Thursday, April 9, 2026
Home Blog Page 457

An cimma kaso 90% na jarjejeniyar gwamnati da ‘yan kwadago- Minista

 An cimma kaso 90% na jarjejeniyar gwamnati da ‘yan kwadago- Minista

Ministar kwadago da samar da ayyukan yi a Nijeriya, Nkiruka Onyejeocha, ta ce gwamnatin kasar ta cimma kusan kaso 90% na yarjejeniyar da ta kulla tsakaninta da kungiyoyin kwadago tun a cikin watan Oktoban 2023.

 Nkiruka is bayyana hakan ne a lokacin da take magana yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels. 

Onyejeocha ta ce shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (TUC), Joe Ajaero, ya shaidawa wakilan gwamnati a wani taro a ranar Lahadi cewa zanga-zangar da suka gabatar ba saboda jarjejeniyarsu da gwamnati ba ce, sun yi ta ne saboda tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyakn masarufi a fadin kasar baki daya.

Har ‘yan adawa na yabon Gwamna Dikko wajen kokarin inganta tsaron jihar Katsina – Bala Abu Musawa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya ce irin kwazon da Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ke yi wajen inganta tsaro ya sa har ‘yan adawa na yabonsa.
Alhaji Bala Abu Musawa na magana a karamar hukumar Jibia, a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman da ke duba ayyukan da aka gudanar a kananan hukumomi 34 na jihar tare da ganawa da shugabannin jam’iyyar a matakin karamar hukuma da mazabu.
Ya ce Allah Ya hore wa Malam Dikko Umaru Radda fasaha da basirar da ya ke amfani da ita wajen ganin zaman lafiya ya inganta a lungu da sako na jihar.
Bala Abu Musawa ya buga misali da kafa matasan sa kai na ‘Community Watch Corp’da Gwamnan ya kaddamar suke ci gaba da ayyukan samar da tsaro tare da sauran jami’an tsaro a wuraren da ke fama da batun tsaron, inda ya ce wannan tunani ne mai kyau da ke haihuwar da mai ido a halin da ake ciki.
Mataimakin shugaban jam’iyyar wanda shi ne Ci Garin Musawa, ya kuma yaba da abin da ya kira kokarin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda na bullo da alawus-alawus ga jagororin jam’iyyar APC tun daga matakin jiha har zuwa matakin mazaba, inda ya ce ya zuwa yanzu an biya alawus-alawus na cikon watanni uku, kuma za a ci gaba da yin haka don karfafa musu guiwar tafiyar da lamurran jam’iyya yadda ya kamata.
Ya kuma yi bayanin cewa ziyarar na da kuma nufin motsa harkokin jam’iyyar APC ganin cewa hukumar zabe ta jiha, ta sanar da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a shekara mai kamawa.

Majalisar Nijeriya nason gwamnatin kasar ta bullo da tsarin da zai sauke farashin kayan abinci a kasar.

 Majalisar dattawan Nijeriya ta bukaci gwamnatin tarayyar kasar da ta bullo da wani shiri na rage kudin abinci a matsayin wani mataki na wucin gadi domin dakile illar yunwa da karancin abinci a kasar.

Majalisar ta kuma yi kira ga ma’aikatar noma da samar da abinci ta kasar da ta yi hulda da sauran masu ruwa da tsaki, domin lalubo hanyoyin da za’a magance tsadar abinci a fadin kasar.

Gabatar da shirin yazama dole, domin akwai bukatar abullo da sabbin dabaru domin da zasu farfado da matsalar abinci da ake fuskanta. 

Wadannan kudurori sun biyo bayan kudirin da babban mai shigar da kara na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume daga ( Borno ta Kudu), da kuma Sanata Saliu Mustapha daga( Kwara ta tsakiya) da wasu da yawa daga cikinsu suka amince da wayannan kudurorin a yayin zaman majalisar.

Dalilin da yasa muka cire tallafin man fetur – Tinubu.

 Dalilin da yasa muka cire tallafin man fetur – Tinubu.

 Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce matakin cire tallafin man fetur abu ne mai kalubale, amma matakin da ya dace tare da bunkasa harkokin makamashi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin bude taron kasa da kasa kan makamashi na Nijeriya (NIES 2024) karo na 7 a dakin taro na Banquet Hall dake Aso Villa, Abuja.

Tinubu ya ce domin rage tasirin cire tallafin man fetur na kankanin lokaci ga marasa galihu, gwamnatinsa ta himmatu wajen aiwatar da Shirye-Shirye daban daban. 

Tinubu, wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Malagi, ya ce tallafin man fetur a tsawon shekaru ya kawo cikas ga albarkatun tattalin arzikin Nijeriya.

Don haka gwamnati na iya kokarinta wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya Amma wannan ba karamin aiki bane da gwamnatin ta dauko, saboda haka aka fito da wayannan  tsare tsare. 

Yace kudaden da aka ware a baya don tallafawa albarkatun man fetur yanzu an karkatar da su zuwa bunkasa da inganta makamashinmu da sauran ababen more rayuwa a kasar. 

Muna rokon Allah Ya yaye mana matsalar tsaro a jihar Katsina – Bala Abu Musawa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa, ya ce a halin da ake ciki matsalar tsaro ce kadai ce ke ci wa al’ummar jihar tuwo a kwarya, inda ya ce ana ci gaba da addu’o’i na neman zaman lafiya dawwamamme a lungu da sako na jihar.
Alhaji Bala Abu Musawa na magana ne, a Dutsinma a lokacin wata ziyarar gani da ido ta duba wasu ayyuka da ganawa da shugabannin jam’iyyar APC a matakin karamar hukuma da mazabu.
Jam’iyyar APC a jihar Katsina dai ta fara wannan ziyarar ne a makon jiya da shiyyar Daura mai kananan hukumomi 12, inda a wannan makon ta fara a shiyyar Katsina da ke da kananan hukumomi 11, da aka fara da kananan hukumomin Danmusa, Safana, Dutsinma da Kurfi.
Jigon jam’iyyar ta APC a jihar Katsina ya ce addu’a kasancewarta takobin mumini, ita ce kadai ya kamata al’ummar jihar Katsina ta kara yi domin a kawo karshen matsalar ta tsaro da ta ke addabar wasu yankunan jihar.
Duk da Alhaji Bala Abu Musawa ya ce ana samun sauki a matsalar tsaro a halin yanzu, amma dai ya nanata kudirin gwamnatin Dikko Umaru Radda a karkashin jam’iyyar APC cewa a duk rana a tsaye take don ganin ta kakkabe ayyukan ta’addanci a jihar.
Ya nusar da mutane cewa wannan matsala ta tsaro ba rana daya ta shigo ba, sai a hankali za ta kwaranye, don haka, ake bukatar mutane su rika ba da hadin kai musamman ga jami’an tsaro don su inganta aikinsu na samar da tsaro.

Za mu yaki ‘yan bindiga har sai mun ga bayansu – Gwamnatin Katsina

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya ya kai ziyarar jajantawa da ta’aziyya ga al’ummar kauyen Yarnasarawa a cikin karamar hukumar Faskari ta jihar bayan da harin da ‘yan ta’adda suka kai wa kauyen a makon jiya.
Harin ‘yan bindigar dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutune 8 kamar yadda sanarwar da daraktan yada labaran ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Aliyu Yar’adua ya aike wa DCL Hausa.
Sanarwar ta ce ‘yan bindigar sun farmaki kauyen, inda suka kuma sace mutane 45 da suka hada da mata 37 da maza 8 da mafiyawansu yara ne.
Gwamnan jihar ta Katsina da ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin jihar Abdullahi Garba Faskari, ya nuna jimami, alhini da takaicin abin da ya faru a wannan kauye, inda ya yi ta’aziyya tare da addu’ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasu.
Gwamnan wanda ya jaddada kudurinsa na ci gaba da yaki da ta’addanci har sai an kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda a jihar, ya kuma bi gida-gida inda ya yi ta’aziyyar wadanda suka rasu.
Sannan Gwamnan ya kuma ziyarci motoci 8 da ‘yan ta’addar suka kona da gidaje 10 da su ma aka kona.

Gwamnatin tarayya ta sake gargadin NLC game da shirin zanga-zanga

0

 

Gwamnatin tarayya ta
sake gargadin kungiyoyin kwadago a Najeriya kan shirin zanga-zanga da suke yi a
cikin makon nan.

Wannan na zuwa ne bayan
da wasu kungiyin fararen hula 65 suka nuna goyon bayan su ga kungiyoyin
kwadagon da kuma tabbatar musu da bada goyon baya a ranar zanga-zangar.

A karshen makon jiya
ne shugaban kungiyar NLC Joe Ajero ya zargi gwamnatin tarayya da shirya ‘yan
dabar da zasu kai musu hari a ranar zanga-zangar, zargin da gwamnati ta
musanta.

Da yake jawabi
babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mr Bayo Onanuga
ya ce tuni ‘yan sanda suka mikawa kungiyoyin daya bayan daya takardun gargadin
fita zanga-zangar don haka abu mafi a’ala shine su janye kudurin nasu.

Sai dai kuma duk da wannan gargadi da gwamnatin tarayya ta sabunta,
kungiyar ta NLC ta ce babu gudu ba ja da baya wajen gudanar da zanga-zangar gobe
Talata da kuma jjibi Laraba.

EFCC ta kwato sama da naira biliyan 60 cikin kasa da kwanaki 100

0

 

Hukumar hana cin
hanci da rashawa ta EFCC ta sanar da kwato naira biliyan 60 cikin kasa da
kwanaki dari, yayin da ta karbi korafe-korafen cin hanci guda dubu 5.

Yayin da yake
jawabin ayyukan da yayi cikin kwanaki 100 da zaman sa shugaban hukumar Mr Ola Olukoyede
ya ce cikin korafe-korafe dubu 5 din da aka shigar gaban hukumar ta amince a
fara bincike kan sama da dubu 3.

Ya ce bayan naira
biliyan 60 din an kuma kwato wata dala miliyan 10 cikin kasa a watanni 4 da yayi
a ofis.

Mr Ola ya ce lamarin
cin hanci da rashawa abu ne da ke bukatar hadin kan jama’ar kasar kasancewar EFCC
ba zata  iya ita kadai.

Baya ga wannan
jamawabi, shugaban na EFCC yayi korafi game da karancin ma’aikata, yana mai
cewa hukumar da ke sanya idanu kan mutane sama da miliyan 150, tana da ma’aikata
4,800 don haka ba za’a ga tasirin aikin da suke yi ba.

 

 

Mutane 7 sun mutu wajen siyan buhun shinkafar da kwastam ke rabawa a Legas

0

 

Mutane 7 sun mutu a sakamakon
turmutustu wajen siyan buhun shinkafar da hukumar kwastam ta ke sayarwa a jihar
Legas.

 

Bayanai sun ce dubban mutanen ne suka fita da nufin
sayan shinkafar, yayin da ake kafa layi tun karfe uku na dare don sayan
shinkafar a ofishin hukumar da ke unguwar Yaba, kan naira dubu 10 akan Kg 25 na
shinkafar.

Wannan ya biyo bayan shelar da hukumar kwastom
din ta yi na fara sayarwa da ‘yan kasa shinkafar da ta kama hannun masu fasakwauri,
sai dai wani abu mai daure kai shine yadda hukumar tayi ikirarin cewa shinkafar
na da illa ga lafiyar jama’a, sai gashi tana sayarwa.

Rahotanni sun ce cikowar mutane ta haddasa
turmutsutsu yayin da aka tattake wasu mutane 7 har suka cimma ajalin su, cikin
su kuwa har da mace mai tsohon ciki.

Wasu bayanai sun ce turmutsutsun ya faru ne
lokacin da yan daba suka yi yunkurin shiga ofishin hukumar da karfin tsiya.

Wasu daga cikin wadanda suka zanta da manema
labarai sun ce jamia’n na custom sun yi iya bakin kokarin su wajen shawo kan
matsalar amma ‘yan dabar sun fi karfin su kasancewar basu shiryawa faruwar
hakan, ba dalilin da ya sanya ‘yan dabar suka fi karfin su.

Bayanai sun ce jami’an ‘yan sanda sun je wajen
sai dai sun je ne ba don shawo kan matsalar ba, illa dai don samun nasu buhun
shinkafar.

 

Za mu tabbatar da samar da ilmi mai inganci a jihar Zamfara – Gwamna Dauda

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa yaran da ke tasowa sun samu ilmi mai inganci a jihar.
Gwamnan na magana ne a wajen gasar wasanni ta shekarar 2024 karo na uku da aka gudanar a makarantar Almufida International Academy, Gusau.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar, Malam Sulaiman Bala Idris ya aike wa DCL Hausa, ta ce wannan makaranta, har ta karrama Gwamna Dauda da lambar girmamawa ta GCFC.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya nuna jin dadi da farinciki sosai na yadda ya ga daliban makarantar na fahimtar karatu da kuma zalaka a wasannin da aka gudanar a cikin gasar.
A jawabinsa a wajen taron, Gwamnan ya yaba wa hukumar gudanarwar makarantar da ta ke kokarin tsare ka’ida da bin dokoki da ka’idojin da aka gindaya don ilmi ya inganta a jihar.