Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 456

MTN ya kulle layukan waya 4.2m da aka kasa hada su da lambar NIN

 MTN ya kulle layuka 4.2m da aka kasa hada su da lambar NIN

Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya ce ya katse layukan sadarwa akalla miliyan 4.2 daga cibiyar sadarwarsa yayin da wa’adin da aka kayyade na ranar 28 ga watan Fabrairu na a hada lambobin layuka da shaidar zama dan kasa (NIN) da SIM ya cika.

Kamfanin MTN ya bayyana hakan ne a sakamakon binciken da ya gudanar a ranar Juma’a.

Kamfanin ya ce layukan da aka katse sune na mutanen da suka yi kunnen kashi suka ki hada shi da lambar shaidar zama dan kasa wato NIN.  

A cewar kamfanin, tun a cikin watan Disambar  2023 ne hukumar NCC ta ba da umurni ga dukkanin kamfanonin sadarwa a  kasar da su tabbatar masu masu amfani da layukan sadarwa su hada layukan wayoyinsu da NIN ɗin su.

Muna ba da shawara ga Gwamnatin Kano da ta nemi afuwar Daurawa – Abdallah Gadon Kaya 

 Muna ba da shawara ga Gwamnatin Kano da nemi afuwar Daurawa – Abdallah Gadon Kaya 

Fitaccen malamin addinin Musulunci daga jihar Kano Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi kira tare da bayar da shawara ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da ya nemi afuwar Sheikh Aminu Daurawa.

Dakta Gadon Kaya ya yi kiran ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na facebook a ranar Juma’a jim kadan bayan Sheikh Daurawa ya ayyana yin murabus daga shugabancin hukumar Hisbah.

 

Ya ce “Muna kira ga gwamna Abba Yusuf tare da makusantansa da su kai zuciya nesa su kira malam Daurawa, su zauna da shi kuma su ba shi haƙuri kan abubuwan da ya faru.”

Jose ya kammala aikin horar da tawagar kungiyar Super Eagles 

 

Jose ya kammala aikin horar da tawagar kungiyar Super Eagles 

Kocin tawagar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya wato Super Eagles Jose Peseiro ya sanar da cewa ya kawo  karshen aikinsa na horar da tawagar ta Super Eagles.

Jose wanda ɗan asalin kasar Portugal ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na X da a ranar Juma’ar nan.

“A jiya muka kawo ƙarshen kwantaragin da na kulla tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Nijeriya NFF.” Inji Jose

Buhun masara mai cin tiya 40 ya kai Naira 73,000 a Katsina

A makon nan dai, al’ummar kudancin Nijeriya  sun dara, sakamakon  saukar farashin kayan abinci, yayin da a yankin Arewacin kasar kuwa, farashin wasu daga cikin kayan abincin ya fi na makon da ya gabata. A kasuwar Mile 12 International Market Lagos dai, a makon jiya, farashin buhun Masara mai cin tiya 40, ya kai N60,000, sai dai, a wannan makon an samu ragin kudi har N5,000, inda farashin buhun masarar ya kama N55,000.
A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuwa, farashin buhun masarar bai sauya zane ba, an dai sayi masarar kan kudi N57,000 a wancan satin, hakan aka saya a wannan makon ma. Sai dai, a kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuma,  masara ta fi sauki a wancan makon, sama da makon da muke ciki, inda aka sayar da buhun  N57,000 a makon da ya gabata, yayin da wannan makon kuwa kuɗin buhun masarar ya shilla zuwa N73,000.
A makonni biyu da suka gabata dai, an sayi masara kan kudi N62-65,000 a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, amma a wannan makon kuɗin buhun masarar  ya kama N55,000 -N57,000.
Ita kuwa kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe, masarar ta fi sauki a makonnin da suka gabata sama da yanzu, inda a wadancan makonnin aka sayar da buhun masara N42,000, amma kudin buhun a makon nan, ya kai N55,000 cif. Haka kudin buhun masarar ya ke a kasuwar Dandume na jihar Katsina,kudin ya kama N55,000
A kasuwar Giwa ta jihar Kaduna ma Masarar ta haure, inda a makonnin da suka shude aka sayar da ita N51,000, amma a makon nan kuɗin buhun masara N55,500 ne.
Shinkafar gida ta fi  sauki a makonnin da suka gabata a kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda a wancan makon kuɗin ya kama N120,000, yayin da a makon nan aka sayi shinkafar N125,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna.
 
A kasuwar Dawanau da ke jihar Kano kuwa, kuɗin buhun shinkafar gida ya kama N108,000, a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma an samu karin N5,000, kan kudin buhun shinkafar na baya, inda aka sayar da buhun N115,000. Sai dai a makon nan, kudin buhun N120,000 ne, a kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuma kuɗin shinkafar Hausa N60,000 cif cif.
Ita ma dai shansharar shinkafar ta fi sauki  a baya sama da na wannan makon, a Kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, inda makon da ya gabata kudin buhun shinkafar mai bawo ya kama N40,000-43,000. Sai dai a makon nan kuɗin N58,000 ne -59,000.
 
Buhun shinkafar Hausar  N130,000-135,000 ne a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe.
Idan muka leka bangaren shinkafar waje, ta fi sauki a makonnin da shuka shude sama da na yanzu da ake ganin kamar ta yi sauki.inda makon nan  kuɗin ya kama N75,000 a kasuwar Mile 12 International Market Legos,da wancan makon aka saya N70,000 daidai.
A kasuwar Kashere da ke jihar Gombe kudin Shinkafar N85,000 ne hakan batun ya ke a kasuwar a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano,amma an samu saukin N3000 a kasuwar Zamani dake jihar Adamawa,inda kuɗin Shinkafar N82,000.
Zamu ƙarƙare farashin kayayyakin abincin na  makon da farashin Taliyar Spaghetti ,a Dukkanin kasuwannin dai farashi yafi na makon biyu da suka shuɗe Tsada,inda aka sayar da  kwalin  Taliyar N14,500 a kasuwar Mile 12 International Market  Legos,Amma an samu sassaucin N1000 a  kasuwar Dawanau  dake jihar Kano,inda kuɗin kwalin Taliyar ya zama   N13,500 ,,haka nan batun bai sauya zani a kasuwar Kashere dake jihar Gombe.
A Mai’adua jihar Katsina kuwa kudin a wannan makon ya kama  N13,000 cif.
A kasuwar Zamani dake jihar Adamawa kuwa,N13,800 ne kudin ko wani kwali guda na Spaghettin.

Tinubu ya umurci BUA/Dangote su dawo da tsohon farashin siminti 

 Tinubu ya umurci BUA/Dangote su dawo da tsohon farashin siminti 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci kamfanonin siminti da su koma yadda suke a halin da ake ciki dangane da farashin kayayyaki.

Ministan ayyuka Sanata David Umahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ya ziyarci masana’antar siminti na BUA da ke Sokoto ranar Alhamis.

A cewarsa shugaban ya umurci masana’antun su koma kan tsohon farashin siminti yadda yake a baya.

Ba ku isa ku yi fada da gwamnatina ba, martanin Tinubu ga kungiyar NLC

 Ba ku isa ku yi fada da ni ba, martanin Tinubu ga kungiyar NLC

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi Allah wadai da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC ta yi a cikin makon nan. 

Shugaba Tinubu ya gargadi ‘yan kungiyar ta kwadago da su sani cewa ba NLC kadai ce muryar jama’a ba.

Ya yi magana ne a yayin kaddamar da layin dogo na jirgin kasa na Red Line a jihar Legas wanda ya hada daga Agbado zuwa Oyingbo.

‘Yan sanda sun kama masu sana’ar awo da ake zargi da tauye mudu a Gombe 

 Yan sanda sun kama masu sana’ar awo da ke algus a Gombe 

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a ranar Alhamis ta tabbatar da cafke wasu mutane biyu Bashir Haruna da Mohammed Isah.

 A cewar wata sanarwa da mataimakin jami’in hulda da jama’a na jihar, ASP Sharif Sa’ad ya rabawa manema labarai, an kama wadanda ake zargin ne da laifin hada baki wajen gauraya abinci da ya lalace da mai kyau.

Sa’ad ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da aka ji labarin cewa sun yi algus a buhunan shinkafa 57 inda za su je su sayar wa jama’a da ba su ji ba gani.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a karkashin jagorancin CP Hayatu Usman na son sanar da jama’a game da kama yan kasuwar da ake zargi da laifin yin algus da ma fasa-kwaurin abinci, musamman shinkafa.

Na dauki laifin tsanani da tsadar rayuwa da ‘yan kasa ke ciki – Tinubu

 Na dauki laifin tsanani da tsadar rayuwa da ‘yan kasa ke ciki – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Nijeriya da su yi hakuri su kuma ci gaba da juriya dangane da halin da matsin da tattalin arzikin kasar ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa akwai haske nan gaba kadan.

Shugaban ya ce yana da cikakkiyar masaniya kuma ya dauki alhakin matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnati.

Ya ce ba zai yi korafi ba amma yana maraba da duk sukar da ake yi masa tunda shi ne ya nemi zama shugaban Nijeriya.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ziyarar da ya kai wa shugaban kungiyar kabilar Yarabawa ta Afenifere a ranar Laraba.

Kungiyoyin matasa a a jihar Ogun sun bukaci shugaba Tinubu ya bude boda

 Kungiyoyin matasa a a jihar Ogun sun bukaci shugaba Tinubu ya bude boda

Gamayyar kungiyoyin matasan jihar Ogun sun yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya bude dukkanin iyakokin kasa a wani mataki na magance matsalar tsadar abinci da yadda za a kara habaka tattalin arziki da kasar.

Kakakin kungiyar, Fẹmi Owoẹye, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a Abeokuta, ya roki Tinubu da ya tashi tsaye wajen shawo kan matsalar ta hanyar bude iyakokin kasa domin bunkasa tattalin arziki da rage tsadar kayan abinci.

Matasan sun kuma nuna damuwarsu kan cewa duk matakan da gwamnati kasar ta bijiro don magance wahalhalun da ake fama da su ba su shafi matasan Nijeriya ba, musamman ma wadanda ba su da aikin yi.

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano ta dakatar da nadin Hakimi a Bichi

 Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano ta dakatar da nadin Hakimi a Bichi

Gwamnatin jihar Kano ta umurci majalisar masarautar Bichi da ta dakatar da bikin nadin sarautar Salisu Ado Bayero a matsayin hakimin masarautar.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa gwamnatin ta dakatar da nadin na Salisu Ado Bayero wanda kane ne ga Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.

A ranar 15 ga watan Fabrairu ne Masarautar Bichi ta rubutawa Salisu Ado Bayero wasika inda ta sanar da shi amincewar sarkin na a nada shi a matsayin hakimin gundumar Bichi.