Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 450

Gwamnatin Kano ta yi ihsani ga maniyyata aikin hajji kan ƙãri da aka yi.

Gwamnatin jahar Kano ta yi wa maniyyata aikin hajji na jahar rangwamen Naira biliyan 1.453 daga cikin sabon ƙãrin da Hukumar Jigilar Alhazzai ta Najeriya ta yi ga maniyyata aikin hajji na bana.

Da wannan ko Wana maniyyaci a Kano zai samu sauki na Naira 500,000 kenan daga cikin sama da Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara da hukumar alhazan Najeriyar ta ƙãra a kan sama miliyan huɗu da suka riga suka biya.

Hukumar jigilar Alhazzai ta jahar Kano ta ce wannan rangwame ya shafi waɗanda suka biya kudin aikin hajji ta hannun ta ne kaɗai, kuma sun biya wani abu daga cikin kuɗin, wadda adadin su ya kai maniyyata 2,906 da sukayi rajista da hukumar dan aikin sauke faralin na bana.

Shugaban Hukumar Mahajjatan ta jahar Kano Alhaji Lami Ɗan Baffa a wani taron manema labarai ya ce sunyi wannan ihsani bisa la’akari da yanayin yau, saidai ya ce duk maniyyaci da ke da bukatar zuwa aikin hajjin na bana toh wajibi ya cika sauran Naira miliyan 1.918,032.91 kafin ƙarfe 11:59 na ranar 28 ga watannan na Maris da muke ciki.

Karin kuɗin na aikin hajjin bana ya zo wa wasu maniyyata bagtatan, abin da ya tilasta wa wasun su karɓar kuɗaɗen su da suka bayar tun farko, suka haƙura da zuwa kasa mai tsarki dan sauke faralin saboda babu yadda zasu iya cika wannan ƙãri da aka yi kuma ake buƙatar a biya cikin ƙanƙanin lokaci

.

Bashin da ake bin Nijeriya ya doshi Naira Tiriliyan 100 – NBS

 

Bashin da ake bin Nijeriya ya doshi Naira Tiriliyan 100 – NBS

Adadin bashin Nijeriya ya karu daga Naira tiriliyan 87.91 (dala biliyan 114.35) a sulusin shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 97.34 (dala biliyan 108.23) a rubu’in shekarar 2023.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana hakan a ranar Talata a cikin rahotonta da ta fitar.

Rahoton ya ce, basussukan da ake bin Nijeriya sun hada da bashin waje da na cikin gida, inda ya karu da kashi 10.73 bisa 100.

MTN za su yi karin farashin kudin kira da na data a Nijeriya

 MTN za su yi karin farashin kudin kira da na data a Nijeriya

MTN za su yi karin farashin kudin kira da na data a Nijeriya 

Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya fara wani yunkuri na karin farashin kudin kira da na sayen data ga kwastomominsa a Nijeriya. 

Matakin na zai faru ne sakamakon yadda Kamfanin ya sanar da cewa kudaden da ake tatsar show haraji da faduwar darajar Naira ne za su sanya ya dauke shi.

A wata kididdiga da Kamfanin ya yi ya sanar da cewa sun tafka mummunar asara sakamakon harajin Naira bilyan 137bn da suka biya.

Gwamna Dauda Lawal ya yi kira da a ƙara yawan sojoji zuwa jihar Zamfara.

 Gwamna Dauda Lawal ya yi kira da a ƙara yawan sojoji zuwa jihar Zamfara.

A ranar litinin ne gwamnan ya ziyarci babban hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa, a hedikwatar tsaro da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamnan ya gana da hafsan tsaro domin tattauna matsalar tsaro data addabi  jihar Zamfara.

Gwamna Lawal ya bayyana damuwarsa bisa yadda ‘yan bindiga suka addabi jihar,ya kuma yi kira ga babban hafsan hafsoshin tsaron kasar da ya tura ƙarin jami’an soji da kayan aiki na zamani da suka dace a jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa jihar tana fama da karancin jami’an tsaro ga kuma matsalar ‘yan bindinga masu garkuwa da mutane domin biyan kudin fansa,hakan yasa manoma ba sa iya noma gonakinsu, ga hare-haren da ake ci gaba da kaiwa na janyo asarar rayuka da dama.

Inda yace bisa wannan dalilai al’umma na shan wahala,domin kusan koyaushe ‘yan bindinga na kokarin kai hare hare a yankuna dadama,hakan yasa muke fatan cewa za’a duba koken mu domin samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Wasu daga cikin maniyyata a Nijeriya,sun nemi a maido musu da kudaden su.

 Wasu daga cikin maniyyata a Nijeriya sun bukaci da amayar musu da kudaden su da suka biya.

Biyo bayan matakin da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta dauka na kara  kudin aikin hajjin shekarar 2024 da naira miliyan 1.9, da dama daga cikin mahajjatan j sun bukaci hukumar jin dadin alhazai ta jihar da ta mayar musu da kudaden da suka ajiye.

Wannan dai na zuwane a daidai lokacin da  kungiyoyin fararen hula da masu ruwa da tsaki a Nijeriya, suka yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dubi halinda maniyyata hajji bana ke ciki don samun mafita.

A ranar Lahadin da ta gabata ne NAHCON ta kara kudin aikin hajjin bana zuwa kasar Saudiyya da N1, 918,032.91 yayin da ta tsayar da ranar 28 ga Maris, 2024 a matsayin ranar da za’a kammala biyan wannan kudi.

 A watan Disambar shekarar 2023 ta kayyade farashin hajjin bana da Naira miliyan 4.9 bisa tashin farashin canji.

Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata, hukumar ta bukaci wadanda suka biya kudin farko da su kara Naira miliyan 1.9, inda adadin ya kai Naira miliyan 6.8.

Wannan yasa wasu daga cikin maniyyatan suka bukaci Hukumar Kula da aikin hajji ta jihohi da su mayar musu da kudaden da suka biya a baya.

Kotu ta yankewa dan chana hukuncin kisa ta hanyar tayaya.

 Babbar kotun jahar Kano, ta yanke wa FrankGeng Quarong hukuncin kisa ta Hanyar rataya har sai ya mutu.

Tun a ranar 16  ga watan satumba 2022,  Frank Geng, ya hallaka ummita a Unguwar janbulo dake Kano.

Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji yanke masa hukuncin ne bayan tabbatar da hujjojin da Masu gabatar da Kara suka yi agaban kotun.

Akwai bukatar Shugaba Tinubu da gwamnoni su kawo daukin gaggawa a karin kudin aikin hajjin 2024 – IHR

Kungiyar sa kai da ke kula da ayyukan hajji da Umrah ta Independent Hajj Reporters IHR ta bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai da u sa baki don kawo daukin gaggawa don gudun samun karancin mahajjata a aikin hajjin shekarar 2024.
A daren Lahadin nan dai ne hukumar kula da aikin hajjin Nijeriya ta sanar da karin kudin aikin hajjin shekarar 2024.
A cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar ta IHR Alhaji Ibrahim Muhammad da ya aike wa DCL Hausa ta ce kusan kaso 90% na maniyyatan da suka biya kudinsu 4.9m ba su da ikon biyan karin wasu kudi har 1.9m a cikin kwanaki hudu kacal.
A kan haka ne, kungiyar ke kira da babbar murya ga gwamnoni da gwamnatin tarayya da su shiga cikin lamarin don tallafar tsarin don biyan cikon ga maniyyata a matsayin wani tallafi na musamman.
Sanarwar ta buga misali da cewa ko a jihohi za a dauki lokaci mai tsawo kafin ma sakoneya isa ga maniyyatan da suka biya kudinsu ganin cewa Mafi yawansu manoma ne, sannan hakan na iya daukar wani karin lokaci matsakaici kafin maniyyaci ya iya tara kudin da suka kai N1.9m cikin wannan lokaci.

Gwamnan Katsina Dikko Radda ya fitar da zakkar Naira milyan 10

Hukumar da ke kula da Zakka da Wakafi ta jihar Katsina ta sanar cewa ta samu zakkar jimillar kudi Naira milyan 12 daga daidaikun mutane a jihar.
A ta bakin shugaban hukumar Dr Ahmad Musa Filin Samji, hukumar za ta rarraba wadannan kudade ga mabukata da sauran masu karamin karfi a lungu da sako na jihar.
Dr. Ahmad Filin Samji ya ce daga cikin mutanen da da suka ba da wannan Zakka, hada gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda da ya fitar da zakkar kudi ta Naira milyan 10 kuma ya hannanta ta ga hukumar don raba wa mabukata a fadin jihar.
Ya ce da farko Gwamnan bai so a ambaci ya ba da zakkar ba, amma ya nusar da shi cewa Musulunci ya amince a rika sanarwar domin a zaburar da wadanda ba su da niyyar badawa su ji suna so su bayar.
Ya ce hukumar ta yi nasarar dawo da batun hadaya, wato dabbar da ake yankawa idan an kammala aikin hajji a kasar Saudi Arabia da za ta rika kula da shirin don tsaftace ba Alhazai damar kammala aikin hajjinsu yadda ya dace.
Shugaban hukumar ya ce sun gabatar da bukata ga majalisa dokokin jihar Katsina domin ta sa baki a kafa dokar da za ta ba da damar a rika lura da shaidar biyan Zakka ga duk wanda ke neman wani mukami.
Dr Ahmad Musa hukumar da ta fara aiki watanni uku da suka gabata a jihar Katsina, ta yi nasarar kafa ayyukan ‘waqafi’ masu tarin yawa da zummar amfanar da al’ummar jihar musamman mabukata.
Daga cikin ayyukan akwai gina gidajen marayu 38 da yanzu haka marayu 280 na cikin wadannan gidaje.

Tinubu ya gwangwaje Kanawa da kyautar kayan abinci

 Gwamnatin tarayya ta tallafama jihar Kano da tireloli na hatsi domin rabawa ga mabukata a wannan wata na Ramadana.

Tallafin ya kunshi tireloli na shinkafa 100, tirelolin dawa 44, da kuma tirela na masara guda hud

u.

Babu dan da na haifa da zan bari ya shiga aikin soja, in ji matar Kanal din soja da aka kashe a Delta

Malama Hawwa Ali, matar marigayi Lt Col Ali A.H ta ce daga cikin ba za ta bar ko da daya ya shiga aikin soja ba.
Malama Hawwa dai ta ce ta yanke wannan shawarar ne biyo bayan kisan gilla da wasu mutane suka yi wa mijinta a kauyen Okuama na jihar Delta.
Matar marigayin ta ce mijinta dai ya rigaya ya ba da rayuwarsa don ci gaban Nijeriya. 
Idan za ku iya tunawa dai, gwamnatin Nijeriya da rundunar sojojin kasar ta samu labarin mutuwar jami’anta 17 a ranar 14 ga watan Maris, 2024 biyo bayan wani kisan gilla da ake zargin al’ummar kauyen Okuama na jihar Delta sun yi musu.
Da jaridar Daily Trust ta tambayi Malama Hawwa ko za ta bar ‘ya’yanta su shiga aikin soji, ta kada baki ta ce ba za ta bari wani daga cikinsu ya shiga ba, mahaifinsu dai ya yi, kuma ya ba Nijeriya rayuwarsa.
Ta ce ba za ta iya mantawa da shi a rayuwarta ba, kasancewarsa mutum kamili mai sanin ya kamata da fita hakkin iyalai da iyayensa.