Katsina za ta karbi bakuncin taron inganta tsaro da zaman lafiya na shiyyar arewa maso yamma
Kullum sau biyu nake magana da shugaba Tinubu kan matsalar tsaro – Uba Sani
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce a kowace rana yana magana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sau biyu yana bayyana masa halin matsalar tsaro da ake fama da ita a jihar.
Uba Sani ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels TV a Siyasar Yau.
A ranar 8 ga Maris, ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar firamare da karamar sakandare ta LEA, Kuriga sannan suna ci gaba da kai hare-hare a yankunan jihar daban-daban
Gwamnatin Nijeriya ta roki kungiyoyin SSANU da NASU su janye yajin aikin gargadi
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyoyin manyan ma’aikatan jami’o’in kasar, SSANU, daNASU, da su janye yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da suka fara gudanarwa a ranar Litinin.
Karamar ministar kwadago da samar da nagartar aiki Nkeiruka ce ta yi wannan roko a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Olajide Oshundun a ranar Litinin a Abuja.
Idan dai ba a manta ba kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin biyu wato SSANU da NASU sun umurci mambobinsu da su shiga yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai kan rashin biyansu albashin watanni hudu da suke bin gwamnati bashi.
Gwamnan Akwa Ibom ya ki a sanya kwai a jerin kayan abincin da za a saukaka farashin su
Gwamnan Akwa Ibom ya ki a sanya kwai a jerin kayan abincin da za a saukaka farashin su
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ki amincewa da bukatar a sanya “kwai” a cikin kayan abincin da gwamnatin jihar za ta sayar wa marasa galihu a kan farashi mai rahusa.
Gwamnan ya nuna kin amincewa ne a yayin wani gagarumin taron Majalisar Zartarwa na Jiha, inda ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar saye da sayarwa.
‘Yan Najeriya na fuskantar mawuyacin hali yayin da farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi bayan cire tallafin man fetur da shugaba Bola Tinubu ya yi.
APC ta zabi Idahosa a matsayin mataimakin gwamnan Edo a zaben da yake gabatowa
APC ta zabi Idahosa a matsayin mataimakin gwamnan Edo a zaben da yake gabatowa.
Jam’iyyar (APC) ta tsayar da Hon. Dennis Idahosa a matsayin mataimakin dan takarar gwamna a zaben gwamnan Edo da za a yi ranar 21 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki.
Shugaban jam’iyyar APCn na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da sakataren jam’iyyar na kasa, Sen. Ajibola Bashiru za su gabatar da Sanata Monday Okpebolo, a matsayin dan takarar gwamnan da kuma abokin takararsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a villa dake Abuja.
Idahosa shine ya maye gurbin Hon. Omoregie Ogbeide-Ihama wanda dan takarar gwamnan ya bayyana a makon da ya gabata a matsayin abokin takararsa.
Jaridar Nation ta rawaito cewa Idahosa, dan majalisar wakilai, an tabbatar dashi a daren ranar Lahadi bayan wani dogon zama da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Edo, da shugabannin jam’iyyar da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima suka yi.
Sheikh Ibrahim Khalil ya bukaci gwamnan Kano ya bada murja kunya a matsayin mataimakiya ta musamman.
Shahararren Malamin Addinin Musulunci ya bukaci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada, Murja Kunya a matsayin mai Taimakawa gwamnan ta musamman a Social Media.
Sanannen malamin addinin musulunci, Sheihk Ibrahim Khaleel, ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya nada , Murja Ibrahim Kunya yar Tik Tok,a matsayin babbar mataimakiya ta musamman kan kafafen sadarwa na zamani.
Sheikh Khalil ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin da ta gabata a cikin wani shiri da yagabatar a tashar Freedom Radio da ke Kano.
Malamin yace yin hakan zaitamakawa gwamnati da al’umma kwarai da gaske wajen,tallafawa mata musamman yan social media ta yadda za’a fito da sabbin hanyoyin kasuwanci na zamani da zai taimaka ta shafukan sada zumunta.
A kwanakin baya ne Hukumar hisbah ta jihar kano ta gurfanar da murja Ibrahima a gaban wata kotun shari’ar Musulunci karkashin jagorancin Nura Yusuf Ahmad ta bayar da umarnin cewa, Murja Ibrahim Kunya a kaita asibiti domin ayimata gwajin tabin hankali a wani asibitin gwamnati domin sanin halin da take ciki.
Farashin kayan abinci ya ki sauka duk da rahusar da Dala ta fara yi a Nijeriya
Farashin kayan abinci ya kara kara ta’azzara a makon farko na azumin Ramadana, domin kuwa a makon jiya, masara ta fi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, inda ake sayar da buhun kan kudi ₦56-57,000, amma a wannan makon kudin buhun masarar ya koma ₦58,000.
Kwastam sun mika wasu motoci 6 makare da abinci ga masu kayan
Kwastam sun mika wasu motoci 6 makare da abinci ga masu kayan
Hukumar Kwastam ta Jihar Katsina ta hannanta wasu manyan motoci guda shida makare da kayan abinci ga masu su kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya ba su umurni.
Motocin da aka mika su ga masu su an tare su ne a shingen binciken kan iyakar Kongolam da ke karamar hukumar Mai-Adua a jihar Katsina.
Shugaban ya bayar da umurnin ne da nufin tabbatar da an samu wadatar abinci da kuma rage wahalhalun da akasarin ‘yan kasar ke fuskanta.
Jam’iyyar PDP na son a yi bincike kan zargin cushen N3.7trn a kasafin 2024
Jam’iyyar PDP na son a yi bincike kan zargin cushen N3.7trn a kasafin 2024
Jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta bukaci a gudanar da bincike kan zargin cushen kudi N3.7trn a kasafin kudin 2024.
Jam’iyyar ta PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a Abuja.
Ologunagba ya ce binciken zai taimaka wajen gano abubuwan da suka sa aka dakatar da Sen. Sanata Abdul Ningi (PDP-Bauchi) da Majalisar Dattawa ta yi, yana mai cewa an dakatar da Ningi ne ba tare da yin cikakken bincike kan kasafin kudin da ake zargin sa ba.







