Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 451

Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto daliban Kuriga gaba dayansu

A cikin wata sanarwa da Gwamna Uba Sani ya sanya wa hannu, ta yi godiya ga shugaban kasa da jami’an bisa abin da ya ce namijin kokarin da suka yi na ganin an kubutar da daliban ba tare da sun yi ko kwarzane ba.

Duk da dai a sanarwar, Gwamnan bai yi bayanin hanyoyin da aka bi aka ceto daliban ba, amma ya ci gaba da godiya har ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da sojoji da daukacin al’ummar Nijeriya da suka yi ta addu’o’in ganin daliban sun kubuta.
A ranar 7 ga wannan wata na Maris ne dai ‘yan bindiga suka shiga makarantar firamaren garin Kuriga na karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna suka yi awon-gaba da dalibai kusan 287.

ECOWAS ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa sojojin Nijar da ya yi sanadiyar rasa rayukan 23 daga cikin su

A cikin wata takarda ce da ta fitar a ranar 23 ga watan nan na Maris, kungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin dadin ta da takaici kan harin baya bayan nan a Nijar wanda ya yi awan gaba da rayukan sojojin kasar 23 
Kungiyar ta ce tana isar da sakon ta’aziyar ta ga gwamnati da al’amurar kasar Nijar tare da jaddada goyan bayan ta ga ‘yan uwan mamatan da sojojin kasar
Kazalika sanarwar ta ce kungiyar na fatan kwanciya ta zama hutu ga wadanda suka kwanta damar tare da fatan manzon sauki ga wadanda suka jikkata
A karshe kungiyar cikin kakkausan kalamai ta ce tana tir da Allah wadai da wannan hari na dabbanci ta kuma tabbatar wa hukumomin na Nijar aniyarta ta bada hadin kai wajen yaki da ta’addanci da kuma tsatsaurar ra’ayi a yankin

Kisan Sojin Nijar: ECOWAS ta mika wa Janar Tiani goron gayyatar hada gwiwar yaki da ta’addanci

 


Daga wakilinmu, Yacouba Maigizawa, Damagaram-Nijar

Kungiyar ECOWAS ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa sojojin Nijar da ya sanadiyar rayukan 23 daga cikin su

A cikin wata takarda ce da ta fitar a ranar 23 ga watan nan na Maris, kungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin dadin ta da takaici kan harin baya bayan nan a Nijar wanda ya yi awan gaba da rayukan sojojin kasar 23 

Kungiyar ta ce tana isar da sakon ta’aziyar ta ga gwamnati da al’amurar kasar Nijar tare da jaddada goyan bayan ta ga ‘yan uwan mamatan da sojojin kasar

Kazalika sanarwar ta ce kungiyar na fatan kwanciya ta zama hutu ga wadanda suka kwanta damar tare da fatan manzon sauki ga wadanda suka jikkata

A karshe kungiyar cikin kakkausan kalamai ta ce tana tir da Allah wadai da wannan hari na dabbanci ta kuma tabbatar wa hukumomin na Nijar aniyarta ta bada hadin kai wajen yaki da ta’addanci da kuma tsatsaurar ra’ayi a yankin

‘Yan bindiga sun harbi mutane biyu a Mairuwa jihar Katsina ana tsaka da sallar ‘taraweeh’

Wasu mutane dauke da muggan makamai sun kai hari a kauyen Mairuwa na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a cikin daren Asabar din nan.

Bayanan da DCL Hausa ta samu sun nuna cewa maharan sun harbi wani fitaccen mutum a garin mai suna Alhaji Lado har hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Majiyar DCL Hausa ta ce maharan da suka zo a kan babura, sun kai samamen ne a masallaci a daidai lokacin da mutane ke sallar ‘asham’ inda suka harbi Alhaji Lado da karin wani mutum.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, babu tabbacin maharan ko sun tafi da wasu mutane ko a’a.
Yanzu haka dai mutanen garin na cikin razani bayan faruwar wannan lamari cikin wannan dare.

Saukar farashin Dala ya sa wasu kayan abinci sun fara sauka a Nijeriya

Farashin kayan abinci na ci gaba da sauka a wasu daga cikin kasuwannin sassan Najeriya, inda a makon nan aka sayi buhun masara ₦52-53 a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe.
Idan baku manta dai a makon da ya shuɗe an sayar da buhun masarar ₦58,000 a kasuwar, a wannan makon an samu sauki ko ragowar ₦5,000 kenan.
Ita ma dai kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, farashin na wannan makon ya sauka, a makon da ya gabata an sayi buhun masara ₦68,000, sai dai a makon nan ₦65,000 ne kudin buhun masara a kasuwar, an samu ragowar Naira 3,000.
Idan muka je kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma an dan samu sassaucin ₦1000 kan farashin makon da ya shude, inda aka sayar da buhun masara ₦58,000 a makon da ya gabata, yayin da makon nan kuwa aka sayi buhun kan kudi ₦57,000 daidai.
Sai dai fa, farashn buhun masarar bai sauya ba a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da ke Arewacin kasar Najeriya, inda aka sayar da buhunta kan kudi ₦64,000 a wancan makon, haka nan a wannan makon ma.
To a kasuwar Giwa a jihar Kaduna ma an samu sauƙi kan kuɗin buhun masarar na baya da aka sayi buhun ₦60,000 cif a makon da ya wuce, amma a makon nan kuɗin Buhun ₦57,000 ne, ma iya cewa an samu sauƙin ₦3000 kenan a satin nan da ke shirin karewa a kasuwar Giwa a jihar Kaduna.
A kasuwa Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, kuɗin buhun masarar bai canza tufafi ba a wannan makon, an sayi buhun masara kan kuɗi ₦59-60,000, haka kuwa aka saida a makon nan ma.
Shinkafar Hausa ta yi tashin gwauron zabi a kasuwar karamar hukumar Gerie da ke jihar Adamawa. A makon nan, an sayi buhun shinkafar ₦139,000, yayin da a makon da ya gabata kuwa aka sayar ₦127,000, an samu karin N12,000 gabadaya.
Hakazalika, shinkafar Hausar ta ɗan haure a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da aka sayar ₦130,000 a ‘yan kwanakin nan, amma a makon nan kuma ₦128,000 farashin shinkafar.
A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano buhun shinkafa ‘yar gida ta sauka a makon da ke dab da ƙarewa, inda aka sayar da buhun shinkafar ₦120,000, amma a satin da ya kare aka sayar ₦130,000, wanda hakan ke nuni da cewa an samu sauƙin ₦10,000 kenan a makon nan.
Sai dai shinkafar ta sauka a kasuwar Mai’adua a jihar Katsina, a wannan makon an sayi buhun shinkafar ₦125,000, saɓanin farashin na baya da aka sayar ₦130,000 daidai.
Ita ma kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, shinkafa ‘yar gida ta fi sauki a makon nan sama da makon da ya wuce, an sayi buhun shinkafar ₦108-110,000, haka nan akwai na ₦115,000, sai dai a makon jiya kuwa ₦115,000 ne -120,000.
Ita kuwa shinkafar bature ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, inda aka sayi buhun shinkafar ₦72,000 a makon nan, sai dai a makon da ya gabata aka sayar kan kudi ₦75,000.
Amma shinkafar wajen ta fi tsada a makon nan a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna da aka sayar ₦78,000 a baya, sai dai a satin nan ₦80,000 ne kuɗin buhun shinkafar.
A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma dai Farashin shinkafar waje na wannan makon ya sauka, inda aka saida ₦83,000 a satin nan, amma a makon da ya shude ₦87,000 kudin buhun, wanda ake danganta hakan da saukar Dala da a kwanaki ta yi tashin gwauron zabi.
Ita ma dai Jihar Gombe ba a barta a baya ba wajen saukar farashin shinkafar baturen, a makon da ya gabata an sayi buhun shinkafar ₦82-85,000, yayin da a makon nan kuwa aka saya ₦80,000 daidai.
Taliyar Spaghetti dai ta fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos, sama da sauran kasuwannin Arewacin Nijeriya, inda ake sayar da kowane kwalin taliyar ₦15,000 a wannan makon, haka ma a makon da ya gabata.
Har ila yau, taliyar ta fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da a makon nan aka sayi kwalin, N13,200, yayin da a wancan makon aka saida N13,5000 .
Haka nan, a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma ,taliyar ta fi tsada a wancan satin da ake saidawa N15,000, amma yanzu N14,500 ne kuɗin kwalin taliyar a makon nan.
A kasuwannin jihohin Kano da Katsina ma kuɗin kwalin taliyar bai sauya ba, inda ake sayar wa N13,500 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, haka kuma aka saya a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma.
Sai dai taliyar ta yi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, a satin nan ana sayar da kwalin Spaghetti N13,000 daidai, bayan da a makon da ya gabata aka sayar N13,200.
Ga maciya doya kuwa, a wannan makon an sayar da kwaryarta kan kudi Naira 350,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke Ikko.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.

Buhari yayi yunkurin rufa wa Nyako asiri kan zargin almundahana

 

Tsohon Ministan Shari’a na Najeriya Micheal Aondoaka ya baiyana wa kotu cewa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi rufa-rufa kan zargin badaƙala ta Naira biliyan 29 da ake ga tsohon gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako tun bayan saukar sa a mulki a shekarar 2015.

An sake gurfanar da tsohon gwamnan na Adamawa da ɗansa Abdulaziz Nyako Alhamisɗinnan a wata babbar kotu da ke Abuja bisa zargin yin sama da fãdi da Naira biliyan 29, zargin da aka fara shari’a kansa tun ranar 8 ga watan Yulin shekarar 2015.

Tsohon ministan shari’an ya fadawa alkali, mai Shari’a Peter Lifu cewa, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci tsohon ministan shari’a na lokacin sa Abubakar Malami ya nemi hanyar sasantawa da hukumar EFCC dan ganin a janye wannan ƙãra.

EFCC dai tana tuhumar Nyakon da ɗansa, da kuma wasu guda biyu Zulƙifik Abba da Abubakar Aliyu da wasu Kamfanoni guda uku Blue Opal Ltd, da Tower Assets Management Ltd da kuma Crust Energy Ltd da laifuka 37 da suka hada da zargin sãta, hadin baki da kuma yin karan tsaye ga dokokin aikin ofis.

Ban yarda da zargin da gwamnatin Tinubu ta yi ga waɗannan bayin Allah ba

Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi yana ƙalubalantar gwamnatin Najeriya bisa zargin wasu da aka fitar da jērin sunayen su cewa suna da hannu dumu-dumu a ayyukan ta’addanci a ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar da ke tattara bayanan sirri kan ilahirin harkokin da suka jībanci kudade a faɗin ƙasar, ta fitar da bayanai dake nuni ga wasu ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni har ma da masu harkar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare da hannu wurin tallafawa ayyukan ta’addanci, musamman da kuɗaɗe.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce jami’an tsaro basu da hurumin aiyana wani a matsayin mai tallafawa taaddanci da kuɗaɗe saboda a cewar sa ‘yan ta’addan su ke ɗaukar nauyin kansu da kansu, ta amfani da kuɗaɗen fansa da suke samu idan suka yi garkuwa da mutane.

Malamin addinin a baya-bayanan ya bukaci gwamnatin Najeriya ta basu damar tattauna wa da yan ta’adda da suka sãce ɗalibai kusan ɗari uku garin Kirga dake jahar Kaduna, saboda da yace da alama abin zai yi matuƙar wahala ga jami’an tsaro, yana mai cewa bai kamata a  zuba idanu ana gani shugaba Tinubu ya maimaita irin kurakurai da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yai ba, na ƙin yin sulhu da ‘yan fashin na dãji.

Tinubu ya haramta wa ministocinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare

 

Tinubu ya haramta wa ministocinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umurnin haramta wa ministocinsa da sauran mukarraban gwamnatinsa tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.

Shugaba Tinubu ya ba da umurnin ne ta cikin wata wasika da shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, ya aike wa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

A cikin wasikar, mai kwanan wata 12 ga Maris, 2024, Tinubu ya ba da umurnin hana duk wasu  tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.

Sai dai ya ce an keɓance tafiyar da ta zama wajibi.

NDLEA ta gana da masu Otal a Katsina don dakile safarar miyagun kwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta jihar Katsina ta sanar da ganawa ta musamman da masu otal-otal a jihar don tattauna yadda za a dakile safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Kwamandan hukumar Hassan Sani Abubakar a cikin wata sanarwa, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa a hankalin a hankali mutane na amfani da otal-otal domin gudanar da haramtaccen kasuwancin cinikin muggan kwayoyi.
Kwamandan a sanarwar da kakakin hukumar Bashir Adamu ya aike wa DCL Hausa, ya ja kunnen cewa hukumar ba za ta yi kasa guiwa ba wajen kakkabowa tare da zakulo wadanda ke da hannu a wannan batu don hukunta su daidai da doka.
Ya ce za su yi duk mai yiwuwa don ganin otal-otal a jihar Katsina ba su zamo mafakar masu haramtaccen kasuwancin miyagun kwayoyi ba.

‘Yan sanda sun dakile yunkurin satar wata mata da mijinta a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cewa ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da miji da mata a kauyen Hayan Dam na karamar hukumar Kankara ta jihar.
A cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq ta ce babban ofishin ‘yan sandan karamar hukumar Kankara ya samu labarin cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da muggan makamai sun mamaye gidan Kabir Magaji da zummar yin garkuwa da shi da matarsa Sa’adatu Magaji.
Bayan samun wannan bayani, ‘yan sanda suka gaggauta kai dauki, suka dakile yunkurin, yanzu haka su na kokarin kama wadanda ake zargi.
Sanarwar ta shawarci al’umma da su ba da bayanai ga duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga ganin yadda wasu ‘yan ta’addar suka sha da kyar da raunuka a jikinsu.