a rufe kamfanonin sarrafa giya guda biyu a Nijeriya
Matsin tattalin arziki ya sa za a rufe kamfanonin sarrafa giya guda biyu a Nijeriya
Kamfanin samar da giya na Nigerian Breweries na shirin rufe kamfanoni guda biyu,hakan nada nasaba ga ɗimbin matsalolin kuɗi da suke fuskanta, kamfanin ya bayyana hakan a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Abubuwan da ke damun babban kamfanin sun hada da asarar musayar kudaden waje da aka yi a bara, wanda hakan ya sa ba shi da wani zabi illa rufe biyu daga cikin masana’antun.
Ya bayyana cewa wani babbar asarar da aka yi kan hada-hadar kudaden waje da ya kai Naira biliyan 153.3 ya sanya Kamfanin Breweries na Nijeriya ya yi babbar asara a bara, tun bayan da ya fara aiki shekaru 77 da suka gabata a kasar.
Asarar Naira biliyan 106.3 da aka yi a cikin 2023 ya samo asali ne daga matsalolin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki, rashin daidaituwar FX, da sauransu,kamar yadda kamfanin ya bayyana.
An sanar da kungiyoyin kwadagon da suka hada da kungiyar abinci da abin sha da ma’aikatar taba sigari da kuma kungiyar masu shayar da kayan sha da taba sigari kan matakin dakatar da aiki na wani dan lokaci a kamfanonin biyu, a cewar takardar.
Hukumar NDLEA ta lalata tare da kona kilogram 304,436 na muggan kwayoyi a Lagos
Hukumar NDLEA ta lalata tare da kona kilogram 304,436 na muggan kwayoyi a Lagos.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, ta lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun abubuwa da aka kama daga sassan jihohin Legas da Ogun a ranar talata.
Da yake jawabi a wajen wani bikin da aka lalata magungunan da aka kama a garin Badagry na jihar Legas, shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya ce an lalata haramtattun kwayoyin da aka kama a fili biyo bayan umarnin da kotu bayar.
Daga nan sai ya yi kira da a kara tallafawa jama’a domin ci gaba da kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke yi na dakile illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Marwa ya ce, “Duk da cewa ana gudanar da atisaye na yau da kullun da kuma tsari na kawar da abubuwa masu hadari daga cikin al’ummarmu, amma ana gudanar da lalatar da haramtattun kwayoyi a gaban jami’an kotu abubuwan da suka hada da haramtattun kwayoyi a jihohin da dama. haka kuma a ajujuwa daban-daban kamar su hodar iblis, da tabar heroin, da wiwi, da tramadol, da sauransu.
Ya ce jami’an hukumar ta NDLEA a sassa daban-daban na hukumar ne suka kama su a jihohin Legas da Ogun tun daga watan Janairun 2022 zuwa yau, musamman a tashoshin jiragen ruwa na Legas da filayen jiragen sama da kuma kan iyakokin kasa.
Matatar mai ta Dangote ta sanar rage farashin man dizal.
Ana hasashen cewa ambaliyar ruwa za ta shafi jihohin Nijeriya 31 a bana
Ana hasashen cewa ambaliyar ruwa za ta shafi jihohin Nijeriya 31 a bana
Gwamnatin tarayya ta rubutawa gwamnoni 31 takardar sanar da su halin da ake ciki na ambaliyar ruwa a jihohinsu tsakanin watan Afrilu zuwa Nuwamba na wannan shekara ta 2024.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2024.
A wajen taron, hukumar kula da ayyukan ruwa ta Nijeriya, an bayyana cewa an ware kananan hukumomi 148 a jihohin Legas, Kano, Delta, da kuma wasu jihohi 28 a matsayin wuraren da ake fama da matsalar ambaliya.
Hasashen da aka samu na shekara ta 2024 na ambaliyar ruwa ya nuna cewa wani bangare na kananan hukumomi 148 a cikin jihohi 31 na tarayya sun fada cikin yankunan da ake fama da matsalar ambaliya, yayin da wani bangare na kananan hukumomi 249 da ke cikin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja sun fada cikin tsaka mai wuya.
Jihohin da ke fama da matsalar ambaliya sun hada da Adamawa, Akwa-Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas , Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe.
‘Yan bindiga sun kashe Sakataren jam’iyyar PDP a jihar Zamfara
‘Yan bindiga sun kashe Sakataren jam’iyyar PDP a jihar Zamfara
‘Yan bindiga sun kashe Sakataren jam’iyyar PDP na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Garba Garewa ne ya tabbatar da kisan sakataren na jam’iyyar a Tsafe ga gidan talabijin na Channels ranar Talata.
“Muna zargin wadanda suka kashe shi ‘yan fashi ne, sun shiga gidansa jiya (Litinin) suka harbe shi,” in ji Garewa.
Na hango za a kara shiga wahala a Nijeriya – Primate Ayodele
Na hango za a kara shiga wahala a Nijeriya – Primate Ayodele
Shugaban cocin INRI Evangelical Church, Primate Ayodele ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya canza salonsa na farfado da tabarbarewar tattalin arziki saboda har yanzu akwai tarin matsalolin a fannin tattalin arziki a Nijeriya.
Ayodele ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu.
Ya bayyana cewa har yanzu abubuwa za su ci gaba da tsada kuma za a kara samun hauhawar farashin kayayyaki matukar gwamnati ba ta inganta harkar noma da tabbatar da samar da man fetur mai sauki da kuma ci gaba da samar da wuraren da za rika tace man fetur a kasar.






