Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 448

Dole ne aba wa al’umma kayan agaji domin ana fama da yunwa

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ce duk da cewa bai yarda da raba kayan abinci da tsabar kudi a matsayin tallafi ba, halin da ake ciki a yanzu yana bukatar irin wadannan matakan saboda mutane na fama da yunwa.

A wata hira da yayi da gidan Talabijin na Channels, Gwamna Sule ya jaddada mahimmancin magance matsalar yunwa tare da mai da hankali kan hanyoyin da za a bi don dogaro da kai. 

Yace bayar da horon sana’o’i da jarin aiki ga wadanda suka kammala karatu da manoma domin fara sana’o’insu yana da mutukar muhimmanci 

Gwamna Sule ya jaddada cewa koya wa mutane yadda ake kamun kifi maimakon a ba su kifi, yafi muhimmanci ga al’umma shiyasa suke baiwa bangaren mahimmanci.

Sai dai yace da ya zama wajibi a samar da abubuwan jin kai, musamman a lokutan da ake fama da matsananciyar yunwa kamar a wannan lokacin

Kotun CCT ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado daga shugabancin Anti – Corruption

 Kotun da’ar ma’aikata (CCT)  ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban hukumar karbar Korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a gaban kotu bisa zargin saba ka’idojin da’a na jami’an gwamnati, da cin hanci da rashawa,bayyana kadarorin karya, cin hanci da karbar kyaututtuka da dai sauransu.

Kotun ta amince da bukatar mai shigar da kara inda ta umurci wanda ake kara da ya sauka a matsayinsa na Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano bisa zargin saba wa tanadin kundin da’ar ma’aikata da kuma Kotu ta CAP C15 LFN 2004 da ke jiran sauraron karar.

Kotun kuma ta bayar da umurni ga Gwamnan Jihar Kano da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano da su dauki dukkan matakan da suka dace don nada jami’in da ya fi dacewa da zai karbi mukamin Shugaban riko na Hukumar Korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar. 

Ko da yake, wata majiya a gwamnatin jihar Kano ta shaida wa jaridar  SOLACEBASE cewa gwamnati za ta daukaka kara kan hukuncin saboda akwai umarnin kotu da ya hana gurfanar da shi, da kuma tsare-tsare na Code of Conduct Bureau, EFCC da sauran su.

Gidauniyar AA Kaura ta rarraba buhunan abinci 500 don bukukuwan sallah

Gidauniyar nan da ta shahara wajen taimakon masu karamin karfi da mabukata mai suna AA Kaura Foundation karkashin jagorancin Comrade Anas Abdullahi Kaura ta tallafa wa mabukata, marasa lafiya, dalibai, mata matasa da dai sauransu, da kayan abinci da sauran abubuwan bukata.
Gidauniyar ta ce ta samar da wannan tallafi ne domin tallafar al’umma su gudanar da hidindimun sallah a wadace.
Bikin rabon kayan da ya gudana a yau Alhamis 4 ga watan Afrilu, Gidauniyar ta kaddamar da raba sama da buhu dari biyar na kayan abinci ga magidanta domin shirye shiryen sallah karama da ke tafe.
Sannan kuma Gidauniyar ta raba wa matasa dari biyar kudi Naira dubu goma-goma 5million kenan domin rage radadin halin da ake ciki. Kazalika, akwai atamfofi sama da guda 500 da aka raba wa mata da kuma kudin dinki domin su fita shagalin sallah fes-fes.
Bugu da kari, sama da kungiyoyi 10 za su rabauta da tallafin Naira million biyu 2 million . Wasu daga cikin kungiyoyin sun hadar da..
1-AA Kaura Volunteer Organization
2-AA Kaura Media Connect
3- AA kaura Orphans and Less Privilege Group
4- Zamfara Support Organization
5- Women and Youths Empowerment
6-AA KAURA GRASS ROOT MOBILIZATION 
7-AA KAURA YOUTH AWARENESS FORUM
8- AA KAURA NE AKIDAR MU
9- ANASAWAN AMANA YOUTH MOBILIZATION
10- AA KAURA DOOR TO DOOR CAMPAIGN MOBILIZATION 
Sannan kowace local government matasan ta zasu Amfana da tallafin kuddi naira dubu Dari Dari A madadin maigirma ministan tsaro Dr. Bello Muhammad matawallen maradun
Da ya ke ganawa da manema labarai, bayan kaddamar da shirin, sakataren kungiyar Hon Sulaiman Sketch ya bayyana cewar dama sun saba yin wannan tallafin kuma dalilin yin shi ne domin rage wa alummah radadin a irin wannan yanayin da aka samu kai.
Sketch ya bayyana fatar sake yin irin tallafin da ya fi wannan a nan gaba.

‘Yan bindiga sun kona mota dauke da kudi a kauyen Katsina

Wasu ‘yan bindiga da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun banka wuta ga wata mota kirar Golf da ke dauke da ‘yan kasuwa na kauyen Mai Dabino da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.
Bayanan da DCL Hausa ta tattara sun ce motar na dauke da fasinjoji ne da za su tafi Kano domin saye-saye. Majiyar DCL Hausa ta ce ‘yan kasuwar sun yi nasarar ficewa daga cikin motar, amma kuma ba su iya samu suka tsira da kudade da kadarorin su da ke cikin motar ba.
Majiyar ta ce daga cikin fasinjojin akwai wani dan kasuwa da ya ke dauke da kudin da suka kai Naira dubu 300, da ya kulle don zuwa Kano sayayya musamman ganin yadda sallah ta gabato.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 7:30 na safe zuwa 8am a kan hanyar Mai Dabino zuwa Gurbi ta karamar hukumar Kankara a jihar.
Majiyar DCL Hausa ta shaida mata cewa yanzu hanyar Mai Dabino zuwa Danmusa a isa garin Yantumaki ta gagare su, shi ne suka koma bi ta hanyar Gurbi zuwa Kankara, nan ma ‘yan bindigar sun gano, sun fara tare su.
Majiyar ta ce ‘yan bindigar ba su yi nasarar tafiya da ko dan kasuwa daya ba, amma dai sun yi awon gaba da wani mutum dan asalin karamar hukumar Mani da ya je kauyen ziyarar ta’aziyya.
Majiyar ta ce lokacin da suka ji karar harbin bindiga, suka yi kokari suka juya suka koma da suka samu suka tsira da kyar, mota kirar Golf da ke gaba, ita ce ba a iya samu aka juya da ita ba sai dai mutanen ciki suka fita suka tsere, da barayin dajin suka zo, suka banka mata wuta.
Kan haka majiyar ta yi roko ga gwamnati da sauran hukumomin tsaro da su kawo musu daukin gaggawa ganin irin halin da suke ciki na rashin tabbas a yankin nasu.

Kwastam sun tattara Naira tiriliyan 1 a wata ukun farkon shekara 2024.

 Kwastam sun tattara Naira tiriliyan 1 a wata ukun farkon shekara 2024

Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya Kwastam (NCS) tace ta tara Naira Tiriliyan 1.3 a wata ukun farko na shekarar 2024 (Q1 2024), a cewar Kwanturola Janar din ta, Adewale Adeniyi.

Ya kuma ce hakan ba ya rasa nasaba da kwazon jami’an hukumar da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, ba ya ga dakile fasa kwaurin da kuma inganta harkokin kasuwanci.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a Abuja kan ayyukan hukumar, kwanturolan ya ce hakan ya nuna karuwar kashi 122.35 cikin 100 wanda ya zarce na shekarar 2023 inda hukumar ta samu N606.1billion.

A cikin wata ukun farkon wannan shekara hukumar NCS ta yi rawar gani wajen tattara kudaden shiga da jimillar kudaden da aka tattara a wannan lokacin sun kai NGN 1,347,675,608,972.75.

Kwantirolan ya jinjina wa jami’an hukumar bisa namijin kokarin da suka yi, ya kuma kara musu karfin gwiwa domin ci gaba da gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Tinubu ya sanya hannu kan kudirin dokar bawa dalibai rancen kudin karatu.

 Tinubu ya sanya hannu kan kudirin dokar bawa dalibai rancen kudin karatu.

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya sanya hannu kan kudurin lamuni ga daliban Nijeriya ya zama doka.

Hakan na zuwa ne bayan nazari da majalisar dattawa da ta wakilai suka yi na rahoton kwamitin kula da manyan makarantu da TETFUND ya gudanar.

Da yake jawabi bayan ya sanya hannu kan kudirin dokar, Tinubu ya ce babu wani dan Nijeriya ko wanene da za a cire daga cikin tsarin samar da ingantaccen ilimi.

Yace gwamnatinsu ta kuduri aniyar ganin an baiwa ilimi kulawar da ta dace, gami da shirye-shiryen bunkasa fasaha ta fannoni da dama.

an fito da wannan shiri ne domin tabbatar da cewa babu wani wanda komai talaucinsa da za a cire shi daga cin gajiyar wannan shiri,domin gina makomar matasan Nijeriya kamar yadda shugaban ya bayyana a fadarsa dake Villa.

An sanar da matar da ta fi kudi a duniya a 2024

An sanar da matar da ta fi kudi a duniya a 2024
Francoise Bettencourt Meyers ta zama macen da ta fi kudi a duniya a shekaru 4 jere.
‘Yar asalin kasar Faransa, Bettencourt na da shekaru 70 a duniya.

Ba mu ciyo sabon bashi ba – Gwamnatin Katsina

 Ba mu ciyo sabon bashi ba – Gwamnatin Katsina 

Gwamnatin jihar Katsina ta musanta ikirarin da ofishin kula da basussuka, DMO, ya yi cewa gwamnatin jihar ta ciyo sabon bashi.

A wani rahoto da Ofishin kula da basussuka ya wallafa kwanan nan ya bayyana cewa jihar Katsina karkashin Gwamna Radda tare da wasu jihohin Nijeriya sun karbo sabon lamuni, domin cike gibi da aiwatar da wasu ayyuka da za su yi.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Dikko Radda, Ibrahim Kaula Mohammed, ya aike wa DCL Hausa, ta musanta rahoton wanda ta ke cewa a halin yanzu jihar ba ta ciyo wani sabon bashi ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa babu wani sabon lamuni da gwamnatin Katsina a yanzu ta karba a karkashin Gwamna Radda amma wannan ba yana nufin gwamnatin jiha ba za ta ci bashi ba a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, za ta iya karbar bashi domin inganta rayuwar al’ummarta da ma jihar baki daya.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar na iya kokarinta wajen ganin ta bijiro da sabbin ayyuka da za su inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.

‘Yan sanda sun yi artabu da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Abuja.

 ‘Yan sanda sun yi artabu da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Abuja.

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya abuja, ta bankado maboya da hanyoyin da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin tsaunuka da dazukan da ke kewaye da Apo-resettled a Abuja.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, “Jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya abuja karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan, CP Benneth Igweh, sun kai farmaki kan tsaunukan da ke kewaye da shiyya ta A da B na Apo-resettlement, a ranar 1 ga Afrilu, 2024. , da misalin karfe 11 na safe, domin daukar wasu matakan tsaro a yankin, domin ana kyautata zaton hanyoyin masu garkuwa da mutane ne da kuma maboyar miyagu.

A cewar sanarwar, Igweh ya bukaci mazauna yankin da su sanya ido tare da kai rahoto ga ‘yan sanda da zarar sunga wani abu da basu yadda dashi ba.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa ko a watan Maris  rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kona maboyar masu garkuwa da mutane kusa da unguwar Awgbu da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa inda ta kwato bindiga kirar AK-47 dauke  da harsasai 50.

Sabon Shugaban kasar Senegal ya nada mai gidansa Fira Ministan kasar.

 Sabon shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya naɗa shugaban babbar jam’iyyar adawa, Ousmane Sonko a matsayin firaiministan ƙasar.

Ousmane Sonko dai shi ne ubangidan shugaba Faye a harkokin siyasa kuma an ɗaure su a gidan yari daf da zaɓen na watan Maris.

Amma daga bisani tsohon shugaban ƙasar Macky Sall ya yi masu afuwa, tare da wasu fursunonin siyasa.

Bayan ƴan sa’o’i kaɗan da hawansa mulki a matsayin shugaban ƙasar Senegal ne shugaba Faye ya naɗa Sonko a matsayin firaiminista,” fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na X.

Tun da fari dai an bayyana Sonko a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa amma bayan an kama shi ne sai aka yanke masa hukuncin cewa bai cancanci tsayawa takara ba – matakin da ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.