Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 454

Tinubu ya umurci a kubutar da daliban jihar Kaduna

 

Tinubu ya umurci a kubutar da daliban jihar Kaduna

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da sace ‘yan gudun hijira a Borno da kuma dalibai a jihar Kaduna.

Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma

’a a Abuja.

Ngalale ya ce shugaban kasar ya umarci jami’an tsaro da na leken asiri da su gaggauta ceto wadanda lamarin ya shafa tare da tabbatar yin hukunci a kan wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Remi Tinubu ta bukaci a yi dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa

Remi Tinubu ta bukaci a yi dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa

Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Tinubu, ta yi kira da a samar da dokokin da za su aiwatar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane a kasar nan.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin wata ganawa da ta yi da shugabar matan jam’iyyar APC ta kasa a fadar shugaban kasa.

Ta koka da irin yadda masu garkuwa da mutane ke girbi daga ‘yan Najeriya suna kashe su, inda ta ba da misali da halin da ake ciki a yanzu da aka yi garkuwa da mutane akalla 200 a Kaduna da sauran wadanda aka kashe daga jihar Borno.

Masara ta yi tsada a Lagos

A dai dai lokacin da Azumin watan Ramadan ke kara gabatowa,kuɗin Buhun Masara ya tashi a kasuwar Mile 12 International Market Legos,inda makon daya gabata aka sayar da Buhun Masarar kan kudi N55,000,sai dai a makon nan, Kudin Buhun Masarar ya kai N65,000, an samu karin kusan Naira dubu 10 kenan. Haka nan kudin Buhun Masarar ya karu a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, da wancan makon kuɗin buhun ya kama N57,000, yayin da a makon nan kuwa aka sayar da Buhun Masarar N58,000 a kasuwar.

Hakazalika, Masara ta kara tsada a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe, a makon da ya shude dai an sayi Buhun Masarar N55,000, yayin da a makon da muke ciki kuwa aka sayar da Masarar N56-57,000.
Idan mu ka yi tattaki zuwa Kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuwa, Masarar ta yi sauki a wannan makon, sama da makon da ya gabata, an sayi buhun Masarar akan kuɗi N55-57,000, amma an dan samu sassauci N2000 a wannan makon, da aka sayar da buhun N53-55,000.
To ita ma dai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna Masarar ta fi sauki a wancan makon, an sayi Masarar N55,500, yayin da makon nan kuwa kuɗin buhun ya kama N57,000, wanda hakan ke nuni da cewa an samu karin N1500 cif.
To idan muka je bangaren shinkafar Hausa kuwa ta fi sauki a wancan makon a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, inda aka sayi buhun Shinkafar N125,000, sai dai a makon nan ya haure da N5000,Kudin buhun dai, ya kama N130,000 a wannan mai karewa.
A wancan makon dai an sayi shinkafar gida N108,000 a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, yayin da a wannan makon kuwa shinkafar ta kara N12,000, inda kuɗin buhun ya kama N120,000. Hakan kudin Buhun shinkafar Hausar take a Kasuwar Mile 12 International Market Legos, da aka sayi shi kan kuɗi N120,000, haka nan batun bai sauya tufafi ba a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, inda a satin nan an sayar da buhun tsabar shinkafar N120,000

A kasuwar Kashere ta jihar Gombe kuwa kuɗin buhun tsabar shinkafar a wannan makon ya kai N115-120,000 hakan akwai na N130,000 a jihar Gomben, sai dai an samu sauƙin N5000 kan kudin na wannan satin da aka sayar da buhun shinkafar har N135,000.
Ita kuwa Shinkafar Bature ta fi sauki a makon nan, a kasuwar Zamani a jihar Adamawa, inda a wancan makon aka sai da shinkafar N82,000, yayin da a makon nan aka sayi buhun shinkafar wajen N75,000
Sai dai a kasuwar Mile 12 International Market Legos kuɗin shinkafar bai sauyi zani ba, a makon da ya shude dai kuɗin N75,000 ne, haka batun ya ke a yanzu ma. 
Shinkafar ta fi sauki a jihohin Kaduna da Gombe, inda a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe da aka sayi buhun N80,000, haka nan aka sayar a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma, sai dai an samu tazarar N5000 cif a kasuwar Dawanau na jihar Kano da aka sayar da shinkafar N85,000.
Taliyar Spaghetti ta fi sauki a kasuwar Kashere dake jihar Gombe a wannan makon,inda ake sai da kwalin Taliyar N13,200 ,yayinda a makon daya gabata kuwa aka sayar da kwalin N13,500.
Hakan Spaghetti ta ɗan yi sauki a kasuwar zamani dake jihar Adamawa,an sayi Taliyar N13,500 a wannan makon,amma makon can kuwa Kuɗin kwalin N13,800 ne.
A kasuwar Dawanau na jihar Kano kuwa Taliyar tafi sauki a makon daya shude sama da wanda muke ciki, a wancan N13,500 ne,amma a makon nan ana sayar da kwalin daga 13,500-14,000 dai dai.
A kasuwar Giwa ta jihar Kaduna kuwa N14,500 ne a wannan makon,kudin Taliyar Spaghetti dai bai sauya Tufafi ba a kasuwar Mile 12 International Market Legos,an sayi kwalin kan kudi N14,500
a makon da ya kare,haka kuwa aka sayar a makon nan dake shirin kare wa.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.

Tinubu ya umurci a fito da abinci domin raba wa mazauna Abuja

 Tinubu ya umurci a fito da abinci domin raba wa mazauna Abuja

 Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya gaggauta sakin hatsi da kayan abinci ga jama’ar gari, domin dakile illar tabarbarewar tattalin arziki.

 Karamar ministar babban birnin tarayya, Dakta Mariya Mahmoud, ce ta bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata, a wani taron gaggawa da ta yi da masu ruwa da tsaki da shugabannin kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja.

 Ta ce umarnin ya zo ne a wata wasika daga fadar shugaban kasa, ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa zuwa ga ministar babban birnin tarayya Abuja, yayin da ta kuma sanar da kafa kwamitin da zai aiwatar da wannan umarni cikin makonni biyu masu zuwa.

 A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja suka kai hari a wani dakin ajiyar kaya da ke unguwar Gwagwa-Tasha a Abuja, mallakin sakatariyar harkokin noma da raya karkara ta babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da kayan abinci tare da lalata ginin.

Kaso 30% cikin 100 na kasafin kudin 2024 na Kano na fannin ilimi – Abba Kabir

 

Kaso 30% cikin 100 na kasafin kudin 2024 na Kano na fannin ilimi – Abba Kabir

Gwamna Abba Kabir Yu

suf na jihar Kano ya ce gwamnatinsa ta ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin shekarar 2024 ga ilimi domin sake farfado da fannin tq yadda za a samu ci gaban zamantakewa da bunkasar tattalin arziki mai dorewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da ayyukan samar da ababen more rayuwa a Jami’ar Bayero Kano, BUK.

Gwamnan ya ce gwamnati ta taimaka wa dalibai marasa galihu da kuma rage kudin rajista da kashi 50 cikin 100 a duk manyan makarantun jihar.

Dan Madamin Katsina ya ba Labaran Mahmud Yar’adua mukamin Sarkin Fada

Dan Madamin Katsina Hakimin Daddara a masarautar Katsina ya sanar da ba Malam Labaran Mahmud Yar’adua mukamin Fadar Dan Madamin Katsina.
Labaran Mahmud Yar’adua dai ma’aikaci ne a gidan rediyon jihar Katsina a sashen labarai da al’amurran yau da kullum.
A cikin wata sanarwa daga ofishin Dan Madamin Katsina Alhaji Usman Nagogo, ta ce nadin na Malam Labaran ya biyo bayan gano kyawawan halayensa da kuma cancantarsa da wannan mukami.
Hakimin na Daddara da ke cikin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina ya ce majalisar masarautar Katsina karkashin jagorancin Mai Martaba Sarki Abdulmumin Kabir Usman ce ta lamunce masa ya nada Malam Labaran Mahmud Yar’adua wannan mukami.
Karshe wasikar ta yi addu’a tare da fatan alheri ga wanda aka ba mukamin.

Gwamnan Katsina Dikko zai ci gaba da ayyukan alherin da za a yi alfahari da APC – Bala Abu Musawa

Alhaji Bala Abu Musawa, mataimakin shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina ya sanar da DCL Hausa cewa Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda na ci gaba da assasawa tare da aiwatar da ayyukan alheran da al’ummar jihar Katsina za su ci gaba da alfahari da jam’iyyar APC.
Ci Garin Musawa, Alhaji Bala Abu na magana ne a lokacin da ya jagoranci wani kwamiti na musamman don duba ayyukan da gwamnatin jihar Katsina da shirin inganta ilmin ‘ya’ya mata na AGILE da kuma karamar hukuma suke gudanarwa a yankuna daban-daban na jihar.
A wannan karon, kwamitin da ya hada jiga-jigan jam’iyyar APC jami’an gwamnati da ‘yan jarida, ya ziyarci kananan hukumomin Malumfashi, Kankara, Musawa da Matazu a shiyyar Funtua ta jihar.
Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC ya ce akwai tsare-tsare da dama da gwamnatin APC ke da su da ke da zummar karade lungu da sako na jihar Katsina domin mutane su samu saukin rayuwa.
Ta fuskar tsaro kuwa, Alhaji Bala Abu Musawa ya ce gwamnatin APC da Malam Dikko Radda ke jagoranta a jihar Katsina, ba za ta gajiya ba wajen ganin ta kakkabe duk wasu masu aikata assha a dazuka da cikin gari domin mutane su koma harkokinsu yadda ya dace.
Ya ce kafa matasan sa kai na ‘Community Watch Corp’ da Gwamna Radda ya yi, alama ce mai karfi na irin aniyarsa ta kawo karshen matsalar tsaro a lungu da sako na jihar Katsina.

UAE ta ɗage haramcin visa kan yan Najeriya

Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce za ta dawo da bayar da biza ga ‘yan Najeriya, hakan wani mataki ne na karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

Bayanin hakan na a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Talata.

Wannan dai na zuwa ne shekaru biyu bayan da Daular Larabawa ta sanya wa yan Najeriya takunkumin shiga kasar.

A cewar hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawar an dawo da shirin ya fara aiki ne daga ranar 4 ga watan Maris din shekarar 2024, wanda hakan ya samo asali ne sakamakon tattaunawa tsakanin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na UAE, Sheikh Mohamed bin Zayad Al Nahyan.

Gwamnan Kano zai nada karin kwamishinoni

Wadanda ya aike da sunayensu a majalisar dokokin jihar don tantancewa da tabbatarwa su ne Engr Kabir Jibrin da Alhaji Shehu Muhammd Na’Allah Kura da Isyaku Ibrahim Kunya.
Sauran su ne Dr Salisu Muhd Tudun Kaya da Amina Inuwa Fagge da kuma Garba Ibrahim Tsanyawa.

Har yanzu Najeriya na biyan tallafin man fetur – Isa Yuguda

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya na biyan tallafin man fetur.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira a gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin data gabata.

A ranar 29 ga Mayu, 2023, Tinubu ya ayyana kawo karshen tallafin man fetur a lokacin jawabinsa na farko.

Asusun ba da lamuni na duniya IMF cikin wani rahoto da ya bayar a watan da ya gabata ya kuma shawarci Najeriya da ta daina kashe kudaden tallafin mai da wutar lantarki gaba daya a wani mataki na magance kalubalen tattalin arzikinta.