Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 46

Amurka za ta kashe $413m kan yaƙi da matsalar tsaro a Nijeriya da Afirka a 2026

Gwamnatin Amurka ta ware kusan Naira biliyan 587 domin ayyukan yaki da ta’addanci a Nijeriya da wasu kasashen Afirka a shekarar 2026, sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin Yammacin Afirka.

Kudaden suna cikin Dokar Kasafin Tsaron Amurka ta 2026 (NDAA), wadda ta amince da kashe dala miliyan 413.046 ga rundunar sojin Amurka a Afrika (AFRICOM), kamar yadda takardun da aka samu suka nuna. Dokar ta samu sahalewar Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar 18 ga Disamba, 2025.

Kasafin ya zo ne a lokacin da Nijeriya ke fama da ta’addanci a Arewa maso Gabas, fashin daji a Arewa maso Yamma, da kuma laifukan teku a Tekun Guinea, yayin da kasashen Mali da Benin ke fama da hare-haren ‘yan jihadi daga yankin Sahel.

Dokar ta kuma tanadi kafa ofishin Mataimakin Sakataren Harkokin Afirka a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, domin sa ido da daidaita manufofin Amurka a Afirka ta Kudu da Sahara, tare da bibiyar tasirin dabarun soja na Rasha a nahiyar.

Har yanzu tattalin arzikin Nijeriya na girgidi, bai tsaya da kafafunsa ba in ji bankin duniya da IMF

0

Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) sun bukaci Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomi su dauki tsauraran matakai domin rage hauhawar farashi, duk da cewa ana samun wasu ci gaba a bangaren tattalin arziki a Nijeriya.

Manyan jami’an biyu, wato Babban Masanin Tattalin Arziki na Bankin Duniya a Nijeriya, Dokta Samer Matta, da Wakilin IMF a Nijeriya, Dokta Christian Ebeke, sun bayyana haka ne a Legas yayin taron NESG na hasashen tattalin arziki na 2026. Sun amince cewa gyare-gyaren tattalin arziki na haifar da ci gaba, amma sun jaddada cewa hauhawar farashi har yanzu na da yawa.

Dokta Ebeke ya gargadi Nijeriya kan yin sakaci da tunanin cewa a riga an kammala aiki, yana mai cewa komawa tsoma bakin gwamnati wajen daidaita farashi da kasuwa ba zai dore ba. Ya bukaci gwamnatocin tarayya da jihohi su tabbatar da ingancin kashe kudade domin amfanin ya isa ga rayuwar talakawa.

A nasa bangaren, Dokta Matta ya ce kodayake hauhawar farashi na raguwa, har yanzu babbar barazana ce ga jin dadin al’umma. Ya bukaci a mayar da hankali kan kashe kudi a bangaren jin dadin jama’a, musamman ilimi, lafiya da kariyar zamantakewa, yana mai cewa jihohi na da karin kudade kuma dole su yi amfani da su yadda ya dace.

‘Yan Nijeriya sun sha litar fetur 63.7m a Disambar 2025 – NMDPRA

0

Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta bayyana cewa matatar Dangote ta samar da lita miliyan 32.02 na man fetur (PMS) a cikin Disamba 2025, daga cikin jimillar lita miliyan 63.7 da Nijeriya ta yi amfani da su a lokacin.

Takardar bayanai da hukumar ta fitar ta nuna cewa matatar Dangote ta kai kashi 71 cikin 100 na aiki a watan, daga burin lita miliyan 50 da ta sanya, yayin da samar da PMS ya karu daga lita miliyan 19.5 zuwa kusan lita miliyan 32 a rana.

Hukumar ta ce bayanan ba su hada da ajiyar man fetur da matatar ta ware wa kasuwar cikin gida ba, domin alkaluman amfani sun ta’allaka ne da man da aka kai kasuwa ta hanyar manyan motoci. Ta kuma tabbatar da cewa matatun NNPC uku ba su samar da fetur ba, duk da cewa an fitar da tsohon dizal daga matatar Fatakwal kafin rufewarta a Mayu 2025.

Rahoton ya kara da cewa saboda bukukuwan karshen shekara, an shigo da lita miliyan 42.2 a rana domin cike gibin bukata, yayin da wasu kananan matatu suka cigaba da samar da dizal. NMDPRA ta ce wadannan bayanai na nuna ci-gaban Nijeriya wajen rage shigo da man fetur daga waje da karfafa samarwa a cikin gida.

Kotu a jihar Kano ta bulale wani mutum ta kuma tura shi Islamiyya don koyon ilmin addini

0

Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano da ke Kofar Kudu ta yankewa wani mutum mai suna Khalifa Auwal hukuncin aikin al’umma na tsawon watanni shida, bayan samunsa da laifin shiga gona ba da izini ba da kuma sata.

Lauyan gwamnati ya shaida wa kotu cewa an kama Auwal ne a yayin da yake yanke sandunan karfe a wurin aikin ginin gadar Tal’adu da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifukan da ake masa a gaban kotu. A hukuncinsa, Alkali Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini ya umarci a yi wa Auwal bulala 50 tare da ɗaure shi da aikin al’umma na tsawon watanni shida.

Alkalin ya kuma bayar da umarnin cewa Auwal ya yi karatun fikihu a makarantar Islamiyya karkashin kulawar Audu Dan Hajiya, wani jami’in kotu, a matsayin wani bangare na gyaran tarbiyyarsa.

Wani mai sana’ar faci ya sace kansa, ya nemi ‘yan’uwansa su biya kudin fansa N12m

0

Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta kama wani mai sana’ar faci mai shekaru 34 mai suna Idris Isiaka, bisa zargin kirkirar sace kansa domin karbar kudin fansa daga iyalansa. Lamarin ya faru ne a Emaudo, Ekpoma da ke Karamar Hukumar Esan West.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Eno Ikoedem, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Janairu, inda Isiaka tare da wasu abokan aikinsa biyu da ke gudun hijira suka yada labarin sace shi a kafafen sada zumunta tare da neman kudin fansa Naira miliyan 12.

Ya ce bayan kirkirar satar, nan take suka shirya yada labarin ta hannun wani blogger, sannan suka tuntubi iyalan wanda ake zargin da ke Jihar Kogi, suna barazanar kashe shi idan ba a biya kudin fansar ba.

Ikoedem ya ce dan’uwan wanda ake zargin ya sayar da kadarorinsa tare da biyan wani bangare na kudin fansar, wanda daga bisani Isiaka ya raba da abokan aikinsa. Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.

Atiku ya ce ɗansa na da ‘yancin shiga APC kuma ra’ayinsa ne na kashin kansa

0

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ce matakin ɗansa Abba Abubakar na shiga jam’iyyar APC zabin kansa ne, kuma bai da wani tasiri a kan siyasar sa ko tsayuwarsa kan matsalolin da suka addabi ƙasa.

Atiku ya bayyana cewa a dimokuraɗiyya, ’ya’ya na da ’yancin ra’ayi, kuma shi a matsayinsa na dattijo mai bin ka’ida, ba ya tilasta wa ’ya’yansa abin da ya saba musu — balle ma tilasta wa ’yan Nijeriya.

Sai dai ya jaddada cewa babban abin da yake damunsa ba batun sauyin jam’iyya ba ne, ƙuncin rayuwa da koma-bayan tattalin arziki da mulkin APC ya haifar wa ƙasa da talakawa.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya ce yana nan tsayin daka tare da sauran ’yan kishin ƙasa domin nemo mafita, dawo da ingantaccen mulki, da kawo sabuwar fata ga ’yan Nijeriya.

Babu wani sabon harajin VAT da muka ce za mu karba domin amfani da banki – Shugaban hukumar tattara haraji ta Nijeriya

0

Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya (NRS) ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa an fara kakaba harajin VAT kan ayyukan banki kamar tura kudi ta waya, kudaden caji da kwamitoci. Hukumar ta ce labaran ba su da tushe kuma suna yaudarar jama’a.

Mai bai wa Shugaban NRS shawara kan harkokin yada labarai, Dare Adekanmbi, ya bayyana a Abuja cewa harajin VAT tun tuni yana aiki kan kudaden caji da bankuna ke karba, ba sabon abu ba ne a karkashin Dokar Haraji ta Nijeriya (Nigeria Tax Act). Ya ce dokar ba ta kirkiro sabon haraji kan kwastomomin banki ba.

Adekanmbi ya ce VAT na aiki ne kawai kan kudin hidima da banki ke karba, kamar kudin tura kudi, USSD, katin ATM da kula da asusu, ba kan adadin kudin da ake turawa ba. Misali, idan banki ya karbi naira 10 a matsayin kudin tura kudi, VAT kashi 7.5 cikin 100 zai hau kan naira 10 din kacal.

Hukumar ta kuma jaddada cewa ribar ajiya ba ta da VAT, haka nan kayan abinci na asali, harkokin lafiya da ilimi duk an ware su daga VAT. NRS ta bukaci jama’a su yi watsi da bayanan bogi tare da dogaro da sahihan bayanai daga hukumomin gwamnati kawai.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu gurbin karatun digiri na farko a fannin Shari’a a Jami’ar Northwest da ke Kano

0

Jami’ar Northwest da ke a Kano ta amince da ba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, gurbin karatu na musamman a shirin LL.B (Common Law da Shari’a).

Wata wasiƙa mai kwanan wata 12 ga Janairu, 2026, wadda shugaban sashen jarrabawa da shigar dalibai na jami’ar, Jafaru Muhammad, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an ba Sarkin gurbin ne bayan ya cika sharuddan da ake bukata na shiga ta musamman.

Wasiƙar ta ce za a fara karɓar Sarkin a mataki na 200 a Kwalejin Shari’a, tun daga zangon karatu na 2024/2025, kuma dole ne ya bi duk ƙa’idojin da ke cikin kundin dokokin dalibai na jami’ar.

Jami’ar ta kuma bukaci Sarkin da ya kammala rajistarsa ta hanyar gabatar da kansa ga sassa daban-daban da suka hada da sashen shigar dalibai, ICT, asusu, ɗakin karatu da kuma sashen harkokin dalibai.

PDP tsagin Turaki ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta inganta walwala da Jin dadin sojoji domin karfafa tsaron Nijeriya

0

Kwamitin Zartarwa na Kasa na jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin Tanimu Turaki (SAN), ya bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta fifita inganta walwala da jin dadin jami’ai da sojojin rundunar tsaro domin karfafa kwarin gwiwa da tsaron kasa.

Turaki ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, yayin da ake bikin Ranar Tunawa da Sojoji ta 2026, inda ya jaddada cewa bayar da cikakken tallafi ga rundunar soji na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Nijeriya.

Ya kuma bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta kara kasafin kudi ga hukumomin tsaro, domin su samu damar yaki da matsalolin tsaro yadda ya kamata tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasa.

A cewarsa, “A wannan rana ta Tunawa da Sojoji, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan jaruman sojojin da suka rasa rayukansu yayin kare ’yancin kai da mutuncin Nijeriya. Muna kuma kira da a tabbatar da walwala da jin dadin jami’an tsaro domin gudunmuwar da suke bayarwa kada ta zama a banza, tare da rokon Allah Ya ji kan jaruman da suka sadaukar da kansu wajen kare kasa.”

‘Yan bindiga sun sace sama da shanu 500 a kasuwar Kauran Namoda da ke a Jihar Zamfara

0

Yan bindiga dauke da makamai sun kwashe shanu sama da 500 a Kasuwar Daji, Karamar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.

Shugaban MACBAN a jihar, Aminu Garba, ya ce harin ya faru da daddare, inda ’yan bindigar da suka haura 50 suka tsere ta bangaren daji. Ya ce an samu dawo da kusan shanu 60 daga cikin wadanda suka watse.

Wani wanda abin ya shafa, Alhaji Sani Yaba Ajiyan Fawa, ya koka kan rashin daukin gaggawa duk da kusancin jami’an tsaro, yayin da MACBAN ke cewa ana daukar matakai domin gano sauran shanun.