Rahotanni daga garin Ibadan babban birnin jihar Oyo na cewa wasu matasa sun fito zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a fadin Nijeriya.
Majiyar DCLHausa ta Nigerian Tribune ta ce matasan sun mamaye manyan titunan Ibadan dauke da kwalaye da rubutun cewa gwamnati ta hanzarta magance matsalar tsadar abinci.
Nijeriya dai na cikin wani yanayi na tashin gwauron zabo da kayayyakin masarufi ke yi tun musamman ma a wannan shekarar ta 2024.
“Babu dalilin da zai sa Tinubu ya yi murabus” martanin APC ga PDP
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya dage cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba zai yi murabus ba saboda halin kuncin da tattalin arzikin kasa ke ciki.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim ya sanya wa hannu, yayin da yake mayar da martani ga gwamnonin jam’iyyar PDP da suka yi kira ga shugaban kasar da ya yi murabus saboda halin kuncin da kasar ke ciki.
A cewarsa, kiran da gwamnonin jam’iyyar adawa suka yi ba wani abu ba ne illa wani yunkuri na karkatar da hankalin jama’a da ya kamata su shagaltu da goyon bayan kokarin shugaban kasar na kawo saukin tattalin arziki ga al’ummar Nijeriya.
Dokta Alheri Ibrahim-Sanchi, Daraktan Kula da Dabbobi na Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Jihar Kebbi, ya ce gwamnatin jihar ta kara kaimi wajen ganin an dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye da ta haifar da mummunar barna a jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida jim kadan bayan fitar da wata gona da ta kamu da cutar da ke kauyen Amanawa, Kalgo, wajen Birnin Kebbi a ranar Lahadi.
Ya zuwa yanzu cutar ta kashe dawisu 14 a wurin da abin ya shafa.
Tawagar kwararru a karkashin “Kiwon Lafiya Daya” ne suka gudanar da fumigation, wadanda suka hada da kwararru daga ma’aikatun kiwon dabbobi, lafiya sa kuna na muhalli.
Kungiyar nan mai zaman kanta da ke ba da rahoton ayyukan hajji da Umrah ta Independent Hajj Reporters IHR ta ja hankalin hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON da ta kama tare da gurfanar da duk wanda suka kama da laifin damfara da ke yada labaran da ba su inganta ba.
Shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Muhammad a cikin wata sanarwa da ya aike wa DCL Hausa, na martani ne kan wata sanarwa da aka yi ta yadawa cewa hukumar NAHCON na daukar ma’aikata musamman na lafiya da ‘yan jarida da za su yi aikin wucin-gadi a aikin hajjin shekarar nan 2024.
Kungiyar ta yaba da yadda hukumar NAHCON ta gaggauta fitar da sanarwar musanta wannan labari. Sannan kungiyar ta karfafi guiwar hukumar NAHCON da ta bi diddigi don kamo wadanda suke kitsa wannan bahallatsa.
IHR ta tunaso cewa ko a aikin hajjin shekarar 2023 da ya gabata, sai da aka samu wasu bata-gari suka kirkiri wani shafi suka rika tura wa mutane cewa su cika Yariman Saudiyya ya dauki nauyin aikin hajji ga ‘yan Nijeriya a kyauta. Sai dai ko a lokacin sai da aka bi diddigi aka gano, ashe wasu ne a jihar Oyo suka kitsa wannan kitimirmira.
Sabanin jita-jitar da ake ta yadawa cewa fitacciyar jarumar Tiktok, Murja Kunya ta tsere daga gidan yari, kakakin gidan gyaran hali na Kano, Musbahu Kofar Nassarawa ya ce an sake ta ne biyo bayan umarnin kotu.
Kofar Nassarawa ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an sake ta tun ranar Alhamis.
“Kotu ce ta kawo mana ita domin a ci gaba da tsare ta, kuma kotun ce ta ba mu umarnin mu sake ta,” in ji shi.
Gwamnan Katsina Dikko Radda ya kafa dokar hana boye kayan abinci a jihar
Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya saka hannu kan dokar da za ta hana mutane boye kayan abinci.
Kafa wannan doka na nufin hana wasu ‘yan kasuwa da ake zargi da boye kayan abinci a rumbuna daban-daban don kayan abincin su yi tsada.
Kazalika Gwamnan ya kafa wani kwamiti na musamman da za a dora wa alhakin bi lungu da sako na jihar don zakulo mutanen da suke boye kayan abinci.
Dokar ta haramta duk wani yunkuri na boye kayan abinci a duk fadin jihar. Kazalika, dokar ta lissafta kayan abinci da suka hada da shinkafa, masara, gero, dawa, waken suya, gyada da ma duk wani nau’in kayan abincin da karancinsa zai jefa al’ummar jihar Katsina cikin halin ha’ula’i.
Bugu da kari, wannan doka ta fayyace karara cewa duk mutumi ko kamfanin da aka samu da laifin boye kayan masarufi, to ya saba dokar da za a iya hukunta shi karkashin sashe na 114 a kundin penal code.
Sannan hatta wurin da aka kama cewa ana boye wadannan kayan abinci, za a barke shi a fitar da abincin don sayar wa al’umma a farashin da ya dace.
Ta bangaren kwamitin karta-kwana na task force da Gwamnan ya kafa kan wannan batu kuwa, an dora masa alhakin zakulo masu boye kayan masarufin a cikin jihar.
Bugu da kari, an kwamitin zai hada da jami’an tsaro don su kamo tare da gurfanar da wadanda aka samu da laifin. Kazalika, kwamitin zai gana da masu ruwa da tsaki kan harkar kayan masarufi a jihar don gudun kitso da kwarkwata.
Sannan wannan kwamitin zai rika kula da yadda ake safarar kayan abincin, daga sassan jihar daban-daban da ma tsallakawa da shi kasashen waje.
Ana kyautata zaton kwamitin zai kunshi shugaba da karin mambobi 10 da za su gudanar da wannan aiki.
Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda PhD ya rarraba hannu kan wannan doka a ranar Juma’ar nan 16 ga watan Fabrairun, 2024.
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a GRA, Zaria jihar Kaduna ta umurci da Hon Sani Sha’aban dan takarar Gwamna a jihar karkashin jam’iyyar ADP a zaben da ya gabata da ya biya bashin Naira milyan 11.2 da wani Alhaji Umar Faruq Abdullahi ke binsa.
Alkalin kotun Alhaji Ishaq Madahu da ya ya ke hukuncin, ya kuma umurci da a kwace kadarar Hon Sani Sha’aban da ya ba da ita a kafin a bashi wancan bashin.
Kazalika, kotun ta umurci da a gaggauta neman wanda zai sayi wannan kadara, domin a biya wannan bashi da ake bin Hon Sani Sha’aban, har kotun ta ce idan kudin wannan kadarar ya zarta kudin bashin da ake binsa, za a maido masa da sauran.
Haka kuma kotun ta umurci Hon Sani da ya yo ciko muddin wannan kadarar ba ta kai yawan kudin da ake binsa ba.
Idan za a tuna dai, an sa hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Hon Sani Mahmud Sha’aban (Dan Duran Zazzau) da Alhaji Umar Faruq Abdullahi don fitar da shi (Hon Sha’aban) daga wata matsala a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE a shekarar 2018.
To a wannan makon dai Masara ta fi sauki a yankin Arewacin Nijeriya sama da kudanci, inda a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano aka sayar da buhun Masara mai cin kwano 40, kan kudi N57,000, haka batun ya ke a kasuwar Mai’adua jihar Katsina, yayin da a kasuwar Mile 12 International Market Lagos, farashin buhun ya kama N60,000, daidai.
A makon nan dai, an sayar da buhun Masarar a kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kan kudi N62,000-65,000 Amma a kasuwar Song na jihar kuwa aka sayar da Masarar N58,000. Sai dai fa batun ya sha bamban a kasuwar Gwalantabal da ke yankin karamar Hukumar Song duk a jihar Adamawa, inda farashin Masarar ya kama N53,500, amma a kasuwar Monday Market, Maduguri, jihar Borno farashin buhun Masarar ya kama N55,000.
Bisa ga dukkan alamu dai, ana ci gaba da samun sauki a yankin arewacin kasar nan, inda aka sayi buhun Masarar a wannan makon kan kudi N42,000 a kasuwar Kashere da ke karamar hukumar Akko, a jihar Gombe.
To Idan muka leka kasuwar Giwa a jihar Kaduna Buhun Masarar ya kama N51,000 a wannan makon.
Ta bangaren shinkafar gida kuwa, babban buhu an sai da shi kan kudi N120,000 a kasuwar Giwa jihar Kaduna, kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuma farashin buhun Shinkafar ya kama N115,000, a kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuma kudin shinkafar Hausar ya kama N110,000. Sannan akwai kasuwar Monday Market Maduguri, jihar Borno da aka sayar da shinkafar Hausa N108,000.
A kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa kuma, an sayar da buhun shanshera na shinkafar mai L N40,000 -43,000. A kasuwar Kashere ta jihar Gombe ma dai batun bai sauya zani ba, kudin N40,000-43,000.
Ita kuwa shinkafar waje ta fi sauki a kasuwar Monday Market, Maduguri a jihar Borno, inda ake sayar wa kan kudi N60,000. Sai dai an samu ‘yar tazarar N5,000, tsakanin jihohin Adamawa da Borno, yayin da a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawar ake sayar da shinkafar N65,000, sai kuma kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kudin buhun shinkafar ya kama N70,000 ita ma dai Kasuwar Mile 12 International Market Lagos kuɗin shinkafar bature N70,000 ne a wannan makon.
A ɓangaren taliyar Spaghetti kuma N12,500 ne a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, ita ma dai kasuwar Monday Market, Maiduguri a jihar Borno haka zancen ya ke, sai kasuwar Kashere da ke jihar Gombe N12,700, a kasuwar Mile 12 International Market Lagos farashin kwalin taliyar ya kama N14,000, sai kasuwar Giwa jihar Kaduna kuma kuɗin Spaghetti ‘yar Waje N18,000 daidai.