Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 455

Hukumar Anti-Corruption ta Kano ba ta da ikon bincikar Ganduje – Babbar Kotun Tarayya

 

Babbar Kotun Tarayya d ake jihar Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano da ake wa lakabi da Anti-Corruption ba ta da ikon a bisa doka na binciken tsohon gwamnan jihar kan bidiyon Dala.

Alkali Abdullahi Muhammad Liman shi ne ya sanar da wannan hukunci a Talatar nan wanda ya ce laifin da ake zargin tsohon gwamnan da shi ya fada cikin laifuka da hukumomin gwamnatin Tarayya ke da hurumin bincikarsu. 

Buhari ne ya lalata makomar Najeriya – Gwamnan jahar Pilato Caleb Mufwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya zargi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifin tabarbarewar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a ranar Litinin a yayin rantsar da masu ba shi shawara na musamman su 22 a gidan gwamnati da ke Jos.

Mutfwang ya ce Buhari ya bar tattalin arzikin kasar cikin mummunan hali ga magajinsa, Bola Tinubu.

Hisbah ta kai samame Gidan Gala a Kano

Malam Aminu Ibrahim Daurawa 

Hukumar Hisbah a jihar Kano sun kama wasu mutane 10 da ake zargi da aikata baɗala a wani gidan Gala da ke a jihar 

Samamen ya biyo bayan ƙorafi da mabiya addinin kirista dake titin Zungeru a karamar hukumar Fagge suka kai ga hukumar.

Mazauna yankin sun koka da cewa an bude gidan Gala dinne a cikin unguwar su, don haka ne suka shigar da kara ta hannun lauyoyinsu.

‘Yan sanda sun haramta amfani da na’urar cire kudi ta POS ko ‘transfer’ a caji ofis

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sake nanata batun nan na haramta amfani da na’urar cire kudi ta POS da duk wani nau’in tura kudi a zamanance ‘bank transfer’ a cikin caji ofis da sauran ofisoshin ‘yan sanda a duk fadin kasar.
Hakan ya biyo bayan zarge-zargen da ke tasowa cewa ana hada-hadar kudi ta hanyar amfani da na’urar POS ko ‘transfer’ da sa hannun wasu bare-gurbin  ‘yan sanda.
Wannan haramci dai na da nufin kare kima da martabar aikin ‘yan sanda da hana yunkurin karbar cim hanci a duk ofisoshin ‘yan sanda na kasar.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce babban sufeton ‘yan sanda na kasa IGP Kayode Egbetokun ya ja kunnen masu aikata hakan cewa za su kuka da kansu idan aka kama su.

Hukumar Kwastam a Najeriya reshen jihar Kano, ta ce ta samu kudaden shiga har Naira biliyan 9.7 a watan Fabrairu.

Hukumar hana fasa kwauri ta Nijeriya kwastam  NCS, reshen jihar Kano, ta samu karin kudin shiga Naira biliyan 9.7 a watan Fabrairu a daga mutanen da suke shiga da kayayyakin kasashen waje zuwa kasar.

Dauda Chana, shine kwanturolan Hukumar Kwastam mai kula da jihohin Kano da Jigawa ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin labaran Nijeriya (NAN)a Kano .

 Chana ya kuma ce rundunar ta samar da matakan hana fitar kudaden shiga ta matsugunan kan iyakokin yankin ta hanyar karfafa tsaro da sa ido domin dakile safarar haramtattun kayayyaki a kasar.

Ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da gwajin kashi 100 na kayan da ke shiga ta kan iyakokinta domin hana shiga da kayayyaki da suka hada da makamai da alburusai.

Kwanturolan ya bayyana cewa,rundunar ta bayar da umarnin gudanar da aiki mai inganci ga jami’anta da ke kan iyakokin kasar kan yadda za a shawo kan matsalar fasa kwauri,kuma zasu cigaba da inganta harkokin kasuwanci a fadin kasar.

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero,yayi Kira ga Yan kasuwa da surage tsadar kayan abinchi da sauran kayayyaki saboda zuwan watan azumi

 Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga ‘yan kasuwa musamman masu sayar da kayan masarufi da su rage farashin kayan abinci da sauran kayayyaki domin baiwa talakawa damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Zariya a lokacin cin abincin rana da aka shirya bayan kaddamar da wani littafi mai suna: “Dauloli a Kasar Hausa” na Farfesa Sa’idu-Mohammed Gusau.

 

Ado Bayero ya kuma shawarci ’yan Najeriya masu hannu da shuni da su rika taimakawa marasa galihu a lokacin azumin Ramadan..

Ya kuma yi addu’ar Allah subhanahu wata’ala ya nuna mana wannan wata mai alfarma cikin koshin lafiya ya kuma karbi addu’o’in da al’umma zasu gudanar.

Sarkin ya yabawa mawallafin littafin, da ya bayar da cikakkun bayanai kan masarautun Hausawa a Kano, Katsina, Zamfara, Kebbi da Zazzau da dai sauransu.

Ya kara da cewa akwai bukatar kowanne dalibi dake bincike a fannin Ilimin harshen Hausa da tarihinsu ya mallaki littafin littafin don kyautata binciken sa.

Ku kawo rahoton duk wanda ya nema cin hanci a wajenku -Tinubu ya fada wa masu zuba hannun jari

Ku kawo rahoton duk wani Jami’ina da ya nema cin hanci a wajen ku -Tinubu ya gayawa masu zuba hannun jari.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga masu zuba jari da su kai rahoton duk wani jami’in Nijeriya da ya nemi cin hanci kafin ya zuba jari a kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron kasuwanci da saka hannun jari na Nijeriya da Qatar a birnin Doha a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake tabbatar wa ‘masu zuba jarin kasar Qatar a shirye suke da karfafa alakar kasuwanci da ya kasuwar kasar.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai,Ajuri Ngelale ya raba wa manema labarai.
Shugaban ya bayhana cewa gwamnatinsa na gudanar da shirye shirye masu inganci dan kara karfafa kasuwanci tareda mutanen kasashen ketare.
Yace duk wata matsala da ‘yan kasuwar suka fuskanta a baya anyi kokarin maganceta yakuma basu tabbacin yin kasuwanci cikin nutsuwa batare da wani matsala ba.
Tinubu ya kuma tabbatar wa masu zuba hannun jarin na kasashen larabawa cewa indai suka zuba jarinsu zasu samu aminci tare da cikakken hadin kan yan Nijeriya kasancewar kasar na bukatarsu a irin wannan lokaci.

Na gamsu da alkiblar gwamnatin Tinubu da Shettima – Buhari

Duk da irin matsalar tattalin arziki da Nijeriya ke ciki da ma matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce ya gamsu da alkiblar da shugabannin siyasa na yanzu suka fuskanta.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a garin Daura na jihar Katsina a ranar Asabar.

Tsohon shugaban kasar ya yabawa gwamnatin Bola Tinubu bisa kokarin da take yi na daidaita tattalin arzikin kasar.

Yadda fusatattun matasa suka tare tirela suka wawushe taliya a Zariya 

 Yadda fusatattun matasa suka tare tirela suka wawushe taliya a Zariya 

Wasu fusatattun matasa sun afkawa wata motar dakon kaya mallakar kamfanin BUA dauke da taliyar spaghetti a Dogarawa kan titi Zariya zuwa Kano sun wawushe taliyar

Dogarawa wani ƙauye ne da ke a wajen birnin Zariya a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano. 

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da wasu matasan sun tare wasy tirelolin da ke makare da kayan abinci a yankin Suleja da ke jihar Neja, inda suka sace buhunan shinkafa da sauran kayan abinci sakamakon yanayin halin kunci da ake ciki a kasar.

 

Shan miyagun kwayoyi ke sa karuwar rashin tsaro a Nijeriya – Marwa

 

Shan miyagun kwayoyi ke sa karuwar rashin tsaro a Nijeriya – Marwa

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, Buba Marwa, ya ce shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin ‘yan kasar ne ke haddasa rashin tsaro a kasar.

Marwa ya bayyana haka ne a yayin taron wayar da kan mata da matasa a babban birnin tarayya Abuja ranar Juma’a a Abuja.

Ya kuma ce matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa ita ce matsalar kowa wanda a cewarsa ya hada da iyaye da makaranta da sauran jama’a da su kansu matasa.