Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 461

Mun gaji da ba talakawa hakuri, don suna gab da yi wa gwamnati tawaye – Sarkin Musulmi

0

Mai Alfarma
Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya gargadi gwamnatin Najeriya ta
gaggauta daukar matakin saukaka wa talakawa rayuwa da fatattakar yunwa, matukar
ba haka ba kuma ta kuka da kanta kan matakin da talakawan zasu dauka akanta.

Da ya ke yiwa manema
labarai jawabi a Arewa House da ke jihar Kaduna Sarkin musulmin yace sarakunan
gargajiya dana shugabannin addini sun gaji da tausar talakawa da kuma basu
hakuri, don haka babu makawa illa gwamnati dauki matakin saukaka rayuwa.

Ya ce a yanzu
talakawa sun kai geji kuma tura ta kai bango kana sarakunan gargajiya ba zasu
iya tare talakawa ba  idan suka fusata da
gwamnati.

Ya ce kullum maganar kenan da
gwamnati ke yi musu kan suci gaba da tausar talakawa, har zuwa yaushe ne za’a
ci gaba da bada hakuri? Har zuwa yaushe ne talakawa zasu ci gaba da mutuwa da
yunwa da sunan hakuri? a yanzu lokaci ne da gwamnati zata yi hakuri ta dauki
matakin da ya dace.

“Mun jima muna rokon talakawa, a
yanzu mun gaji, kunyar su muke ji, sun fara daina yarda da maganar mu, don babu
wata alamar sauki daga gwamnati don haka matukar gwamnati bata dawo cikin
hayyacin ta ba, to duk matakin da talakawa suka dauka tabbas ta kuka da kanta”
inji sarki musulmi.

 

 

‘Yan majalisar Najeriya na fatan mayar da shugabancin kasar tsarin Prime minister

0

 

‘Yan majalisar dokokin Najeriya 60 sun kada kuri’a
kan bukatar sauya tsarin tafiyar da gwamnatin Najeriya zuwa tsarin gwamnatin
Prime minister a maimakon shugaban kasa wanda aka fara amfani da shi a
jamhuriya ta farko.

‘Yan mahalisar su 60
sun gabatrwa majalisar wani kwarya-kwaryan kundin tsarin mulki, wanda suke
ganin matukar aka bi shi, za’a yi nasarar mayar da kasar kan tsarin na Prime
minister nan da shekara ta 2031.

 

Da yake yiwa manema labaran fadar shugaban kasa
jawabi bayan gabatar da kundin, mai magana da yawun yan majalisar su 60
Abdulsamad Dasuki, ya ce lokaci yayi da ya kamata a kawo karshen tsarin
shugaban kasa mai cikakken iko a Najeriya, la’akari da tsadar da yake da shi.

Duk da dai ‘yan majalisar sun nuna shakku game da
samun nasarar sauya tsarin gwamnatin kasar nan da shekara ta 2031, amma sun ce
karfin da tsarin shugaban kasa mai cikakken iko ya baiwa shugaban kasar ya yi
yawan da yake janyo ci baya ga kasa.

 

Gwamnatin Najeriya ta sanya Interpol cikin masu bincike kan kwaikwayar sa hannun shugaba Buhari

 


Gwamnatin Najeriya
ta bukaci ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol su sanya wasu mutane uku cikin
jerin wadanda suke nema ruwa a jallo sakamakon zargin su da hada baki wajen
kwaiwakayar sa hannun tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, inda suka fitar
da dala miliyan 6 da dubu dari 230 daga asusun kasar.


Mutanen da ake zargi sun hadar
da Adamu Abubakar da Imam Abubakar da kuma Odoh Eric Ocheme.

Tuni dai gwamnatin kasar ta shigar da
karar mutanen uku, kan zargin satar bayanan tsohon shugaban kasa, yiwa kasa
zagon kasa da yaudarar ma’aikatan gwamnati.

Tun farko mutanen sun rubuta
takarardar bayar da umarnin fitar da wadannan kudi daga asusun gwamnati dauke
da sa hannun shugaba Buhari, sannan suka kaiwa sakataren gwamnati na wancan
lokaci Boss Mustapha wanda ya fitar da kudin, karkashin babban bankin kasar.

Bayanai sun ce an yi
amfani da kudaden ne wajen raba su ga kungiyoyin da ke sanya idanu kan zaben da
aka gudanar a kasa.

 

An kwaikwayi sa-hannun Buhari wajen fitar da kudi dala miliyan 6.2 – Boss Mustapha

 

An kwaikwayi sa-hannun Buhari wajen fitar da kudi dala miliyan 6.2 – Boss Mustapha

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya musanta bayanan da ce cewa gwamnatin da da shude ta amince an fitar da dala miliyan 6.2 da ake zargin an yi amfani da su wajen warewa masu sa ido na kasa da kasa a zaben kasar.

Mustapha wanda ke ba da shaida a ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce an yi amfani da sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na bogi.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da kara da aka yi wa kwaskwarima masu dauke da tuhume-tuhume kusan guda 20.

An kwaikwayi sa-hannun Buhari wajen fitar da kudi dala miliyan 6.2 – Boss Mustapha

0

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha,  ya bayyana cewa an kwaikwayi sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, don ba da izinin cire tsabar kudi dala miliyan 6.2 daga asusun babban bankin Najeriya.

Mustapha wanda ke ba da shaida a ci gaba da shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja a yau Talata, yace sa hannun tsohon shugaban kasar na jabu ne ba na gaskeba.

Da yake bayanin abin da ya faru, Mustapha ya ce shi ko tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su amince da a cire kudaden ba.

Tsadar rayuwa: Gwamnatin tarayya zata kafa hukumar daidaita farashin kayan abinci

0

Gwamnatin Tarayya na shirin kafa Hukumar da zata kula da daidaiton tashin farashin kayan masarufi a kasar

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yau Talata a wajen wani babban taro na kwanaki biyu kan sauyin yanayi da tsarin abinci a Abuja.

Shettima ya ce za’a baiwa hukumar damar tantancewa da daidaita farashin kayan abinci, tare da kula da tsarin tanadin abinci don daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci.

Tinubu ya gwangwaje yan wasan Super Eagles da gidaje da filaye a Abuja

0

Shugaba Tinubu ya gana da kungiyar kwallon Super Eagles, inda ya karrama su da lambar yabo ta kasa MON da gidaje a babban birnin tarayya Abuja da filaye ga kowannen su a yau Talata.

Tawagar ta samu jagorancin ministan raya wasanni, Sanata John Owan Enoh gami da jami’an hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafan dai ta zo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala a ƙasar Cote d’Ivoire.

Tinubu na ganawa da tawagar kungiyar kwallon kafar Nijeriya Super Eagles

0

 Tinubu na ganawa da tawagar kungiyar kwallon kafar Nijeriya Super Eagles

Shugaba Tinubu yana ganawa da kungiyar Super Eagles a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Kungiyar Super Eagles dai ta sha kashi da ci 2-1 a hannun mai masaukin baki Ivory Coast a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2023 a ranar Lahadin data gabata.

Bayan kammala wasan, shugaba Tinubu ya jinjina wa Super Eagles bisa jajircewar da suka nuna a wasan karshen.

Karin bayani kan kama Murja ‘yar Tik-tok

 

Karin bayani kan kama Murja ‘yar Tik-tok

Karin bayani kan kama Murja ‘yar Tik-tok 

Hukumar Hisbah a jahar Kano ta kama shahararriyar yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya.

Gidan rediyon Freedom ta ruwaito labarin kama Murja a safiyar yau Talata.

Hakan dai ya biyo bayan farautar Murja da wasu ƴan Tiktok biyar da Hukumar Hisbah a Jihar ke yi masu.

Mutanen da hukumar ke nema sun haɗa da Murja, Abubakar Ibrahim (G-Fresh), Sadiya Haruna, Ashiru Idris (Maiwushirya), Ummee Shakira da Hassan Makeup.

Hisbah ta cafke jarumar TikTok Murja Kunya

0

 

Hukumar Hisbah a jahar Kano ta kama shahararriyar yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya.

Gidan rediyon Freedom ta ruwaito labarin kama Murja a safiyar yau Talata.

Hakan dai ya biyo bayan farautar Murja tare da wasu ƴan Tiktok biyar da Hukumar Hisbah a Jihar ke yi.

Mutanen da hukumar ke nema sun haɗa da Murja, Abubakar Ibrahim (G-Fresh), Sadiya Haruna, Ashiru Idris (Maiwushirya), Ummee Shakira da Hassan Makeup.