Wednesday, April 8, 2026
Home Blog Page 463

Nagartattun Finafinan mu ka iya dawo da martabar Nijeriya.

Shugaban Hukumar kula da harkar shirya Finafinai a Najeriya kuma jarumi a Kamfanin shirya finafinai na Kannywood Ali Nuhu yana mai hangen cewa shirya nagartattun finafinai ka iya dawo da martabar Najeriya a idon Duniya.

Ali Nuhu ya gano wata matsala da ya ke gani idan aka shawo kanta, nagartattun finafinai na ƙasar zasu iya kaiwa kaso saba’in zuwa saba’in da biyar cikin ɗari, saɓanin yanzu da ake da kaso talatin zuwa talatin da biyar cikin ɗari na nagartattun finafinai a ƙasar.

Daga cikin turbar cimma wannan buri na sabunta Najeriya ta hanyar finafinai Ali Nuhu a wani labari da Jaridar Daily Trust ta wallafa ya ce akwai karin ilimi ga masu harkar ta film da kuma samar musu kayakin aiki irin na zamani.

A cewar Ali Nuhu akwai wasu da ke ɓata suna Najeriya daga cikin ‘yan ƙasar wadda idan aka dukufa ta hanyar nan ta finafinai za’a wanke ƙasar da waccan ɓãtanci, ya kuma nuna muhimmancin manyan kamfanonin finafinai na Kannywood da Nollywood su hada kai wuri guda.

Kaso 30% na jariran da ke mutuwa a duniya ‘yan Nijeriya ne inji wani rahoto

Kwamitin kwamishinonin kiwon lafiya a Arewa maso gabashin Najeriya na bukatar Hukumar Raya Cigaban yanki wato North East Development Commission ta yi hoɓbasa wurin ceto rayukan jarirai da iyayen su da ke mutuwa kafin da kuma bayan haihuwa.

A cewar wannan kwamiti kaso talatin cikin ɗari na mutuwar mata masu juna biyu da jariri a Najeriya ya ke faruwa, saboda haka shugaban wannan kwamiti Farfesa Baba Malam Ganã a wata ganawa da suka yi da hukumar ta NEDC ya ce ya kamata hukumar ta yi dukkan mai yiyuwa wurin taimakawa, dan ganin an magance matsalar. 

Wannan matsala inji Farfesa Ganã tana tayar da hankalin hukumomin kiwon lafiya a Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoto na baya-bayanan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar ya nuna cewa Nijeriya ce ta biyu a irin wannan matsala ta mace-macen mata masu juna biyu da yara ƙanana.

Gwamnatin Kebbi ta rufe wasu kwalejojin kiwon lafiya guda biyu

Gwamnatin jahar Kebbi ta rufe wasu man’yan makarantu biyu masu zaman kansu bisa rashin biyan haraji har na tsawon shekaru biyu.

A wata sanarwa da ta fito daga ofishin Kwamishinan ilimin na jahar Isa Abubakar Tunga ta nuna cewa gwamnati bazata yi musu da wasa ba saboda sakaci da suka yi bayan tunatar da su da kuma kashedi da gwamnati ta yi garesu a lokuta daban-daban.

Makarantun da aka rufe sune Kwalejin ilimi da kimiyyar kiwon lafiya ta Lamiɗo Umaru Mutube da ke Ɗakin- Gari da Kwalejin Kimiyya da fasahar kiwon lafiya ta SAHAM da ke Zuru.

Gwamnatin ta Kebbi ta ce babu wata bita da ƙulli a batun dakatarwa kuma da zãrar sun biya kuɗaɗen da gwamnati ke bin su za’a buɗe makarantun su ci gaba da harkokin karantarwa.

Binciken hukumar kula da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO na 2012 ya nuna cewa Jihar Kebbi dai na daga cikin jihohin Najeriya da ke baya a ɓangaren ilimi bayan jihohin Katsina, Taraba, Borno da Jigawa.

DSS sun kwace wasu kadarori mallakar ‘yan uwan Abdulrasheed Bawa

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta gayyaci wasu ‘yan uwan dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, domin amsa tambayoyi.
Jaridar DAILY NIGERIAN bada rahotan cewa hukumar ta SSS ta gayyaci ’yan’uwan Bawan su biyu, Yazid Bawa (wanda shi ma yake aiki a hukumar ta EFCC) sai kuma Bashir Bawa (wanda ke aiki a NCC).
Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa jami’an tsaron sun kwace motar alfarma da harsashi baya ratsa ta da kuma sabuwar mota kirar Mercedes-Benz mallakin  ‘yan uwan ​​na Bawa.
Tun a ranar 14 ga watan Yunin shekarar nan ne dai Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Bawa daga aiki.

Zan je da kaina in sanar da shugaba Tinubu halin matsin rayuwa da ake ciki – Gwamna Abba

Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya ce shi da kashin kansa zai sanar da shugaba Tinubu halin da talakawan Nijeriya ke ciki na matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a Kano.
Ya koka kan yadda a kullum rana ake samun tashin farashin kayayyaki, inda ya ce hakan na bukatar daukin gaggawa don a yi wa tufkar hanci.
Gwamna Abba Gida-Gida ya ce gwamnatin jihar Kano za ta yi duk abin da ya dace son samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa don bunkasar tattalin arziki.

Ba da jimawa ba halin matsin da ake ciki a Nijeriya zai wuce inji matar Tinubu

Uwargidan shugaban Nijeriya Sanata Oluremi Tinubu ta ba ‘yan kasar tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za su fita daga cikin halin kuncin da suka shiga.
Oluremi Tinubu ta ba da wannan tabbacin a lokacin da take ganawa da matan gwamnonin kasar a Abuja.
Ta ce shekarar 2024 cike take da zaman lafiya, ci gaba da sauran abubuwan ci gaba da ‘yan kasar za su mora.

Mun yaba wa NAHCON da ta nemo ragin kudin kujerar aikin hajji ga ‘yan Nijeriya – IHR

Kungiyar masu aike wa da rahotannin yadda aikin hajji ke gudana ta ‘Independent Hajj Reporters – IHR’ ta yi jinjina ga hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON da ta nemo wa maniyyata aikin hajjin bana na kasar sauki wajen farashin kujerar zuwa aikin hajji a shekarar 2024.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar mai zaman kanta Alhaji Ibrahim Muhammad, ta ce tana sane cewa kudin aikin hajjin bana na iya kaiwa Dala 6,000 kwatankwacin Naira milyan 8,400,000 a kudin Nijeriya idan aka sayar da Dala daya kan kudi N1,400.
Sai kungiyar ta ce bayan yunkurin da hukumar NAHCON ta yi, yanzu duk a fadin Nijeriya, karshen kudin zuwa aikin hajjin shi ne Naira milyan 4.9 da zai taimaki ‘yan Nijeriya su samu rarar kudin da suka kai kusan Naira milyan biyu ga yadda Saudiyya ta tsara za a biya.

An katse intanet a kasar Senegal

A cikin wata sanarwa ce da ya fitar a ranar lahadin nan, ministan sadarwar Sénégal ya bayyana matakin katse intanet din a duk fadin kasar
Ministan ta cikin takardar ya ce an dauki wannan mataki ne biyo bayan yada sakonnin tayar da hankali ‘yan kasar a shafukan sada zumanta na zamani da ke tattare da barazanar tayar da tarzoma a kasar

An sake dage shari’ar matashi Sani Zangina da Rarara

Kotun Majistare mai lamba 1 da ke zamanta Lafia babban birnin jihar Nasarawa ta sanar da dage zaman sauraron karar da matashi Alhaji Sani Ahmad Zangina ya kai kan mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi da aka fi sani da Rarara har sai ranar 9 ga wannan wata na Fabrairu.
A zaman kotun da ya gudana a ranar Juma’ar da ta gabata 2 ga watan Fabrairu, da Alkalin kotun……. jagoranta, ya ce hakan ya biyo bayan rokon da lauyan matashi Sani Zangina  ya yi.
Shi dai wannan matashi Sani Ahmad Zangina na neman kotu ta bi masa hakkinsa bisa abin da ya ce tunzura shi da wasu kalaman mawaki Dauda Rarara suka yi a lokacin da ya gudanar da wani taron manema labarai ya yi kalamai kan tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari.
A zaman kotun da aka gudanar a ranar 6 ga watan Janairu da ya gabata, kotun ta dage kai da fata sai mawakin siyasar ya bayyana a gabanta duk kuwa da wakilcin lauyoyinsa da yake samu a duk lokacin da za a gudanar da zaman.
Dama dai sai da kotun ta ba da umurnin a lika wa Mawaki Dauda Kahutu Rarara takardar sammaci a kofar gidansa biyo bayan wahalar samunsa don a hannanta masa wannan takarda.

‘Yan jihar Neja na zanga-zanga kan tsadar rayuwa

‘Yan sanda sun harba bindiga don tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Minna na jihar Neja kan tsadar rayuwa.
Da sanyin safiyar Litinin, mata suka datse hanyar Minna-Bidda, inda suke nuna matukar damuwarsu kan yadda farashin kayayyaki ke tashi ba kakkautawa.
Daga bisani, bayan matan sun fito, sai maza ma suka fito suka mara musu baya don ci gaba da zanga-zangar.
Kokarin da ‘yan sanda suka yi na shawo kan tarurun jama’ar ya ci tura, har ta kai ga sun harba bindiga a sama.