Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 47

‘Yan bindiga sun sace sama da shanu 500 a kasuwar Kauran Namoda da ke a Jihar Zamfara

0

Yan bindiga dauke da makamai sun kwashe shanu sama da 500 a Kasuwar Daji, Karamar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.

Shugaban MACBAN a jihar, Aminu Garba, ya ce harin ya faru da daddare, inda ’yan bindigar da suka haura 50 suka tsere ta bangaren daji. Ya ce an samu dawo da kusan shanu 60 daga cikin wadanda suka watse.

Wani wanda abin ya shafa, Alhaji Sani Yaba Ajiyan Fawa, ya koka kan rashin daukin gaggawa duk da kusancin jami’an tsaro, yayin da MACBAN ke cewa ana daukar matakai domin gano sauran shanun.

Kashim Shettima ya jagoranci sakin tsuntsaye a bikin ranar tunawa da sojoji ta 2026

0

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya jagoranci manyan jami’an gwamnati wajen sakin tsuntsaye a bikin Ranar Tunawa da Sojoji ta 2026, a matsayin alamar kudirin Nijeriya na zaman lafiya, hadin kai da ’yanci.

An gudanar da bikin ne tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Babbar Alkalin Alkalan Nijeriya, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, da sauran manyan baki. An wallafa bidiyon taron ne a ranar Alhamis ta hannun Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Nijeriya kan Harkokin Watsa Labarai (Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), Stanley Nkwocha.

Tsuntsayen da aka saki sun tashi nan take, abin da masu kallo suka bayyana a matsayin alama ta kimar sadaukarwa da jaruman sojojin Nijeriya da suka rasu suka bayar domin kare kasa.

Ana gudanar da Ranar Tunawa da Sojoji a ranar 15 ga Janairu duk shekara, domin girmama ’yan rundunar sojin Nijeriya da suka sadaukar da rayuwarsu a bakin aiki, ciki har da Yakin Basasa, ayyukan wanzar da zaman lafiya, da kuma yaki da ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta yi karin haske kan bidiyon mazauna kauyen Tidibale da ƴan bindiga suka kora daga gidajensu

0

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ce mutanen da aka gani a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, ’yan garin Tidibale ne a Karamar Hukumar Isa, amma ba ’yan bindiga suka kore su ba, kamar yadda ake yadawa.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnati, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Alhamis 15 ga Janairu, 2026, inda ya ce an ɗauki matakin kwashe mutanen ne na ɗan lokaci bayan samun jita-jitar cewa ’yan bindiga na shirin kai hari yankin.

Sanarwar ta ce kansilan mazabar Tidibale, Dayyabu Sani, ne ya kai rahoton jita-jitar ga Shugaban Karamar Hukumar Isa, Alhaji Sherifu Kamarawa, wanda daga nan ya bayar da umarnin kwashe mutanen zuwa hedkwatar karamar hukumar a matsayin matakin kariya. Daga bisani, an mayar da mutanen lafiya zuwa gidajensu, yayin da jami’an tsaro suka ƙara sintiri a yankin.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta kuma sanar da amincewa da kafa sansanin sojoji na Forward Operations Base (FOB) a Tidibale domin ƙarfafa tsaro, tare da gargadin jama’a kan yaɗa jita-jita da siyasantar da batutuwan tsaro.

Hakazalika, ta kuma bukaci ’yan ƙasa da su haɗa kai da hukumomi wajen yaki da ’yan bindiga, tare da tona asirin masu bai wa miyagu bayanai a cikin al’umma.

Kotu ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin Nijeriya ta shigar kan Sanata Natasha

0

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar laifi da Gwamnatin Nijeriya ta shigar kan Sanata mai wakiltar Kogi Ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, lamarin da ya kawo karshen shari’ar da ta tayar da kura a fadin Nijeriya.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan Ofishin Babban Lauyan Nijeriya ya shigar da sanarwar janye kara, lamarin da ya sa alkalin kotun, Mai shari’a C. N. Oji, ya goge tuhumar bata suna da sauran laifukan da aka dora wa Sanatar, wadda ta samo asali daga kalaman da ta yi a wata hira ta talabijin.

Mai shari’a Oji ya ce matakin ya nuna bukatar takatsantsan wajen amfani da ikon shigar da kara, yana mai fatan hakan zai karfafa mutunta doka da tsarin dimokuradiyya. Lauyan gwamnati ya tabbatar wa kotu cewa an janye karar ne domin amfanin adalci da amincewar jama’a ga tsarin shari’a.

Da take martani bayan zaman kotu, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce hukuncin ya tabbatar da imaninta ga doka, tana mai jaddada kudirinta na ci-gaba da yi wa al’ummarta hidima da kare ’yancin dimokuradiyya, tare da gode wa lauyoyinta da magoya bayanta.

Jam’iyyun adawa sun yi tir da gwamnatin Nijeriya kan zargin kwangilar Dala miliyan 9 domin toshiyar bakin Amurka

Jam’iyyun ADC, PDP, NNPP da Labour Party sun soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan rahoton amincewa da kwangilar dala miliyan 9 domin yin toshiyar baki a Amurka, suna cewa gwamnati na ƙoƙarin goge hoton Nijeriya a waje alhali jama’a na fama da matsanancin tsaro da wahalar rayuwa.

ADC ta ce kuɗin ya nuna fifiko mara kyau, inda ta jaddada cewa babu wata toshiyar baki da zai ɓoye zubar da jini ko gazawar kare rayuka.

PDP ta ce inganta walwalar ’yan ƙasa ne kaɗai zai gyara hoton ƙasa, ba kwaɓaɓɓen toshin baki ba. NNPP kuma ta bayyana kwangilar a matsayin ɓarna, tana cewa tura jakadu zai fi dacewa wajen sadarwa da ƙasashen waje.

Rahotanni sun ce an ɗauki kamfanin DCI Group ta hannun Aster Legal a madadin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, domin bayyana ƙoƙarin gwamnati kan kare Kiristoci a Amurka.

Sai dai jam’iyyun adawa sun ce kashe irin wannan kuɗi a lokacin da talakawa ke fama da tsaro da tsadar rayuwa ya sabawa hankali, kuma ba zai maye gurbin sahihin tsarin kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya ba.

Tsare-tsaren Tinubu ya sanya Nijeriya kan gaba wajen samun masu zuba jarin makamashi a Afrika – Hadimin Shugaban Nijeriya

0

Nijeriya ta sake zama babbar cibiyar jawo jarin makamashi a yankin Afirka ta Kudu da Sahara, bayan ta karɓi kashi 38 cikin 100 na manyan ayyukan makamashi da aka amince da su a nahiyar cikin watanni 24 da suka gabata.

Mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ta ce ƙasar ta jawo jarin dala biliyan 5.3 a bangaren hako mai da gas a shekarar 2025 kaɗai.

Verheijen ta bayyana cewa wannan ci gaba ya zo ne duk da raguwar kashe kuɗi da kashi 18 cikin 100 a yankin, lamarin da ke nuna cewa Nijeriya ta rabu da koma bayan yankin baki ɗaya. Ta ce gyare-gyaren da aka yi sun dawo da amincewar masu zuba jari, inda Nijeriya ta samu manyan ayyuka 5 daga cikin 8 da aka amince da su a Afirka cikin shekaru biyu kacal.

Ta kara da cewa aikin Shell–Sunlink HI Field (OML 144) da aka amince da shi a 2025, tare da sabbin tsare-tsaren ƙarfafa hako gas da aka ƙaddamar a 2024, sun taka muhimmiyar rawa wajen wannan nasara.

Verheijen ta ce ana sa ran wannan gagarumin ci-gaba zai ci gaba zuwa 2026, tare da bukatar hukumomi su sauya tsofaffin tunani domin sauƙaƙa zuba jari da bunƙasa ƙwarewar ’yan Nijeriya a bangaren makamashi.

Muna alfahari da ku duk da rashin nasarar da aka samu a wasan da aka buga da Morocco a AFCON – Gwamnatin Nijeriya

0

Gwamnatin Nijeriya ta yaba wa tawagar Super Eagles bisa rawar da suka taka a gasar AFCON 2025, tana mai cewa ’yan Nijeriya na alfahari da su duk da ficewarsu a wasan kusa da na ƙarshe.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce ’yan wasan sun wakilci ƙasa da mutunci, jajircewa da haɗin kai.

Ministan ya ce, duk da sun sha kashi, Super Eagles sun nuna halayen da ke dacewa da tutar ƙasa, inda ya jaddada cewa saka rigar kore da fari na nufin jarumta, haɗin kai da rashin yanke ƙauna. Idris ya ce ƙoƙarinsu ya fi muhimmanci fiye da sakamakon wasa kawai.

Super Eagles sun fice ne bayan Morocco ta doke su da bugun fenariti 4–2, bayan wasan ya tashi babu ci har bayan ƙarin lokaci.

Hakazalika, mainistan ya ƙarfafa musu gwiwa da su ɗaga kai, su koyi darasi, su dawo da ƙarfi, yana mai tabbatar musu da ci-gaba da goyon bayan ’yan Nijeriya a kodayaushe.

Gwamnatin Nijeriya ta amince da karin kaso 40 ga albashi malaman jami’a

Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da sabon alawus na farfesoshi wanda zai ba su damar karɓar ƙarin kuɗi sama da ₦140,000 a kowane wata, tare da ƙarin albashi kashi 40 cikin 100 ga dukkan malaman jami’o’in gwamnati.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin hira da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV, bayan cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) bayan shafe shekaru 16 ana takaddama.

A cewar Alausa, yarjejeniyar ta 2025 ta kawo ƙarshen rikicin sake duba yarjejeniyar 2009, inda aka tsara alawus na ilimi guda tara (9) cikin tsari mai kyau, ciki har da sabon tsarin alawus na Farfesa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati ta riga ta fara aiwatar da yarjejeniyar, yana mai cewa an fitar da dukkanin takardun doka da ke goyon bayan walwalar malamai, kuma an tanadi kuɗaɗen da za su tabbatar da aiwatar da ƙarin albashin kashi 40% da sabbin alawus-alawus ba tare da tsaiko ba.

Shugaba Tinubu ya bukaci Sojojin Nijeriya da su kasance masu biyayya ga dimokradiyya

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci dakarun sojin Nijeriya su cigaba da kasancewa masu ladabi, biyayya da haɗin kai, yana mai bayyana su a matsayin alamar ƙarfin bai ɗaya da kuma masu kare dimokuraɗiyyar ƙasa. Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, a bikin Ranar Tunawa da Sojoji ta 2026 (AFCRD).

Tinubu ya ce walwalar sojoji ba ta rabu da tsaron ƙasa ba, inda ya ba su tabbacin ingantattun kayan aiki, horaswa da kyakkyawan yanayin rayuwa, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tallafa musu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.

Shugaban ya kuma jinjinawa jaruman da suka rasu wajen kare Nijeriya, yana cewa tunawa da su hakki ne na ƙasa baki ɗaya, ba wai biki kawai ba. Haka kuma, ya sanar da ƙaddamar da shirye-shirye guda biyu, Thank-A-Soldier Electronic Wall da My Nigerian Hero Campaign domin bai wa ’yan Nijeriya damar girmama sojoji da tsoffin dakarun ƙasa, yayin da aka karrama wasu manyan jami’an soja masu aiki da masu ritaya a taron.

Gwamnatin Nijeriya za ta fara karbar harajin kaso 7.5 ga duk wanda ya yi amfani da banki daga 19 ga Janairun 2026

Gwamnatin Nijeriya ta umurci dukkan bankuna da kamfanonin fintech su fara karɓa da tura harajin VAT kashi 7.5 cikin 100 kan wasu ayyukan banki na zamani daga Litinin, 19 ga Janairu, 2026.

Harajin zai shafi kuɗaɗen hidimar banki irin su cajin tura kuɗi ta waya, USSD, da kuɗin fitar da kati, amma ba zai shafi kuɗin da ake turawa ba, sai cajin hidimar kawai. Misali, idan cajin tura kuɗi N100 ne, VAT zai zama N7.50 kamar yadda bankin Zamani na Moniepoint ya aike da sakonni ga kwastamominsa.

Kamfanin Moniepoint ya ce wannan ba ƙarin farashi ba ne, wajibi ne na doka, kuma ana tura kuɗin kai tsaye zuwa Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS). Ya ƙara da cewa ribar ajiyar kuɗi a asusu ba ta cikin harajin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, matakin na daga cikin shirin gwamnati na daidaita karɓar VAT a harkokin kuɗin dijital da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga, yayin da aka tabbatar wa kwastomomi cewa harajin na VAT za a rika nuna shi a fili a bayanan mu’amala.