An samu Gidauniyar da ta yi karo-karon kudi sama da Naira Milyan 140 don tallafa wa gajiyayyu cikin watan Ramadan a Kano
Gwamnatin Kebbi ta rage sa’o’in aiki ga ma’aikatan gwamnatin jihar
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnatin jihar a cikin wannan watan na Ramadan.
Kwamishinan ma’aikatar fansho da horaswa na jihar Auwal Manu-Dogondaji ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Birnin Kebbi a yau Talata.
Ya ce matakin zai baiwa ma’aikatan gwamnati damar gudanar da ibada cikin sauki.
Majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Ningi bisa zargin karkatar da kasafin kudi
Majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Ningi bisa zargin karkatar da kasafin kudi
Majalisar dattijai ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku bisa zargin cusa Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin 2024.
Ningi shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan al’umma kuma yana wakiltar Bauchi ta Tsakiya.
Akwai yiyuwar sojojin Nijar su saki Bazoum a Azumin nan
Akwai yiyuwar sojojin Nijar su saki Bazoum a Azumin nan
Gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta ce a shirye take ta amince da sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da matarsa Khadija.
Majiyoyi da dama a Nijeriya da makwabciyarta Nijar, sun tabbatar da shirin gwamnatin mulkin soja na sakin hambararren shugaban kasar a cikin ‘yan kwanaki nan na watan Ramadan.
Sai dai an gano cewa babban abin da ke damun manyan jami’an soji a jamhuriyar Nijar shi ne nacewar Bazoum na cewa zai ci gaba da zama a cikin kasar ta Nijar, bisa dalilin cewa ba ya sha’awar komawa wata kasa daban don ci gaba da rayuwa.
Bazoum na samun goyon bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, sannan kuma shugaban Najeriyar kuma jagoran kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), Bola Tinubu.
Gwamnan Kano ya roki Tinubu da ya bude boda
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya roki shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da ya bude boda domin a samu wadatar abinci a Nijeriya baki daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar ban girma da shugaban hukumar kwastam, Adewale Adeniyi, ya kai masa ranar Litinin a Kano.
Gwamna Abba Kabir-Yusuf, ya koka kan mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon matsi da tattalin arzikin kasar ke ciki, ya ce sake bude iyakokin zai taimaka wajen magance hauhawar farashin kayayyaki da kuma saukar da farashin su.
NiMet ta yi hasashen za a yi rana a wasu jihohin Nijeriya
NiMet ta yi hasashen za a yi rana a wasu jihohin Nijeriya
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen hasken rana da jin dadi daga ranar Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.
An fitar da hasashen yanayi na NiMet ranar Lahadi a Abuja, inda aka yi hasashen yanayi za a iya samun yanayi na rana daga ranar Litinin a yankin arewa.
A cewarta, ana sa ran samun gizagizai tare da hasken rana a jihohin Arewa ta Tsakiya da ake sa ran za a iya samu yanayin tsawa a sassan jihar Benue da safiyar Laraba.
Gwamnan Katsina Dikko Radda ya umurci a zaftare farashin kayan abinci daga rumbun gwamnati saboda azumi
Fursuna ya kwace bindigar Gandiroba ya harbi wani mai faci a Kwara
Fursuna ya kwace bindigar Gandiroba ya harbi wani mai faci a Kwara
Wani fursuna a gidan yari da ke Oke-Kura a Ilorin babban birnin jihar Kwara ya yi kukan kura ya kwace bindiga hannun jami’in tsaron gidan yari ya harbe wani wani mai sana’ar faci a gefen hanya.
Hakan ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da aka fitar da wasu fursunonin gidan yarin.
Lamarin dai ya faru ne misalin karfe 8:00 na safe, kuma ya haifar da firgici da fargaba yayin da mazauna yankin suka tarwatse domin samu tsira a yayin faruwar qbin wanda ya yi kama da wasan kwaikwayo.
Nan take aka garzaya da mai facin zuwa wani asibiti domin kula da lafiyarsa aka kuma ci gaba da tsare wannan fursuna da ya yi aika-aika.

.jpeg)





