Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 446

Ni ba uban gidan kowa ba ne a siyasar jihar Kaduna – Elrufa’i

 Ni ba uban gidan kowa ba ne a siyasar jihar Kaduna – Elrufa’i 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce ba ya son a yi masa kallon ubangidan kowa a siyasar jihar Kaduna.

Elrufa’i ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna ilimi ga manyan jami’an gwamnati a jihar Borno, ranar Litinin.

Ya ce sau biyar kacal ya ziyarci jihar ta Kaduna tun bayan da ya bar mulki kusan shekara daya da ta wuce.

An lissafto Sanatocin Katsina da Kano da ba su gabatar da kudirin doka a zauren majalisa ta 10 ba

Daga cikin Sanatocin kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna, akwai Sanata Rufa’i Hanga da ke wakiltar Kano ta tsakiya da Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da ke wakiltar Katsina ta tsakiya da Sanata Muntari Dandutse da ke wakiltar Katsina ta Kudu.
Kazalika binciken ya gano tsoffin Gwamnoni 4 da ke zauren majalisar yanzu haka da ba su gabatar da kudirin doka ko daya ba tun da aka rantsar da majalisar, daga cikin akwai Abdul’aziz Yari daga jihar Zamfara, Adams Oshimhole daga jihar Edo da Simon Lalong daga jihar Plateau.
A majalisa ta 10 dai akwai tsoffin Gwamnoni 13 da suka yi nasarar zama sanatoci bayan sun kammala wa’adin mulkinsu na gwamnoni. Daga cikinsu akwai shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio daga Akwa Ibom da Abdul’aziz Yari daga jihar Zamfara da Aliyu Wamakko daga Sokoto da Aminu Tambuwal daga Sokoto.

Gwamnan Katsina ya nada sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar

Gwamna Radda ya nada Falalu Bawale a matsayin sabon shugaban ma’aikata na Katsina (Head of Civil Service)

Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince da nadin Alhaji Falalu Bawale a matsayin shugaban ma’aikata na jihar.
Bawale har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina ya kasance Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikata na Katsina.
Alhaji Bawale ya karbi mukamin ne daga Alhaji Usman Isyaku wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati bayan ya shafe shekaru 35 yana aiki.
Gwamna Radda ya kuma amince da nadin tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Isyaku a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sake fasalin harkokin ma’aikatan gwamnati.
Gwamna Radda ya taya sabon shugaban ma’aikata murnar nadin da aka yi masa, ya kuma bukace shi da ya kawo kwarewa a sabon mukamin da aka nada shi. Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban ma’aikata mai barin gado bisa gudunmawar da ya bayar tare da yi masa fatan alheri a kan sabon mukaminsa.

Karamar hukumar Danmusa na bukatar daukin gaggawa a bangaren tsaro in ji Danmusa Forum

Kungiyar tabbatar da shugabanci na gari ta karamar hukumar Danmusa wato (Danmusa LG Forum for Good Governnace) ta roki gwamnatin jiha da ta samar da shingen jami’an tsaro akan hanyar Yantumaki zuwa Danmusa don tababbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. 
Shugaban kungiyar kwamarad Haruna Jafaru Danmusa ya yi wannan rokon a cikin wata sanarwa da ya fitar aka kuma raba wa manema labarai a Katsina. 
Kamar yadda ya ce hanyar Yantumaki zuwa Danmusa ta kasance cikin hatsari a halin yanzu sakamakon yawan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa matafiya a hanyar wanda ke jawo rasa rayuka da kuma yin garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa ‘yan ta’adda sun mayar da hanyar abin tsoro ga jama’ar yankin sakamakon yadda kusan duk rana ta Allah sai sun tare matafiya a hanyar.
Kwamarad Haruna jafar ya jaddada cewa kiran ya zama wajibi ta la’akari da yadda hare-haren ‘yan ta’adda ya kassara tattalin arzikin al’ummar yan’kin. 
Shugaban kungiyar ya yi amfani da damar wajen yaba ma gwamnatin jiha bisa irin kokarin da ta ke yi wajen tabbatar da kawar da matsalar tsaro a fadin jihar.

Zargin cin hanci da rashawa:An dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa.

 Zargin cin hanci da rashawa:An dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa.

Jam’iyyar APC reshen mazabar Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar kano, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a na mazabar Ganduje Halliru Gwanzo shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Dakta Ganduje daga jam’iyyar ne saboda zargin karbar cin hanci da gwamnatin Kano ke yi masa.

Sun ce dakatarwar ta fara ne yau 15 ga Afrilu 2024.

Hukumar EFCC ta tabbatar da kwato N32.7billion da $445,000 daga ma’aikatar jin kai ta kasa.

 Hukumar EFCC ta tabbatar da kwato N32.7billion da $445,000 daga ma’aikatar jin kai ta kasa.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar da kwato naira biliyan 32.7 da kuma dala 445,000 yayin binciken jami’an ma’aikatar jin kai da kula da walwalar al’umma na baya da na yanzu.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, a ranar 8 ga watan Janairu, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya dakatar da ministar harkokin jin kai, yaki da ci gaban al’umma, Betta Edu, kan badakalar kudade.

Betta Edu dai ta fuskanci suka ne bayan da wata takarda ta bayyana a yanar gizo, inda ta bukaci babban akanta na tarayya Oluwatoyin Madein da ta tura kudi naira miliyan 585 zuwa wani asusu mai zaman kansa.

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Mista Tinubu ya umurci hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Kasa ta’annati, EFCC, ta gudanar da cikakken bincike a kan dukkan al’amuran da suka shafi hada-hadar kudi da ta shafi ma’aikatar da Edu ke jagoranta.

A baya-bayan nan dai an samu rahotannin da ke nuna cewa hukumar EFCC ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga hannun  Edu, wanda daga baya ta musanta.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce binciken da takeyi ya shafi jami’an ma’aikatar na da da na yanzu.

Jami’an tsaro sun ceto sauran daliban jami’ar Gwamnatin tarayya ta Gusau su 23 da karin wasu masu yiwa kasa hidima (NYSC).

 Jami’an tsaro sun ceto sauran daliban jami’ar Gwamnatin tarayya ta Gusau su 23 da karin wasu masu yiwa kasa hidima (NYSC).

Ragowar ma’aikatan Jami’ar tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da aka sace a ranar 22 ga Satumba, 2023, sun samu ‘yanci.

Wasu ‘yan bindiga a kwanakin baya sun kai farmaki gidajen kwanan dalibai a unguwar Sabon-Gida da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 20,da yawancinsu mata ne.

Bayan kokarin da hukumomin jami’ar da ‘yan uwan su suka yi, an sako wasu daga cikin wadanda aka kama bayan watanni, amma 23 sun ci gaba da kasancewa a hannunsu ‘yan bindingar.

Sai dai wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa jami’an tsaro sun ceto sauran daliban a ranar Lahadin da ta gabata.

An sako su ne a Kuncin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara kuma aka mika su ga jami’an gwamnati ranar Lahadi. Jimillar mutane 23 ne gaba daya,kamar yadda wata majiya ta bayyana

Majiyar ta kara da cewa an kubutar da wasu daga cikin masu yi wa kasa hidima (NYSC) da aka sace a jihar Sokoto.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin da rikicin ya shafa a yakin da ake yi da ‘yan bindigar da suka addabi mazauna yankin Arewa maso yamma.

Har yanzu ba mu ga darajar da Naira ta samu kan Dala ba a kasuwa, don farashi ya ki sauka in ji ‘yan Nijeriya

 Har yanzu ba mu ga darajar da Naira ta samu kan Dala ba a kasuwa, don farashi ya ki sauka in ji ‘yan Nijeriya

‘Yan Nijeriya sun koka da cewa duk da farfadowar darajar Naira a kan kudaden kasashen waje a ‘yan kwanakin nan, farashin kayayyakin abinci da na kayayyakin masarufi bai sauka ba.

Sun bayyana hakane a wani bincike da Daily Trust ta gudanar a shafukan sada zumunta, inda suka ce zuwa yanzu babu abinda yafaru a kwanakin nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa Naira ta samu gagarumar nasara a ‘yan kwanakin nan biyo bayan kakkausar murya da babban bankin ƙasar ya yi na kare kudin gida a kan dala.

Dalar dai da ta kusa kaiwa N2,000 makwanni da suka gabata, zuwa yanzu takoma kusan Naira 1,150 a kasuwar da ke bayan fage

A lokacin da Naira ke fama da faduwa, farashin kayan abinci da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje sun yi tsada sossai, lamarin da ya kara tabarbare tsadar rayuwa a Nijeriya.

Daily Trust ta tattauna da wasu yan Nijeriya inda suka cigaba da bayyana ra’ayoyinsu game da yadda naira take kara daraja amma haryanzu kayan masarufi basuyi sauki ba

Sedai duk da haka, sun yi fatan abubuwa za su fara sauka idan gwamnati ta ci gaba da tafiyar da yadda harkar kudade a halin yanzu.

Babban layin wutar lantarki na Nijeriya ya sake faduwa.

 Babban layin wutar lantarki na Nijeriya ya sake faduwa.

Kamfanin samar da wutar lantarki guda daya ne kawai ke aiki kamar yadda bayanai daga cibiyar mai zaman kanta (ISO) reshen kamfanin watsa labarai na Nijeriya ya bayyana.

Wannan shine karo na shida da Babban layin wutar yana faduwa a shekarar 2024 da muke ciki.

Daily Trust ta rawaito cewa da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin, sabbin bayanai da hukumar ta ISO ta fitar sun nuna cewa a halin yanzu tashar tana samar da wutar lantarki mai karfin mega watt266.50.

Da yake tabbatar da faduwar layin wutar a cikin wata sanarwa, Jos Disco ya ce Katsewar da ake fuskanta a halin yanzu a cikin jihohinmu ya samo asali ne daga cibiyar sadarwa ta kasa. Kuma faduwar layin wutar ya afku ne da sanyin safiya da misalin karfe 02:42 na yau litinin 15 ga watan Afrilu 2024, wanda hakan ya sa aka samu katsewar wutar lantarki ga dukkan bangarorin Nijeriya.

Shugaban Kamfanonin, Dakta Friday Adakole Elijah, ya bayyana fatan cewa za a dawo da grid din don samar da wutar lantarki ga masu amfani da ita da kuma kwastomin su.

DSS sun kama wata ‘yar APC mai goyon bayan tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i biyo bayan wani rubutu da ta yi a shafin Facebook.

 DSS sun kama wata ‘yar APC mai goyon bayan tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i biyo bayan wani rubutu da ta yi a shafin Facebook.

A ranar Lahadin da ta gabata ne jami’an tsaro da ake kyautata zaton jami’an tsaron farin kaya ne na hukumar DSS ne suka kama wata ‘yar siyasa mace kuma ‘yar jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Aisha Galadima.

An ce kamen na da nasaba da wani sako da aka wallafa a kafafen sada zumunta na yanar gizo game da gwamnan jihar, Uba Sani.

Wata majiya ta bayyana cewa, Galadima ta soki kalaman Uba Sani na karshe akan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Wata makwabciyarta ta ce an kama ta ne a unguwarsu da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi da yamma, sedai tun bayan daukan ta wayanta akashe yake ba asamu ji daga gareta ba. 

Sai dai babban sakataren yada labarai na gwamnan Jihar, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya game da kama ta, kuma ya mika wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS karin haske kan lamarin kamar yadda ya shaidawa Jaridar Daily Trust.