Gwamnonin PDP sun bukaci Tinubu ya magance tsadar abinci da ake fama da ita a dukkanin fadin kasar.
Gwamnonin PDP sun bukaci Tinubu ya magance tsadar abinci
Ki sanar da mijinki halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, sakon Sarkin Kano ga matar Tinubu.
Ki sanar da mijinki halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, sakon Sarkin Kano ga matar Tinubu.
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga uwargidan Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ta sanar dashi halin matsi da yan Nijeriya ke ciki.
Sarkin yayi kiranne yayin wata ziyarar da Remi Tinubu ta kai kano, ya kuma bukaci shugaban kasar da ya gaggauta magance matsalar rashin tsaro a shiyyoyi shida na Nijeriya domin a cewar sa wannan babban kalu balene.
Yace al’ummar kasar nan na cikin mawuyacin hali na matsin rayuwa don haka dole shugabanni su tashi tsaye domin nemowa al’umma mafita.
Batun rashin tsaro wata babbar matsala ce da gwamnatin Tinubu ta gada amma yakamata gwamnati tayi iyakar kokarinta wajen kwarda matsalar tsaro a fadin kasa.
Da yake magana kan batun mayar da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa (FAAN) da wasu ma’aikatun babban bankin Najeriya (CBN) zuwa Legas, Sarkin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta fito da tsari na wayar dakan al’umma ta hanyar da zasu gane domin ta hakane za’a samu fahimta tsakanin gwamnati da al’umma.
Gwamnatin Tinubu ba ta da alhakin jefa al’ummar Nijeriya cikin matsi Inji Sunusi.
Gwamnatin Tinubu ba ta da alhakin jefa al’ummar Nijeriya cikin matsi Inji Sunusi.
Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Muhammed Sunusi, ya ce rashin adalci ne a zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan halin matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki a halin yanzu.
Sunusi ya ce Nijeriya na fama da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon rashin gudanar da manufofin tattalin arziki na shekaru takwas da suka gabata.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ranar Lahadi a wani taro daya gudana a Abuja,
ya ce ba zai bi sahun masu sukar Tinubu kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu ba, Indai za’ai uzuri ba tun yanzu ake fama da wannan matsin ba.
Sanusi ya ce ya shafe shekaru yana magana a kan matsin da ake ta fama da shi kafin tabarbarewar tattalin arziki. Duk wani masanin tattalin arziki a Nijeriya ya yi nazarin manufofin a cikin shekaru takwas da suka wuce ya san cewa ‘yan Najeriya za su fada cikin wannan mawuyacin hali.
Yace sunsha fadawa al’ummar Nijeriya cewa za’a shiga wannan halin, kuma dole sai anbi manufofin da masana tattalin arziki suka bayyana sannan za’a samu sauki.
Gobara ta tashi a ofishin ‘yan sanda a jihar Kano.
Gobara ta tashi a ofishin ‘yan sanda a jihar Kano.
An samu tashin gobara a ofishin ‘yan sanda na a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano da sanyin safiyar ranar Litinin dinnan.
kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel,ya bayyana haka ga manema labarai inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 05.45 na safe inda wani gini daga ciki ya kone gaba daya duk da cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai dauki.
Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar har zuwa wannan lokaci.
Yace an killace yankin domin hana kutsawar bata-gari, domin akwai makamai da alburusai da ke cikin ofishin wannan dalilin yasa aka rufe shige da fice a wajen
A halin yanzu dai Babban jami’in ‘yan sanda na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa kamar yadda kwamishinan ya fada.
An samu tashin gobara a ofishin ‘yan sanda na a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano da sanyin safiyar ranar Litinin dinnan.
kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel,ya bayyana haka ga manema labarai inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 05.45 na safe inda wani gini daga ciki ya kone gaba daya duk da cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai dauki.
Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar har zuwa wannan lokaci.
Yace an killace yankin domin hana kutsawar bata-gari, domin akwai makamai da alburusai da ke cikin ofishin wannan dalilin yasa aka rufe shige da fice a wajen
A halin yanzu dai Babban jami’in ‘yan sanda na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa kamar yadda kwamishinan ya fada.
An kashe jami’an sa kai na ‘Community Watch Corp’ a Katsina
Kungiyar kwadago ta NLC ta fitar da sanarwar yajin aiki nan da mako biyu.
Kungiyar kwadago ta NLC ta fitar da sanarwar yajin aiki nan da mako biyu.
Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun fitar da sanarwar tsunduma yajin aiki nan da kwanaki 14 masu zuwa muddin gwamnatin tarayya ba ta yi abin da ya dace game da tsadar rayuwa da ‘yan kasa ke ciki.
Sanarwar ta kuma ce kungiyoyin sun yanke wannan shawarar ne saboda gazawar gwamnatin Bola Tinubu na aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ranar 2 ga Oktoba, 2023, biyo bayan cire tallafin da aka yi wa man fetur.
Shugabannin NLC da TUC sun bayyana bakin cikinsu cewa duk da kokarin da kungiyoyin kwadago ke yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma’aikatan gwamnati, da alama ita gwamnatin ba ta damu da dimbin wahalhalun da ake fama da su a fadin kasar ba.
Wadannan tsare-tsare guda biyu, kamar yadda suka yi hasashe, ya yi wa tattalin arziki mummunar illar ga talakawa da ma’aikatan Nijeriya.
Gwamnatin Kano za ta fara farautar ‘yan kasuwa da ke boye kayan Abinci
Da Dumi-Dumi: Hukumar PCACC a Kano ta fara farautar ‘yan kasuwa da ke boye kayan Abinci.
Hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta ce ta fara aikin leken asiri domin farautar ’yan kasuwa da ke taskance kayan masarufi da nufin magance hauhawar farashin kayayyaki a jihar.
Shugaban Hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis.
Muhyi ya ce hukumar ta PCACC na fuskantar matsananciyar matsin lamba wajen matakin da ta dauka kan irin wadannan ‘yan kasuwa saboda irin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Jam’iyyar APC ta yi gargadi kan rusa masarautun Kano
Jam’iyyar APC ta yi gargadi kan rusa masarautun Kano.
Jam’iyyar adawa ta APC ta gargadi gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya yi taka-tsan-tsan don gudun kada a tura shi yin wani abu da zai iya shafar zaman lafiya da ake samu a jihar Kano.
Jam’iyyar APC ta yi gargadin cewa duk wani yunkuri na kawo cikas ga tsarin masarautun, kamar yadda Ganduje ya kirkiro, na iya tayar da zaune tsaye a garin muddin suka dauki matakin hakan kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
A ranar 5 ga watan Fabrairu ne wata kungiya mai suna‘Yan Dangwalen Jihar Kano ta rubutawa Majalisar Dokokin Jihar Kano, takardar neman a sake duba dokar kafa karin masarautu hudu a Gaya, Rano, Karaye, da Bichi da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi.
Kungiyar ta kuma yi kira da a mayar da tsohon Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II.
Kotu ta umurci Tinubu da ya karya farashin kayan masarufi
Kotu ta umurci Tinubu da ya karya farashin kayan masarufi
Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Legas, ta umarci Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ta daidaita farashin kayayyaki da na man fetur, a cikin kwanaki bakwai.
Alƙalin Kotun Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa, shine ya bada umarnin a yayin zaman kotun, bayan da Lauyan nan mai fafutuka, Mista Femi Falana (SAN) yayi Ƙarar Gwamnatin kan hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Falana ya shigar da ƙarar ne, inda ya dogara da sashe na 4 na dokar kayyade farashin kayayyaki, kuma tuni kotun ta umarci gwamnati da ta gyara farashin kayayyakin.
Kayan da umarnin ya shafa sun haɗar da madara, gari, gishiri, sukari, kekuna, ashana, babura, motoci, man fetur, gas da kuma kalanzir.
Kuma dai Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne ga Ministan shari’a na Nijeriya da kuma Hukumar Kula da Farashi Kaya ta ƙasar (PCB).
An rubuta wa majalisar dokokin Kano wasikar neman a rusa masarautu 4, a dawo da guda daya
An rubuta wa majalisar dokokin Kano wasikar neman a rusa masarautu 4, a dawo da guda daya
Wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” (The Kano Electorate), ta rubuta wa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman a sake duba dokar kafa karin masarautu hudu na Gaya, Rano, Karaye da Bichi da gwamnatin Ganduje ta yi.
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga Fabrairu, 2024 da aka aika wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano ta nemi a rusa masarautun tare da maido da Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, inda kungiyar ra ce hakan zai samar da hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da kuma makwabtanta a cewar wasikar.
A ranar 5 ga watan Disamba, Shekarar 2019, tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya rattaba hannu kan dokar masarautu kuma a nan take majalisar dokokin ta amince da dokar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa ana ta cece-kuce kan shirin mayar da Sarki Muhammadu Sunusi ll, kan karagar mulki tare da rusa sauran. masarautun wadanda ake tunanin an kirkire su ne domin tozarta tsohon Sarkin.











