Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 458

Zaman lafiya ya dawo a kananan hukumomi 13 na jihar Katsina – Gwamnati

0

Dikko Umar Raɗɗa 

Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Faruq Lawan Jobe, ya ce gwamnatin jiha ta yi kokari ta maido da zaman lafiya a kananan hukumomi 13 cikin 22 da ke fama da matsalar tsaro a jihar.

Jaridar This day ta rawaito cewa Faruq Jobe na magana ne a gaban ‘yan jarida, inda ya ce an samu wannan nasarar ne ta dalilin ayyukan jami’an sa kai na ‘Community Watch Corp’ da gwamnatin ta kirkiro, hadin guiwa da sauran jami’an tsaro a jihar.

Daga cikin kananan hukumomin da tsaron ya fara inganta, a ta bakin mataimakin Gwamnan jihar, akwai Batagarawa, Dutsinma, Bindawa, Kusada, Funtua, Danja, Bakori, Malumfashi, Kafur, Musawa, Ingawa, Charanci da Matazu.

Ziyarar shugaba Tinubu na nan ta zuwa ƙasar Qatar

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, a ranakun 2 da 3 ga watan Maris.

ma’aikatar harkokin wajen kasashen wajen ce ta bayyana hakan a wani martani da ta mayar kan rahotanni da ake ya dawa na cewa hukumomin Qatar sun ki amincewa da shugaba Tinubu na ziyartar kasar.

Ministan harkokin wajen kasashen waje Ambasada Yusuf Tuggar, a ranar Asabar ta ce shugaba Tinubu zai gudanar da ziyarar kamar yadda aka tsara tun da farko.

Karin bayani kan takunkumin da ECOWAS ta janye wa Nijar

0

 

Kola Sulaimon / AFP

ECOWAS da shugabanninta sun lashe amansu bayan da a taron kungiyar
a Abuja, ta janye wasu daga cikin takunkuman da ita da kanta ta lafta wa Nijar
don ladabtar da sojojin da suka hambarar da gwamnatin dimukuradiyya a shekrar
da ta gabata. A sanarwar da ECOWAS din ta fitar ta ce a hankali za ta janye
sauran, amma ta ce ta janye wa kasashen Mali da Guinea takunkuman kudi da
tattalin arziki. Sai dai ‘yan Nijar sun fi damuwa da bukatar a janye musu
takunkuman iyakoki da kudade da na wutar lantarki wanda kawo yanzu sanarwar ta
ECOWAS ba ta ce komai a kai ba. 




 

Tun bayan lafta wannan takunkumi dai, hukumomin mulkin sojan kasar
suka dukufa wajen lalubu hanyoyin rage radadin takunkumin amma kusan ba su yi
wani tasiri ba duba da yadda farashin kayayyakin musamman abinci ya ki sauka
tare da ci gaba da fuskantar matsalar rashin wadatuwar kudade a hannun mutane.

 

To sai dai duk da wannan yanayi da aka shiga sojojin suka ci gaba
da kafewa kai da fata ak an matsayin su har ma a karshe suka ayyana ficewarsu
tare da takwarorinsu na Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar baki
daya  don haka ne ga masu fashin baki irinsu Dr Gambo Alhaji Sani masanin
kimiyar siyasa a Jami’ar André Salifou ta Damagaram ke ganin dole ne kungiyar
ta ECOWAS ta rungumi kaddara domin kuwa ta ga ba wurin zuwa ne sai gona shi ya
sa ta ci tuwon fashin, mai sharhin ya shaida wa DCL Hausa cewa duk da ECOWAS ta
janye takunkuman amma zai wahala idan yanzu sojojin na Nijar za su janye fita
daga kungiyar da suka yi domin sun yanka sun ga jinni

Tun farkon wannan mako mai karewa ne dai rahotanni cire takunkumin
na ECOWAS kan Nijar ke yawo kafin a tsakiyar makon tsohon shugaban kasar
Tarayyar Najeriya Yakubu Gowon wanda ke cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS
ya yi kira ga kungiyar  da ta gaggauta cire Nijar din takunkumin da ta
kakaba mata.

Gwamnatin Qatar ta hana Tinubu damar halartar wani taro a kasar

Gwamnatin kasar Qatar ta hana Shugaba Tinubu damar gudanar da wani taron bunkasa kasuwanci da ya so halarta a ranar 02 ga watan Maris. 
Hukumomin kasar sun ce akwai wasu abubuwa da suka tsara yi a wannan rana kuma Nijeriya ba ta da yarjejeniyar da shugabanta zai iya zuwa Qatar ya yi irin wannan taro.

Bankin CBN ya fito da sauye-sauye masu tsauri ga ‘yan chanji

Babban Bankin Najeriya ya sanya wa yan chanji dokar dole sai wanda yake da jarin Naira miliyan 500(tier2) ko biliyan biyu ne za a ba shi lasisin (tier 1)

Karin haske a game da tsarin :
-Mai lasisin ‘Tier 1’ zai iya mu’amala kai tsaye da CBN kuma za a yi ba shi damar bude rassa wuraren chanji a kowacce jiha a Najeriya.
-Mai lasisin ‘Tier 2’ kuma sai dai ya yi mu’amala da bankunan kasuwanci kuma a jiha daya kawai zai iya bude wurin chanji kudi amma zai iya yin rassa a wannan jihar.
-A baya mai jarin miliyan 350 yana iya samun ‘Tier 1’ amma yanzu sai jarinka ya kai Naira miliyan 500 zuwa biliyan 2 za a ba ka.

APC na bakin kokarinta don inganta rayuwar al’umma – Bala Abu Musawa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya ce gwamnatin APc a jihar na bakin kokari nta don ganin ta kyautata tare da inganta rayuwar al’ummar jihar da ke lungu da sako na jihar.
Alhaji Bala Abu Musawa na magana ne a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman don duba ayyukan da ake gudanarwa a lungu da sako na jihar.
Tawagar da Alhaji Bala Abu Musawa ya jagoranta, ta ziyarci illahirin kananan hukumomin da ke shiyyar Daura a jihar su 12.
A duk kananan hukumomin da aka ziyarta, shugabannin kananan hukumomin sun tarbi tawagar sun kuma zagaya da su a kauyukan da ke cikin kowace karamar hukuma domin duba ayyukan da ake gudanarwa na ci gaban al’umma.
Alhaji Bala Abu Musawa ya ce wannan ziyara na da nufin karfafa guiwa ga shugabannin kananan hukumomin na su kara azamar aiwatar da ayyuka ga alummominsu.
Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC ya ce gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda a jihar ba ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin ta samar da saukin rayuwa ga mutanen da ke lungu da sako na jihar.
Shiyyar Daura sai ta kunshi kananan hukumomin Mani, Bindawa, Mashi, Dutsi, Kankia, Kusada, Ingawa, Daura, Sandamu, Mai’adua, Baure da Zango.

Hukumar Kwastam a Nijeriya ta fara siyar da kayan abinci ga Yan kasar.

 Hukumar hana fasa kwauri a Nijeriya (NCS) ta kaddamar da wani shiri na rage karancin abinci a Najeriya. 

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam (CGC), Bashir Adewale Adeniyi MFR, ya bayyana kudirinsa na ganin ya dace da shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na magance matsalar karancin abinci ta hanyar tabbatar da wadatar kayan abinci ga ‘yan Nijeriya ana siyar da shinkafar Naira 10,000 akan kowane buhu 25kg.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rabon shinkafar a Legas a ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairu, 2024, CGC Adeniyi ya jaddada cewa za a yi rabon shinkafar ne a wuraren da ake gudanar da ayyukan kwastam, tare da tabbatar da samun masu amfana kai tsaye.

 Adeniyi ya jaddada mahimmancin tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin shirin rabon, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da ke shiga wannan shiri da su guji sayar da shinkafar a kasuwanni ko kuma tara ta domin wasu dalilai da ba na cikin gida ba.

Inda ya bayyana cewa hukumar ta kwastam ta samu amincewar gwamnati na bayar da kayayyakin abincin da aka kama ga mabukata a kan farashi mai rahusa bayan ta gamsu da aikin tantance lambar shedar dan kasa ta (NIN).

Na daina badala a Tik-tok- Zanaib Daura

 Kungiyar masu amfani da shafukan sada zumunta ta garin Daura a jihar Katsina sun ziyarci gidan wata matashiya ‘yar Tik-tok da ta dauko salo irin na Murja Kunya. 

Kungiyar ta DESOMF ta ce bayan ganawa da Zainab sun samu fahimtar juna da ita inda ta yi alkawarin cewa ba za ta kara aikata badala ba a shafint

a.

Mahadi Shehu ya kai ‘yan sanda kara kotu

Dan kasuwar nan Malam Mahadi Shehu ya garzaya kotu, inda ya ke karar rundunar ‘yan sandan Nijeriya da  Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar da kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja bisa zargin an tauye masa hakki.
Malam Mahadi Shehu ya yi zargin cewa an kama shi tare da tsare shi ba bisa ka’ida ba bisa.
Mahadi Shehu dai na neman a biya shi diyyar kudi Naira milyan 100 kan wannan batu.
An dai saka ranar 28 ga wannan wata na Fabrairu, 2024 don fara sauraren karar.

Zakzaky ya dawo Nijeriya bayan watanni 5 yana jinya a Iran

 Zakzaky ya dawo Nijeriya bayan watanni 5 yana jinya a Iran

Bayan shafe watanni biyar suna jinya a kasar Iran, Jagoran mabiya mazahabar Shi’a a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Zeenah, sun dawo Abuja.

Jagoran na mabiya Shi’a ya samu kyakkyawar tarba daga dubban magoya bayansa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.

Kafin daga bisani ya wuce filin wasa na Moshood Abiola domin yin gagarumin liyafa.