Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 447

‘Yan bindiga sun bude wa motar fasinja wuta a kauyen Katsina

Wasu mahara bisa babura sun bude wuta ga wata motar fasinja dauke mutane da mafiyawansu ‘yan yawon sallah ne a titin Yantumaki zuwa Danmusa a jihar Katsina
Majiyar DCL Hausa ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:36 na ranar Asabar din nan.
Sai dai bayanai sun ce ‘yan bindigar ba su yi nasarar kashewa ko raunata kowa ba a cikin motar. Amma majiyar ta ce razani ya sa wasu daga cikin fasinjojin sun ji raunuka.
Bayanai sun ce motar kirar Golf mai launin ja, na dauke da fasinjoji kusan 10, da ta tashi daga Sabuwar Tasha a cikin kwaryar birnin Katsina zuwa garin na Danmusa.
Rahotanni sun ce a karshe-karshen azumin Ramadana har zuwa shagulgulan sallah kusan duk rana sai barayin dajin sun tare hanyar Yantumaki zuwa Danmusa, ko dai su bude wuta ga matafiya ko su sace wadanda suka yi nasarar kamawa.
Tsakanin garin Yantumaki zuwa Danmusa dai na da nisan kilomita 17.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya ce zai tuntubi babban baturen ‘yan sanda na karamar hukumar Danmusa don jin yadda abin ya kasance, amma har lokacin hada wannan labarin, DCL Hausa ba ta samu martaninsa ba.

Neman suna kungiyar NEF ke yi – Shugaba Tinubu na son arewa in ji minista Matawalle

Neman suna kungiyar NEF ke yi – Shugaba Tinubu na son arewa inji minista Matawalle 
Ministan kasa a ma’aikatar tsaro ta Nijeriya Bello Mohammed Matawalle ya ce wadannan mutanen da ke kiran kansu dattawa a arewacin Nijeriya, su na yi ne ba don yankin ba, sai don neman suna a siyasance.
A cikin wata sanarwa da ministan ya sanya wa hannu da DCL Hausa ta samu kwafi, Bello Matawalle ya ce mutanen na yin wadannan kalamai ne kawai don su haddasa rudani, rarrabuwar kai da jefa shakku a zukatan ‘yan Nijeriya.
Ministan na martani ne kan kungiyar dattawan arewacin Nijeriya da ake kira NEF, wace da farko ta soki lamarin gwamnatin Bola Ahmad Tinubu cewa ba ta amfanin gwamnatin Muslim-Muslim ticket ba.
Sai dai a cikin sanarwar Minista Bello Matawalle ya ce wadannan mutane ba su da wani tasiri a yankin, asali ma, ba yankin arewar ne a gabansu ba.
Ya ce dan takararsu da ya sha kaye a zaben 2023 ne ya sa suka fito suke wadannan maganganun don su kawar da hankalin ‘yan Nijeriya daga irin abubuwa ci gaban da shugaba Tinubu ya fara assasawa.
Bello Matawalle ya ce NEF da ke kiran kansu dattawa, sai ga shi sun gaza samar da hadin kai a yankin na arewa. 
Ministan ya ce har yanzu ba kungiyar ba ta taba ziyartar wani minista da sunan su na so a tattauna batun tsaro, aikin gona, lafiya, ilmi da sauran batutuwan da suka shafi yankin ba domin sanin inda aka dosa a harkar aikin gwamnati.
Ya ce mafiyawansu sun fi son ganin laifin gwamnati don su yi suna.

Ganduje da matar sa zasu gurfana gaban kotu ranar 17 ga wannan wata na Aprilu

Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanar da ranar 17 ga watan Afrilun wannan shekara a matsayin ranar da tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a yanzu, Abdullahi Ganduje da matar sa da wasu mutane shida za su gurfana a gaban ta bisa zargin su da aikata laifuka har kashi takwas da suka haɗa da na karkata wasu kuɗaɗen gwamnati da almundahana da ma batun karɓan cin hanci na dalolin Amurka da aka yi wa tsohon gwamnan Ganduje.

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano Haruna Isa Dederi ya tabbatar da cewa an kammala hada dukkan takardu kan wannan Shari’a kuma za’a tura sammaci ga dukkan waɗanda ake zargi.

Kwamishinan Shari’a na Kanon ya ce abin da Ganduje bai fahimta ba shine bazai iya shã ba a wannan tuhume-tuhume, da yake fadin wai gwamnatin Kano bazata iya gurfanar da shi tare da kama shi da laifi ba saboda yana tãƙamar shi shugaban jam’iyyar APC ne na ƙasa, to amma ya sanī cewa wannan batu ne da ya shafi harkar jiha ba taraiya ba.

Yan kwanaki da suka wuce an jiwo Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano yana alwashin sai ya binciki Ganduje, saboda abin kunya da ya ce ya haifar wa jihar Kano.

Mahauci ya daɓa wa matar sa wuƙa a dalilin wayar salula

Wani mahauci yayi sanadin mutuwar matar sa bayan caka mata wuƙa da yayi bila adadin a bayan ta saboda daukar wayar sa ta salula da ya ce ta yi.
Rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin a Sabon Gari-Futy da ke ƙaramar hukumar Girei, inda a cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ta yan sandan jihar Adamawan ta fitar ke nuna cewar mijin matar mai suna Ibrahim Abubakar ɗan kimanin shekaru 33 a Duniya, shi ya fallasa kansa da kansa yana faɗin cewa yayi nadamar kashe uwar ɗan su guda.
Rundunar yan sandan ta ce an samu nasarar kama shi ne bayan sanar da ita wannan mummunan al’amari da mahaifin matar yayi, da kuma wasu bincike da aka gudanar da suka bada dãmar gano makami da yayi kisan da shi.

Abin da ya kamata ku sani dangane da Zakkar Fida-da-Kai tare da Sheikh Daurawa

 

((Daga shafin Facebook na Malam Daurawa))

ZAKKAR FIDDA KAI A CIKIN SAUƘI
Tambaya, Maicece zakkar fidda kai?
Amsa : Zakkar (kono) fidda kai, itace zakkar da a ke fitarwa duk shekara, a ranar ɗaya ga watan shawwal wato ranar salla.
Tambaya : Mainene Hukuncin ta?
Amsa : Hukuncin zakkar fidda kai, wajibi ce akan dukkan musulmi, namiji ko mace babba ko ƙarami.
Tambaya : Mainene Hikmar zakkar fidda kai?
Amsa : Hikmar zakkar fidda kai, tana da yawa daga ciki, akwai:
1. Tsafta ce da tsarkake mai azumi daga maganganu da aiyuka mara sa amfani da suka faru a gare shi a watan azumi.
2. Bayar da tallafi da taimako na jinƙai ga marasa ƙarfi.
3. Tana tsaftace jiki daga nauyin zunubi wanda ya rage, wanda a azumi bai kankare ba.
4. Nuna godiya ce ga Allah (ta’ala) bisa ni’imar gama azumi lafiya.
5. Ƙara yawan lada ne a kan wanda aka samu a cikin azumi.
6. Nuna farin ciki ne ga kowa yadda ko wanne talaka ya sami tuwan salla.
Tambaya a kan wa wannan zakkar ta wajaba?
Amsa : Ta wajaba a kan dukkan musulmi namiji ko mace, babba ko yaro. Bawa ko ɗa, Mai hali
Tambaya : Yaya ake gani mai hali da mara hali wajan yin zakkar?
Mai hali shi ne, wanda ya ke da abincin da zai ishe shi ranar salla shi da iyalin sa, abin da ya yi ragowa sai ya fitar da shi,
Tambaya : Shin Wanda ake bi bashi zai iya zakkar fidda kai?
Amsa: Idan bashin lokacin sa bai zo ba zai yi zakka, amma idan lokacin biyan bashin ya yi sai ya biya bashin, idan ya sami ragowa sai ya yi zakkar.
Tambaya : Shin uba zai fitarwa yayansa ƙanana zakkar.?
Amsa : Uba shi ne zai fitarwa ƴaƴansa ƙanana da zakkar fidda kai, manya kuwa kowa idan yana hali ya fitarwa kan sa.
Tambaya : Shin Mai bayi shi zai yi musu zakkar fidda kai?
Amsa: Idan mutum ya na da bayi marasa shi sai ya fitar musu tun da suna ƙarƙashin ikon sa.
Tambaya : Shin Miji ne zai fitarwa matarsa zakkar fidda kai?
Amsa. : Asali kowa ya fitarwa da kansa, tunda kowa shi ya yi azumin sa, domin wannan zakka ce bata ƙarƙashin ciyarwa, amma idan bata da hali sai ya fitar mata.
Tambaya : Shin za a fitarwa da jariri zakkar fidda kai.?
AMSA. : Idan an haifi yaro a cikin watan azumi ko kafin a saukowa daga idi sai a fitar masa.
Haka idan mutum ya musulunta kafin a sauko daga idi shima idan yana da hali sai fitar tunda ya riski lokacin ta yana musulmi.
Tambaya : A wane Lokacin da ake fidda zakkar fidda kai.?
Amsa: za a iya fitar da zakkar fidda kai a hali uku :
1. Kafin ranar salla, da kwana biyu, wannan fatawa da aikin Abdullahi dan umar.
2. bayan an ga watan salla. Wannan shi ne lokacin da take farawa.
3. Fitar da zakka kafin tafiya idi.
Tambaya wanda bai fitar ba har sai bayan an sako daga idi yaya hukuncin sa?
Amsa: Wanda bai fitar ba sai bayan idi to ta zama sadaƙa, amma bashi da ladan zakka idan da gangan yaƙi fitarwar.
Tambaya : Yaya hukuncin Fitar da zakkar fidda kai bayan an sakko daga idi?
Amsa: duk wanda bai fitar da zakkar fidda kai ba har aka sakko daga idi, to, ta zama sadaƙa, idan sakaci yayi zai sami laifi.
Amma Malikiyya suna ganin har zuwa rana ta fadi a ranar salla za a iya fitarwa, ga wanda bai sami dama ba kafin idi.
Tambaya za a iya rama zakkar fidda kai?
Amsa : za a iya rama zakkar fidda kai.
Tambaya : Wa za a bawa zakkar fidda kai,?
Amsa : Talakawa faƙirai, da miskinai marasa hali, da Wadanda suka cancanci a basu zakka.
Tambaya : Za a iya bawa wanda ba musulmi ba zakkar fidda kai,
Amsa :asali zakkar fidda kai ana bawa musulmi ne, amma ana iya bawa wadanda ba musulmi ba, idan ana maƙotaka da su, domin ciyarwa ce.
Tambaya : Wane Irin kayan abinci ake fitar da zakkar fidda kai daga gare su.?
Amsa : ana fitarwa daga abincin da aka fi yawan samu wanda aka fi ci, a wannan garin, ko a wannan ƙasar, da za a fitar da zakkar, ko wacce ƙasa da irin na su kayan abincin.
14.Yaya Gwargwadon yadda ake fitar da zakkar fidda kai.?
Mudu hudu ake fitarwa ga kowanne mutum daya.
. Tambaya: Shin za a iya bayar ƙima ta kuɗi?
Asali abinci ake bayarwa, amma idan akwai buƙarar bayar da kudin ana iya bayarwa, musamman wadanda suke ƙasashen da babu mabuƙata da yawa, suna iya aikawa da kudi a yi musu a wata Kasar.
tambihi.
An taƙaita hujjojin saboda sauƙaƙawa
Amma a duba :
. 1 ملخص الفقه الإسلامي، للدرر السنية
2. الفقه الميسر في ضوء الكتاب والسنة.

Like

Comment
Share

Gidauniyar MaiGemu Foundation ta yi wa marayu 3,000 dinkin sallah

Gidauniyar nan ta MaiGemu Development Foundation da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kankia a majalisar dokokin jihar Katsina Hon Salisu Hamza Rimaye ya assasa, ta sanar da yin dinkin sallah ga yara marayu su kimanin 3,000 a wannan shekarar ta 2024.
Kazalika, Gidauniyar ta kuma sanar da ba da hatsi ga magidanta su kimanin 2,000 da za su yi abincin sallah duk a karamar hukumar ta Kankia.
Bugu da kari, Gidauniyar ta MaiGemu Development Foundation ta sanar da ba da tallafin kudi masu tarin yawa ga masu karamin karfi, ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Kankia domin yin cefane da sauran hidindimun sallah da ke tafe.
Wanda ya assasa wannan Gidauniya, Hon Salisu Hamza Rimaye ya ce wannan bikin rabon kaya, shi ne karo na 7 a jere da ya assasa da ake tallafar marayu, masu karamin karfi da sauran mabukata su samu su gudanar da shagulgulan sallah cikin salama.
Ya ce ya yanke shawarar kafa wannan Gidauniya domin rage wa marayu da masu karamin karfi radadin halin matsin rayuwa da mafiyawansu ke shiga musamman idan lokuttan sallah sun gabato.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci taron hada mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawan Jobe, kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Hon Nasir Yahaya Daura, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Bala Abu Musawa da sauran su.

GWAMNA NAMADI YA DAKATAR DA KWAMISHINAN KASUWANCI, AMINU KANTA.

 GWAMNA NAMADI YA DAKATAR DA KWAMISHINAN KASUWANCI, AMINU KANTA.

Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar A Namadi, ya dakatar da kwamishinan kasuwancin jihar Alhaji Aminu Kanta har zuwa lokacin gudanar da bincike kan shirin ciyar war azumi a karamar hukumar Babura.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim.

Sanarwar ta ce matakin wani bangare ne na kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da bin diddigin kudi da kuma tafiyar da kudaden gwamnati kamar yadda aka saba,wadda take nuni da cewa zai cigaba da zama harsai an kammala bincike

A cewar samarwar an dakatar da Kwamishinan ne bisa zarginsa da hannu wajen karkatar da asusun ciyar wa ta buda baki a da gwamnatin ta kaddamar a cikin azumi a karamar hukumar Babura,

‘Yan ta’adda sun bude wuta a kasuwar Yantumaki sun kashe mutane

Wasu ‘yan bindiga da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun bude wuta a kasuwar Yantumaki da ke cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a ranar Juma’ar nan.
Majiyar DCL Hausa ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar nan, a yayin da ake tsaka da cin kasuwa, wasu kuma sun fara tafiya masallaci sallar Juma’a.
Bayanai sun ce an ga gawarwakin mutane biyu ciki hada wata mace da aka fasa wa kai har kwakwalwa ta fito.
Kazalika, bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce mutane da dama sun samu raunuka a yayin da suke gudun tsira da rayuwa. Sannan an yi asarar duniya mai tarin yawa.
Sai dai ‘yan bindigar ba su dauki dogon lokaci ba,  su na fara harbi ba kakkautawa suka ranta a na kare suka tsere, kafin jami’an tsaro su kawo dauki.
Kasuwar Yantumaki da ke cikin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina dai na ci ne a dukkanin ranar Juma’a ta kowane mako.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani daga hukumomi game da wannan batu.

Na ware N4.2m ga matasa masu amfani da soshiyal midiya su yi cefanen sallah – Engr Surajo Yazid Abukur

Tun bayan ganin wani rubutu na Aisha Mashi sai abubuwa da yawa suka dawo man sabbi a kwakwalwata.
Na fara tuna irin yadda matasanmu masu amfani da kafafen sadarwar na zamani suka rika taka muhimmiyar rawa wajen samar da kungiyoyi da take na Tallata manufofin Jami’iyyar APC a bangare na matasanmu sun shiga gwagwarmayar tallata manufar Jami’iyyar APC a karkashin taken *Mun Gani a Kasa Dikko Sabon Shafi* da *Masari ba Rabo da gwani ba* da sauran nau’ukan tallace-tallace da masu jawo hankali.
 Ko shakka babu masu amfani da kafar social media a wannan zamani su ne gishiri na siyasa, domin su ke taka rawa wajen saka siyasa ta yi armashi ko kuma akasin haka. Suna taka muhimmiyar rawa wajen yada ayyukan gwamnati da kuma kareta tare da tallata manufofinta gwamnatin Jami’iyyar APC da kudurorin ta. 
Wannan ya sa koyaushe nake gaza mantawa da ranar 5/12/2022 lokacin da tawagar yakin neman zaben Malam. Dikko Umaru Radda ta kaddamar da yakin neman zabe a garin Faskari da yawa daga cikin matasanmu masu amfani da wannan kafa suna daya daga cikin wadanda suka yi zandi suka isa wannan karamar hukuma aka fara kaddamarwa tare da su. 
Haka ma a ranar 11/12/2022 a garin Daura wajen yakin neman zaben Jami’iyyar APC, sai da na gana tare da zantawa da tarin matasan da ke amfani da kafafen sadarwar na zamani inda na kara masu kwara wa juna kwarin guiwa tare da jawo hankalinsu kan yadda za su cigaba da tallafawa wannan Jami’iyya ta APC wajen yada manufarta da kuma jawo hankalin mutane su zabeta. 
A wannan ranar mun ci abinci tare da su da kuma tattauna irin yadda jami’iyyar APC ke samun karbuwa.
Ranar 19/1/2023 ita ce rana da ta zama wani babin tarihi a game da matasanmu masu amfani da kafafen sadarwar na zamani domin a ranar tawagar yakin neman zaben gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Umaru Radda ta sauka garin Sabuwa. Na tafo da motata na iso garin Sabuwa na tarar da tawagar ta riga ta wuce wasu mazabu da ke da hatsarin shiga, ga kuma matasanmu masu amfani da wannan kafa a farkon garin Sabuwa duk an barsu, suna jira tawagar ta fito, daga zuwa na suka yi kuwwa “ga Kwamnada” nan take na amsa na yi Shahada na jagorance su muka shiga cikin daji domin tarar da tawagar dukkaninsu cikin bugun zuciya tare da karawa juna kwarin guiwa.
Wannan kokari na matasan media tabbas wani abun a yaba ne. Don haka ba za a taba mantawa da su ba, kuma muna tare da su kamar yadda mai girma gwamna ya zabi kusan mutum 70 daga cikinsu ya basu mukamai domin yabawa da kuma kara masu kwarin guiwa na ayyukan su.
Ina sanar da matasanmu masu amfani da wadannan kafafe cewa, gwamnatin jihar Katsina ba zata taba mantawa da su ba.
Amma dai ni a nawa bangaren zan zabi masu amfani da wannan kafar akalla mutane 200 in basu kudin cefane Naira dubu goma-goma (10,000) domin kara masu kwarin guiwa da kuma tabbatar masu da cewa muna tare da su dari bisa dari kuma mu da su duk abu daya ne.
Zan dauki mutane 25 masu taimaka wa gwamna a manyan ma’aikatun jihar nan da kuma mutane 11 masu taimakawa Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua sai mutane talatin-talatin (90) daga kananan hukumomi uku da suka kasance mazabata wato Rimi da Charanci da kuma Batagarawa.
Haka kuma zan zabi mutane goma-goma (20) daga shiyar Funtua da Daura wadanda suke amfani da wannan kafa. Sai mutane 21 fitattu daga shiyar Katsina ta tsakiya. Kazalika zan bayar da kudin cefanan ga mutane 10 da suka kasance abokai garemu da ke aiki a kafafen sadarwar na gwamnatoci da kamfanoni masu zaman kansu (Print and Broadcast media)
Sai kuma wasu kafafen sadarwar na zamani guda 10 da suka bayar da gudumuwarsu wajen ganin an kafa wannan gwamnati cikin aminci.
Kazalika suma iyayyenmu da suka dade a wannan kafa zan zabi goma daga cikinsu domin basu na cefanan Sallah na dubu goma-goma (10,000) domin kara masu kwarin guiwa.
Daga karshe suma wasu daga cikin shugabanin Jami’iyya ta ta APC a matakin karamar hukuma da Jiha na kananan hukumomina na Rimi da Charanchi da Batagarawa su 198 za su amfana da dubu goma-goma kudin cefane sai karin mutane shidda za su amfana da dubu hamsin- hamsin. Wanda jumullar kudin da za a raba baki daya zasu kama *Miliyan Hudu da dubu dari biyu da ashirin (N4,220,000)* 
 Muna fatan mu yi tawassali da ayyukanmu wajen rokon Ubangiji ya zaunar da Jiharmu da kasarmu lafiya, ya taimaki mai girma gwamna Malam Dikko Umaru Radda wajen tafiyar da gwamnatinsa lafiya, muna fatan ku saka mu a addu’o’inku Allah ya biya mana bukatunmu ya bamu dacewa da daren Lailaitul Kadari.
Insha Allah daren 27 ga watan Ramadana kowa zai samu kudin sa a asusun ajiyar da ya bayar ta hannun wadanda suka tuntube shi. Da fatan mun sha ruwa lafiya.

Farashin shinkafa ya fara karyewa a jihohi masu makwabtaka da Nijar

Shinkafar waje ta fara sauka a kasuwannin jihohin Kano da Katsina, inda a wannan makon aka saida buhun Shinkafar Baturen

N66,000 a Kasuwar Dawanau dake jihar Kano,wanda aka sai da N75,000 a makon da ya gabata.
 
Yayin da a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ake sayarwa N62,000 a wannan makon, amma a wancan satin N65,000 ne kuɗin buhun Shinkafa ‘yar waje a kasuwar.
Sai dai kuma Shinkafar wajen tafi tsada a kasuwannin jihohin Adamawa da Gombe da ke makwabtaka da juna, inda aka sayar da Buhun Shinkafar Baturen N82-83,000 a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe a wannan makon, yayin da a makon da ya shude kuwa aka sai da N75,000.
Ita kuwa kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, an sayar da shinkafar N75,000 a makon da ya gabata, to wannan satin ma dai hakan take, N75,000
Kuɗin Buhun Shinkafar waje.
A kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa kuwa, Kudin Buhun Shinkafar N80,000 ne a satin nan, a makon da ya wuce kuwa N78,000 aka sai da buhun.
An samu karin N3000 kan kudin buhun Shinkafar a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna a wannan makon, inda aka sayar da Buhun N78,000, a satin nan, a makon jiya kuma N75,000 ne Kudin buhun yake a kasuwar Giwa dake jihar Kaduna.
Shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a kasuwar Dawanau dake jihar Kano,an saida buhun N105,000 a makon nan,yayinda a makon daya gabata ake saidawa N110,000 a kasuwar,an samu sauƙin N5000 kenan a wannan makon.
 
Haka nan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma Shinkafar Hausan ta sauka,a makon nan a sayar da kowane buhu na shinkafar kan kuɗi N120,000, yayin da makon jiya kuma aka saya N130,000 daidai, ita ma dai an samu sauƙin N10,000,wanda ake danganta hakan da Faɗuwar darajar CFA a Kasuwannin Duniya.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuɗin buhun Shinkafar bai sauya ba daga N120,000 da aka sai da a makonni biyu da suka shude.
A jihohin Adamawa da Gombe kuwa Shinkafar ta sake tashi a wannan makon, inda a kasuwannin jihar Gombe ake sai da buhun shinkafar N135-140,000 a makon nan, sai dai a makon da ya gabata kuwa an sai da buhun N115-120,000, an dai samu karin N20,000 kenan a wannan satin.
A kasuwar karamar hukumar Girie dake jihar Adamawa kuwa,an sai da buhun shinkafar Hausa N143,000 a makon da ya gabata,haka nan aka sai da a makon nan dake shirin kare wa.
A kasuwar Giwa dake jihar Kaduna kuwa an samu kari kan kudin buhun Shinkafar a wannan satin,an sai da Buhun N130,000,yayinda a makon daya wuce aka saya N128,000.
Masara tafi tsada a wannan makon a kasuwar Kashere dake jihar Gombe,inda ake sai da buhun N60-65,000 a kasuwar,amma a makon jiya kuwa N60,000 cif ne kuɗin buhun masarar.
Ana sai dai buhun Masara N65,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a wannan makon,inda a wancan satin ake sai da buhun N63,000 ,an samu sassaucin N2000 kenan a satin nan.
N58,000 aka sayi buhun masara a kasuwar Dawanau dake jihar a wannan makon,haka batun yake a makon daya gabata ma.
Farashin buhun masara ya sauka a kasuwar Giwa na jihar Kaduna a satin nan,inda aka sai da buhun kan kudi N57,000,amma a satin da ya kare, kudin Buhun N62,000 ne.
Kuɗin Buhun Masara bai sauya zani a kasuwar Gombi dake jihar Adamawa,inda aka sai da buhun N59-60,000 a makon nan,haka nan aka sayar a makon daya shude.
Haka zalika, a kasuwar Mai’adua da ke jihar Katsina kudin buhun masara bai canza tufafi ba,an sayi buhun N62,000 a makon jiya,haka batun yake a wannan satin da ke yi mana bankwana.
Ga ma’abota cin Taliya kuma,taliyar yafi tsada a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna,inda ake sai da kwalin N14,000 daidai,sai dai an samu saukin N500 kan kudin na makon daya gabata,da aka sayar N14,500.
Sai dai fa Farashin kwalin taliyar a ko wani mako kara sauka yake a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a kudancin kasar,inda a makon nan aka sayi kwalin N13,500,bayan da makon daya wuce aka saya N14,000 daidai.
A kasuwar kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe,kuɗin kwalin taliyar N13,300 ne a makon nan,haka nan a satin daya gabata.
A kasuwar Dawanau dake jihar Kano ma kudin kwalin taliyar yana nan kamar yadda yake a makon daya shude,Inda aka saya N13,500,kuma haka farashin yake a makon dake dab da kare wa.
 
A kasuwar Mai’adua jihar Katsina an samu karin N500 kan farashin kwalin taliyar na baya,an sayi kwalin kan kudi 13,500 a makon daya shude,yayinda a satin nan kuma aka saya N14,000 cif-cif a Kasuwar.
To idan maka je kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa,an sai da kwalin taliya N13,200 a satin da ya kare ,haka yake a makon nan,N13,200 farashin taliyar.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.