Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 449

Sabon shugaban Senegal da zai yi fito-na-fito da Faransa

 

Daga ranar 02 ga watan Afrilu na 2024, kasar Seengal ta samu savon shugaba Bassirou Diomaye Faye da zai shiga fadar gwamnati ta matansa biyu. 

 A cikin abubuwan da ya lashi takobin yaƙa, Bassirou Diomaye Faye, ya hadar  da zargin  ‘Ɗaurin talala’ da kasar Faransa ta yi wa tattalin arzikin ƙasarsa da ke Yammacin Afirka. Duk da cewa shuagaban Faransa Emmanuel Macron ya aike wa sabon shugaban da sakon taya murna, amma matashin bai janye alwashinsa na farko a yayin yakin neman zabe na cewa zai ceto kasarsa daga hannun Faransa a siyasance. 

Bassirou Diomaye Faye ya samu  kwarjinin cikin kankanin lokaci. Tsakanin nasararsa ta samu zama shugaban kasa da zaman gidan kaso, makonni 2 ne kacal, ya zama Daga wani gidan yari da ke Dakar zuwa fadar shugaban ƙasa.  Madugun adawar kasar Ousmane Sonko, ne ya  tsayar da shi ya maye gurbinsa a kasancewar shi Sonkon an haramta masa tsayawa takara. Faye da Sonko abokai ne na kud-da-kud, har ya raɗa wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan sunan Ousmane domin martaba abotarsu.

Rahoton bidiyo/murya: 

Bassirou Diomaye Faye da aka haifa a ranar 25 ga watan Maris na 1980 ɗan siyasar ƙasar Senegal ne kuma tsohon mai kula da lamurran haraji, shi ne  tsohon babban sakataren jam’iyyar PASTEF da aka rushe, matansa biyu sun hada da , Marie Khone Faye da Absa Faye. Marie Khone auren zumunci aka yi musu domin kuwa ‘yar uwarsa ce, kuma ta haifa masa ‘ya’ya huɗu, maza uku da mace ɗaya. Absa ba ta taɓa haihuwa ba.

Daye da shi da matansa biyu

A shekarar 2000, Faye ya yi jarabawarsa ta Baccalaureate kwatankwacin jarabawar WAEC a Nijeriya. Ya yi nasarar kammala karatun digiri na biyu a bangare karatun lauya sannan ya cinye jarabawar guda biyu, ya shiga makarantar koyon sha’anin mulki ta kasar ENA a takaice sai kuma majistare a 2004. Bayan ya kammala, sai Faye ya zaɓi zama jami’in haraji a sashen haraji da rukunin gidaje, inda abotarsu ta ƙullu da Sonko, wanda makaranta ɗaya suka yi.

A 2014, dangantakar Faye da Sonko ta yi ƙarfi, suka zama kud-da-kud a ƙungiyar haraji da rukunin gidaje wato Taxes and Estates Union da Sonko ya kafa.

Bayan kasancewa cikin halin rashin tabbas a tsayawa takarar Sonko a zaɓen na shugaban ƙasa. Jam’iyyar PASTEF ta zaɓi Faye a watan Nuwamba na 2023 a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen na 2024, duk da ana tsare da shi. Sai da an rushe PASTEF watannin baya, da ke nuna cewa yana takara ne a matsayin ɗan takara indifenda.

A ranar 20 ga watan Janairu na 2024, Majalisar Tsarin Mulki ta Senegal ta wallafa jerin sunaye na ƙarshe na ‘yan takarar shugaban kasa, kuma ba sunan Sonko a ciki. Bayan shari’a daban-daban, aka wanke Sonko cewa zai tsaya takara tun da kotu ba ta taɓa samun sa da wani laifi ba, kodayake yana ci gaba da zama a tsare. Dandanan Sonko ya sanar da goyon bayansa ga Faye a zaɓen.

A lokacin yaƙin neman zaɓe Faye ya ɗauki alƙawarin samar da ayyukan yi, ya yi yaƙin neman zaɓe ba ƙarami ba a kan zai yaki rashawa, ya kuma lashi takobin sake duba kwagilolin makamashi. Taken takararsa shi ne “Diomaye mooy Ousmane” da ke nufin “Diomaye Ousmane ne” a Wolof, kuma yake fatar kwarjini irin na Sonko da kuma samun karɓuwa da matasan Senegal za su ƙarfafa gangaminsa. Tsare-tsaren Faye sun yi kama da na Sonko a takarar da ya yi a shekarar 2019.

Shugaba Tinubu na Nijeriya tare da Faye

A ranar 14 ga watan Afrilu na shekarar 2023, aka kama Faye a lokacin da yake hanyarsa ta fita daga ofishinsa na haraji da ke a birnin Dakar. Daga nan a ka miƙa shi a hannun ‘yan sanda ana tuhumarsa da “yaɗa labarun ƙarya, da ƙin bin umarnin kotu, da ɓata sunan hukuma” biyo bayan wasu rubuce-rubucen da ya yi a soshiyal midiya. A wannan rubutu ya yi Allah wadai da rashin adalcin da ya ce ana aikatawa a tsarin shari’a na ƙasar. Ana ci gaba da haka aka ƙara wasu tuhume-tuhumen na ‘tunzura jama’a da tauye lamurran tsaro na ƙasa da suka sa aka tsare shi.

Bayan wani yunkuri da tsohon shugaban ƙasa Macky Sall ya yi a watan Fabrairu na ɗage zaɓukan, da dalilan ba a warware taƙaddamar wane ne zai tsaya kara ba, aka soma bore da zanga-zanga, inda Kotun  Tsarin Mulkin ƙasar ta soke ɗagewar.

Faye ya ce ya yi imani da tsari na sauyi da kuma gwagwarmayar kishin Afirka domin ƙwato ɗiyaucin Senegal, taken da wasu masu nazarin lamurra suka yi imanin manufa ce ta nesanta ƙasar da Turawan Yammacin Turai musamman tsohuwar ƙasar da ta musu mulkin mallaka Faransa

Akkufo-Addo tare da Faye

Faye ya ɗauki alƙawarin rage ƙarfi da ikon shugaban ƙasa, da maido da tsarin mataimakin shugaban ƙasa.

Tun kafin a zabe shi, Faye ya ce zai  fifita,  yaƙi da siyasar rashawa idan aka zabe sa matsayin shugaban ƙasa, inda ya ce babu wata ƙasa da za ta iya ci gaba idan rashawa da almunbazzaranci da dukiyar jama’a suka zama ruwan dare a kasar te Senegal mai mutane miliyan 18.

Shugaban Senegal mai kananan shekaru ya sha rantsuwar kama aiki

An rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban kasar Senegal mafi karancin shekaru a Talatar nan.
Sabon zababben shugaban kasar Sénégal Bassirou Diomaye Faye ya karbi rantsuwar kama aiki a gaban kotun kundun tsarin mulkin kasar.
Diomaye shine shugaban kasa na biyar a kasar ta Sénégal ya kuma gaji shugaba Macky Sall da ya mulki kasar daga shekarar 2012 zuwa 2024.

Ku sanar wa maniyyata kuɗin guzurin su cikin lokaci, kiran kungiyar IHR ga hukumar NAHCON

Kungiya mai zaman kanta da ke kawo rahotannin Aikin Hajji da Umrah, Independent Hajj Reporters, IHR, ta bukaci hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, da hukumomin jin dadin alhazai na jahohi da su sanar wa maniyyatan Hajjin 2024 ko nawa zasu karba a matsayin kudin guzirinsu.
Kungiyar ta ce ya zama wajibi a ja hankalin hukumar NAHCON da hukumomin alhazai na jihohi cewa kudin aikin hajjin 2024 da suka sanar kawo yanzu bai nuna adadin da za a bai wa maniyyatan a matsayin kudin guziri ba sabanin yadda aka saba yi tsawon shekaru.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar na kasa, Ibrahim Muhammed wanda aka rabawa manema labarai.
IHR ta ce a al’adance NAHCON na sanar da kuɗin aikin Hajji ne tare da baiyana guzurin da za a baiwa maniyyata, in da ta ce ana nufin hakan ne don baiwa mahajjata damar shirya tunaninsu kan nawa za su samu da kuma yin shirinsu na kudi yadda ya kamata.
“Misali, Alhazan 2023 sun biya N2.9m kuɗin Hajji, wanda ya hada da Dalar Amurka 800 kudin guzuri. Ƙididdigar kuɗin aikin Hajji ya ƙunshi abubuwan hidimar gida da na Saudiyya da za a yi wa kowanne mahajjaci.
“Sai dai daga baya hukumar NAHCON da ta gabata ta rage kudin guzurim na 2023 zuwa dala 700 saboda abin da suka bayyana a matsayin bambance-bambancen farashin tikitin jirgi. 
“Yanzu dai an sanar da kudin aikin hajjin bana ba tare da bayyana nawa ne kudin guzuri ba duk da an sanar da karin kudin aikin hajji,” in ji IHR.
Kungiyar ta ce ana baiwa mahajjatan kudin guzuri ne a ranar da za su tashi zuwa kasar Saudiyya a matsayin kudaden da ake kashewa a aljihunsu domin baiwa alhazai damar kula da wasu bukatu na kudi yayin da suke kasa mai tsarki.
“Muna kira ga NAHCON da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da su gaggauta sanar da nawa ne guzurin aikin hajjin 2024 ga maniyyata,” in ji IHR.

An samu wata fashewa cikin wani barikin sojoji da ke Lagos

 

Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da fashewar wani abu a barikinta da ke Ikeja a Lagos. Lamarin ya haifar da rudani ga mazauna barikin. 

Amma a sanarwar da mai magana da yawun rundunar soji ta kasa Manjo Janar Onyema Nwachukwu ta ce fashewar ba wata mai girma ba ce. 

Ya ce an samu hakan ne a wata gona da ke kusa da kasuwar Mammy da ke barikin na Ikeja, inda ake zargin wasu abubuwa da wani manomi ya binne a cikin gona suka haddasa fashewar.

Gwamnatin APC ce ta nemi bashin N20bn a jihar Zamfara ba ta PDP ba – Gwamnati

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar cewa jimillar kudin da ake magana N14.26bn ba ita ce ta ciyo bashin ba, ta gaje shi ne daga cikin bashin N20bn da gwamnatin da ta gabata ta nema wa jihar.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara Malam Sulaiman Bala Idris da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce babu wani bashi na cikin gida ko na waje da Gwamna Dauda Lawan Dare ya ciyo wa jihar tun da ya hau karagar mulki.
Sanarwar ta ce “muna son mu warware zare da abawa ga ofishin kula da basuka na Nijeriya DMO a rahoton da ya fitar cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ci bashin N14.26bn.
“Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Dauda Lawan Dare, ba ta taba neman bashi ko ma tunkarar majalisar jiha ko ta tarayya da zummar neman bashi ba.
“Na da matukar muhimmanci mutane su gane cewa gwamnatin da ta gabata ce ta nemi bashin zunzurutun kudi N20bn, amma ta gaza karbar kudin duka.
Sanarwar Malam Sulaiman Bala Idris ta ce gwamnatin da ta gabata ta karbi kudi N4bn daga cikin bashin N20bn da ta nema domin aikin filin jirgi na jihar Zamfara, amma ba ta yi abin da ya kamata da kudin ba.

Liman ya sauka daga aikin limanci saboda takaddamar kudi N500,000 a Kebbi

Babban malamin masallacin juma’a na Wala da ke Birnin Kebbi, Alhaji Rufai Ibrahim ya sauka daga mukaminsa sakamakon takaddamar N500,000 da ta shiga tsakaninsa da na’ibinsa, Malam Mamman Na Ta’ala Yahaya. 
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Alhaji Ibrahim ya kai karar Malam Yahaya ga hukumar DSS, bayan da ya zarge shi da yin cogen N500,000 daga cikin kudin da ya kamata su raba na kyautar kudin da gwamnan jihar ya ba su, lamarin da ya sanya aka dakatar da shi saboda rashin kai karar ga hukumomin da suka dace. Sai dai daga bisani ya rubuta aje aiki.

Talakawa sun fasa rumbun adana kayan abinci na gwamnatin jihar Kebbi da shagunan ‘yan kasuwa, sun kwasa

Wasu mazauna jihar Kebbi sun kai hari a rumbun adana kayan abinci na gwamnatin jihar da ke Bayan Kara cikin kwaryar Birnin Kebbi, inda suka kwashi kayan abinci.

Lamarin kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ya faru ne a daren Asabar.
Maharan da suka yi kukan-kura suka afka a rumbun, sun kuma fasa wasu shagunan ‘yan kasuwa, suka saci kayan abinci can ma.
Kazalika, sun kuma tare wata tirela makare da kayan abinci da aka ba gwamnatin jihar Kebbi ta kayan abinci, nan ma suka wawashi hatsi.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Muhammad Gwadangwaji, wanda shi ne shugaban ‘yan kasuwar na Bayan Kara Birnin Kebbi, ya ce matasan sun kuma banka wuta ga wasu rumbunan adana kaya ‘yan kasuwa.

APC ta dakatar da shugabar mata ta jam’iyyar a jihar Kaduna Maryam Mai Rusau

An dakatar da Maryam Mai Rusau daga jam’iyyar APC bayan hirarta da DCL Hausa

Maryam Mai Rusau dai ita ce shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar Kaduna.
A cikin hirarta da DCL Hausa, Maryam Sulaiman ta soki lamirin gwamnatin Sanata Uba Sani, bayan aka jiyo Gwamnan na cewa ya gaji tarin basuka daga hannun Malam Nasir El-Rufa’i. Basukan da suka jaza har ba su iya biyan albashi a halin da ake ciki.

Nijeriya za ta bude cibiyar rubuta jarabawar NECO a kasar Saudiyya

Hukumomi a Nijeriya sun sanar cewa ba da jimawa ba za a bude sabuwar cibiyar da za a rika zauna jarabawar karshe ta ‘yan sakandare ta NECO a kasar Saudiyya.
Hakan kuwa ya biyo kammala tantance cibiyar zauna jarabawar da ke makarantar Nigeria International School, Jedda kasar Saudi Arabia da karamin ministan ilmi Dr Yusuf Tanko Sununu ya jagoranci tawaga ta musamman don gudanar da wannan aiki. Daga cikin tawagar akwai Magatakardar hukumar shirya jarabawar ta NECO na Nijeriya Prof Ibrahim Wushishi.
A lokacin ziyarar, tawagar ta samu damar ganawa da hukumomin makarantar da duba duk abubuwan da suka kamata a mallaka kafin a bude cibiyar zauna jarabawar.

Daliban jami’ar Alqalam Katsina sun maka ta kotu

Wasu daliban jami’ar nan mai zaman kanta da ke Katsina, Alqalam University, su uku sun garzaya kotu, inda suke neman da a tilasta wa jami’ar ta tura sunayensu a jerin matasa masu yi wa kasa hidima na NYSC.
Daliban sun je babbar kotun jihar Katsina ne bisa zargin da jami’ar ta yi musu na cewa ba su biya kudin rajistar zangunan karatu hudu ba a jami’ar.
Daliban ‘yan gida daya, Hawwa’u Sani Barda, Rabi’atu Sani Barda da Hafsat Sani Barda sun samu takardar shaidar shiga jami’a ta ‘admission’ a zangon karatu na 2018/2019 da suka kammala a zangon karatu na 2022/2023.
Daliban dai sun yi ikirarin cewa jami’ar ta ki ta tura sunayensu a shirin hidimta wa kasa na NYSC, bisa hujjar jami’ar cewa, daliban ba su biya kudaden rajistar karatu ba.
A lokacin zaman kotun, lauyan masu kara Muhammad Mukhtar Lawal ya ce wadanda ya ke karewa sun zo kotu ne domin neman hakkinsu kamar yadda kundin mulkin kasa na 1999 ya tanadar.
Mukhtar Lawal ya ce takardar ta nemi izinin kotu domin a duba wannan shari’a.
Bayan gabatar da karar, Alkalin kotun, Mai shari’a Abbas Bawale, ya ce ya kamata masu karar su shigar da bukatar kotu ta aike sammace ga jami’ar domin lauyoyinta suma su halarci zaman shari’ar.
Sai dai Mai Shari’a Abbas Bawale ya ba masu karar damar yin nazari sosai a kan wannan karar, inda aka basu wa’adun kara shigar da karar wadda ta hada da bukatar kotu ta aikawa jami’ar takardar sammace.
Ya ce bayan haka za a bi hanyoyin da suka dace don isar da sammacen, daga nan kuma kotu ta sanya ranar da za’a fara shari’ar.