Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 459

‘Yan bindiga sun hallaka Kwamandan jami’an sa kai na ‘Community Watch Corp’ a jihar Katsina

Sanusi Hassan Gambo, wanda tsohon jami’in dan sanda ne da ya yi ritaya, DCL Hausa ta samu labarin cewa dama ya takura wa ‘yan ta’addar da ke aiki a wannan yanki na karamar hukumar Kankara.
Majiyar DCL Hausa ta tabbatar da cewa Kwamandan ya fita aiki ne tare da jami’an ‘yan sanda na ‘mopol’ a lokacin da ya cimma lokacinsa. Sai dai had yanzu babu takamaiman halin da su ‘yan sandan da suka fita aiki tare suke ciki ya zuwa lokacin hada wannan labari.
Lamarin dai ya faru ne da safiyar Larabar nan a cikin dajin Kankara a lokacin da rahotanni suka nuna cewa sun je kakkabe wasu ‘yan ta’adda ne.
A watan Oktobar, 2023 ne Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya kaddamar da jami’an sa kan na Community Watch Corp’ su 2,400 domin tallafar jami’an tsaron gwamnati a yaki ‘yan ta’adda.

Ma’aikatan Jihar Neja sunfara yajin aikin sai Baba tagani.

 Ma’aikatan Jihar Neja sunfara yajin aikin sai Baba tagani. 

Kungiyar kwadago a jihar Neja ta sanar da daukar matakin fara yajin aiki na masana’antu wanda zai fara aiki daga ranar Laraba 21 ga Fabrairu, 2024.

 A cikin wata wasika da ta aikewa gwamnatin jihar Neja ta ofishin sakataren gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar shugaban kungiyar NLC na jihar Idris A. Lafene da shugaban kungiyar TUC na jihar Ibrahim Gana.

 matakin zai cigaba har sai gwamnati ta warware duk wata takaddamar da ke tsakaninta da kungiyar kwadago ta jihar.

Kungiyar kwadagon ta bukaci gwamnatin jihar da ta sauya duk wasu nade-naden siyasa a matsayin manyan daraktocin kudi, ayyuka da gudanarwa na  hukumomi.

Haka kuma ta bukaci gwamnati da ta sauya nadin shugabanni da mambobi da kwamishinonin dindindin na hukumar ma’aikatar kananan hukumomi da na hukumar da kuma nadin manyan daraktoci na wasu hukumomi.

Za a hukunta ‘Yansandan da ke amfani da sunan IGP wajen aikata ba daidai ba.

 Za a hukunta ‘Yansandan da ke amfani da  sunan IGP wajen aikata ba daidai ba. 

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun ya yi kakkausar suka ga duk wani nau’i na karbar kudi tare da yin gargadi ga duk wani jami’in da ya yi amfani da su ko kuma a sakaya sunansa wajen aikata miyagun ayyuka.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa Sufeto Janar din ya nuna matukar damuwarsa, inda ya jaddada cewa irin wannan aika-aikar na zubar da mutuncin sa da kuma rundunar ‘yan sandan Nijeriya, wanda hakan ke zubar da mutuncin jama’a.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Laraba.

IGP din ya jaddada cewa duk wani jami’in da aka samu da laifin yin amfani da sunansa da laifin zamba ko karbar kudi zai fuskanci hukunci mai tsanani. Daga nan sai ya bukaci jami’an da su tabbatar da gaskiya da sanin ya kamata, yana mai jaddada cewa mutuncin rundunar ‘yan sandan Nijeriya na cikin hadari idan ba a duba irin wannan ba, ‘’in ji sanarwar.

Gwamnatin Dikko ta dora harsashin gina jihar Katsina yadda ya kamata – Bala Abu Musawa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya sanar cewa gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda a jihar ta dora harsashin gina jihar mai kwari da za a mora shekara da shekaru.
Alhaji Bala Abu Musawa na magana ne a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin duba wasu ayyuka da aka assasa a kananan hukumomin Sandamu, Baure, Zango da Mai’adua a shiyyar Daura jihar Katsina.
Ya ce ire-iren tsare-tsaren ayyukan ci gaban da gwamnatin APC a jihar Katsina ta zo da su, za su sauya rayuwar mutanen jihar da kara inganta musu rayuwa.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC din, wanda shi ne Ci Garin Musawa, ya ba da tabbacin cewa, a gwamnatin nan da Malam Dikko Umaru Radda ke jagoranta, jihar Katsina za ta zamo a sahun gaba wajen ci gaba ba ma a Nijeriya ba, har ma a idon duniya.
A duk kananan hukumomin da aka ziyarta, tawagar ta samu duba wasu ayyuka a lunguna da sako na wadannan kananan hukumomi domin tabbatar da ingancin aiki da kara karfafa guiwa ga ‘yan kwangilar da ke gudanar da wadannan ayyuka, na su kammala cikin lokacin da aka kayyade musu.
Daga cikin tawagar akwai Hon Ya’u Umar Gwajo-gwajo, mai ba Gwamna shawara ta musamman kan harkokin siyasa da Hon Shafi’u Abdu Duwan da Hon Shehu Kabir Jani da Alhaji Sabo Musa Hassan da Mamman Yaro Batsari da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC ta jihar Katsina.

Hukumar kwastam ta bayyana shirinta na raba kayan abinci ga yan Najeriya

Dangane da halin kunci da ake fama dashi a Najeriya, hukumar kwastam ta bayyana shirin ta na raba kayan abinci da da hukumar ta kama ga ‘yan Najeriya.

Shugaban Hukumar Bashir Adewale Adeniyi, ya ce za a raba kayan abincin ne bayan an tantance mutane.

Hakan dai na a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Maiwada ya fitar a yau Talata, Adeniyi ya jaddada aniyarsa na shirin samar da abinci kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya ƙudiri aniya.

Ƙudirin kafa yan sandan jihohi ya tsallake karatu na biyu a majalisa

0

Majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar karatu na biyu, daftarin da ke neman yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 ta hanyar ba jihohi 36 na tarayyar kasar damar kafa ‘yan sandan jihohi.

A zaman majalisar na yau Talata an yi muhawara kan kudirin dokar da ke neman yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, inda aka yi karatu na biyu.

Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu da wasu mutane 14 suka dauki nauyin kudurin.

‘Yan sanda sun tabbatar da mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai a jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kai hari a kauyen ‘Yar Nasarawa a karamar hukumar Faskari ta jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya aike wa DCL Hausa, ta ce ‘yan bindigar sun kashe mutane 6, sun kuma raunata 10.
Kazalika, sanarwar ta ce ‘yan bindigar sun kone gidaje 3 da motoci kusan 10. Tuni dai jami’an tsaro sun kewaye yankin a yunkurin kama wadanda suka yi wannan aika-aika.
Da sanyin safiyar Talatar nan, DCL Hausa ta ba da labarin cewa wasu ‘yan ta’adda sun farmaki kauyen ‘Yar Nasarawa a karamar hukumar Faskari, inda har suka kone wani mutum da ransa.

‘Yan bindiga sun kai mummunan hari kusa da sansanin sojoji a Katsina

Wasu ‘yan ta’adda da har zuwa lokacin hada wannan labari ba a tabbatar da adadinsu ba, sun hallaka wani mutum ta hanyar kone shi da ransa a kauyen ‘Yar Nasarawa da ke cikin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Majiyar DCL Hausa a yankin, ta tabbatar da cewa maharan sun shiga kauyen ne da daren Litinin wayewar Talatar nan, inda a jimilce suka kashe mutane 8.
Kazalika, ‘yan ta’addar, an rawaito cewa sun kuma kona shaguna akalla 6, da rumbunan hatsi 7 da gidaje akalla 6 da motoci da baburan da har yanzu ba a kai ga tantance ko nawa bane.
Bugu da kari, a yayin harin, bayanai sun zo wa DCL Hausa cewa an raunata mutane da dama sannan ‘yan ta’addar sun kwashi mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba.
Sai dai, a kauyen Maigora, daya daga cikin mazabu a karamar hukumar ta Faskari, nan ma wasu maharan ne suka yi dirar mikiya, suka yi awon-gana da dabbobin da ba a san adadinsu ba ya zuwa yanzu.
Haka kuma, duk a daren na Litinin wayewar Talatar nan, wasu maharan sun kutsa kai kauyen Ruwan Godiya duk a karamar hukumar ta Faskari, inda suka yi ayyukan ta’addancin da har ya zuwa lokacin hada wannan labarin ba a kammala tantance yawan barnar da suka yi ba.
Kauyen ‘Yar Nasarawa dai bai fi nisan kilomita 5 ba zuwa babbar hedikwatar karamar hukumar Faskari. Sannan a kusa da su akwai sansanin nan na sojoji da ake kira da ‘Army Super Camp, Faskari’ da aka bude tun zamanin Lt. Gen Turkur Yusuf Buratai na babban hafsan sojin Nijeriya.
Karamar hukumar Faskari, na iyaka da jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Nijeriya.

Nijar: Janar Tiani ya yi wa gwamnatinsa garanbawul

 Nijar: Janar Tiani ya yi wa gwamnatinsa garanbawul

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar Janar ABDOURAHAMANE Tiana ya yi wa gwamnatin sa kwarya kwaryar garan bawul

Sakataren gwamnatin kasar ya bayyana hakan ta kafar talabejin din kasar

Kuma wannan garan bawul ya shafi ma’aikatu uku ne da suka hada da ta ma’adanai, ta man fetur da ta makamashi inda aka nada musu sabbin ministoci

ECOWAS na shirin dage takunkumin da ta sanyawa Nijar

 

ECOWAS na shirin

dage takunkumin da ta sanyawa Nijar

Kungiyar ECOWAS za ta dage wa Nijar takunkumin da ta labta mata tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin 2023

Jaridar Jeune Afrique ce ta ruwaito hakan inda ta ce wasu daga cikin ministocin kasashen Afirka ta Yammar ne suka shaida mata hakan

Wasu rahotanni na cewa dai a ranar 24 ga watan nan na Febarairu ne kungiyar za ta gudanar da wani taro wanda a yayin sa ne za ta cire wa Nijar din takunkumin tattalin arzikin